Sashe 218
Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kasa yin magana ya yi ya tsareta da idanu yana kallon tula tulanta da suke tsole mashi idanu a maimakon face É—inta.
Ƴan yatsun hannunta guda biyu ta sake kyasta mashi a saitin face ɗinsa tare da hura chewing gum da take tauna ta yi balo balo kenan.
Kamar wani maras gaskiya da sauri ya dawo da kallonsa a kan face É—inta yana wani É—aure fuska irin ya basar ta kamashi yana kallonsu É—in nan.
"Big bro, face ɗina fa zaka kalla mu yi magana ba wani waje ba, da ni kake magana ba da kirjina ba, wai nace ba, mema kake kallo a kirjin nawa? Ko dai............". Dakatawa ta yi da yin maganar ta kasa ƙarisawa sakamakon zaro mata kaifafan sexy eyes ɗin nan nasa da ya yi.
Wato wannan ƙaddarar tasa ta zama tacacciyar ƴar ikka, kuma yasan dik waye ya ja mashi hakan, dole ya ɗauki mataki, yarinya ce ta wuci dik yadda yake tunani, yanzu ya shiga uku tun da ta kama shi yana kalle mata tula tula, wannan zance ba zai tsaya iya nan ba, to wai ma me ya kaisa? Shi anya ba zai ɓatar da yarinyar nan ba kowa ya huta?.
Wani ɓangare na zuciyarsa ce ta amsa mashi da, ai ba zaka iya ɓatar da ita ba, ka manta ita ɗin kaddarar ka ce, zama da ita dole, wannan shi ne ba saki ba karin aure, mutu ka raba takalmin kaza in ji hausawa..............😂
Kai Hasbunallahu wani'imal wakil, wato ana wani iyashege a wannan gida.😂🥱
Zata sake yin magana tana ƙoƙarin huro chewing gum ɗinta ya ɗan sanya mata zarra ta hanyar matsar da face ɗinsa dab da ita yana zare mata ido. Ai a miliyan ta yi baya, ta tsorata sosai. Ɗan gocewa high heel na kafarta ya yi saboda baya da ta ɗan yi ba shiri, hakan yasa chewing gum da ta huro ya ɓata mata fuska, tafita ta yi ta zube ƙasa a saman gwiwowinta!. Wuceta ya yi da sauri ya sauka ƙasa, dan tana neman kawo mashi wani sabon al'amari.
Turo baki ta yi, a fili ta ce. "Allah ba zan barka ba, tin da ka sanya na faɗi kasa kuma na ɓata face ɗina da chewing gum sai na ɗauki fansa, ai a yarjejeniyarmu mun yi da kai ba zaka taɓa mun abin da bana so ba kuma ba zaka taɓa bari na cutu ba, amma da kanka ka cutar dani yanzu". ME KUKE TINANIN ZATA YI MASHI?.
Tana ƙoƙarin miƙewa Ronnie ya hauro sama da gudu yana faɗin. "Sister come and see our surprise, Big Bro ya yi mana surprised mai matuƙar kayatarwa, za'ayi shagali a ranar white Happy and Sad day ɗinmu, zamu fi kowa kyau".
MEMENE WHITE HAPPY AND SAD DAY?
kalar fari shi ne fav kalar Black Tiger, wannan dalilin yasa ya sanyawa wannan rana sunan white Happy and Sad day, sau ɗaya suke shagalin wannan rana a shekara, rana ce da babansa ya mutu, kuma rana ce da a cikinta babansa ya karɓawa birnin Black world takardar zama ƙasa mai cin gashin kanta, wato rana ce da suka samu ƴancin kai! So ranar suna shagali da rana, da daddare kuma su yi kuka da jimamin mutuwar babansa, the whole ranar white clothes suke sanyawa, komai fari tas............ Wato babu kamar addinin musulunci fa my people's, wai ayi shagali da rana, da daddare kuma ayi kuka na jimami, kai jama'a Allah ka dawwamar da mu a cikin musulunci!!.
Miƙewa ta yi tana faɗin. "Menene white Happy and Sad day kuma?". Hannunta ya zo ya riko yana faɗin. "Muje ki ga kayan da Big Bro yasa aka kawo mana daga kasar England, idan kika gani zan faɗa maki menene white Happy and Sad day da irin shagali da kuka da muke yi"...... "Shagali da kuka kuma?". Ta tambaya cike da mamaki......... Wai shagali da kuka, dole kanta ya kulle...................... "Let's go zan yi maki bayani idan muka je bedroom". Ya kai karshen tare da jan hannunta, bayansa kawai ta bi mamaki kamar ya kasheta!!. My people's wannan rana ta W.H.S.D ɗin nan nasu fa ba ƙaramin gagarumin rana bane wanda kura zai tashi a cikinsa, uhm zamu sha shagali kuma mu sha kuka, kowacce shekara da Floris ake yi, amma wannan babu ita.............. 😥💔
-----------------------------------------------🔥
🔥🔥🔥KINGDOM OF POWER.🔥🔥🔥
A yau jirgin momma ya ɗaga zuwa Dubai, tamkar Smart ya zuba ruwa a ƙasa ya sha haka yake ji, ya ji daɗin tafiyanta matuƙa, ta so tafiya da Auta dan ta kaita can ko zata huta ta ji sauki, amma King ya hana, saboda ya ƙasa samun natsuwa, yana cikin fargaba da tashin hankali, dan yana ganin kamar zai rasata ne kawai, saboda dik yadda kuke tinani abin ya wuci nan, Zunaira ta lallace ta rame, tamkar mai ciwon H.I.V, abin gwanin ban tausayi, uncle Jahiz sam baya san zuwa wajenta, saboda tana saka shi kwallah!.
Zaune take tare da Chuchu a saman bed a cikin part da aka kaita, sai ƙoƙarin janta da hira Chuchu take yi domin su samu ta ɗan saki jiki da su, sai dai ina, dik hiran da Chuchu take yi mata taki tofa ko uppan, kanta a ƙasa tana kallan yatsun hannunta da suke ɓulɓul a da, yanzu sun rame sosai, kamar ba nata ba!.
Dafata Chuchu ta yi tana faÉ—in. "Auta dan Allah ki ce wani abin mana! Tsawon awa biyu muna tare, ni kaÉ—ai nike ta yin magana kinki ki amsani, kina son nima in kara ciwo a kan wanda nike ciki ne?". Cikin raunatacciyar murya Chuchu ta yi maganar, tamkar zata yi kuka, idanunta sun cicciko da kwallah, ta rame sosai ita ma, tamkar ita take jinya!.
Kanta a kasa ta ɗan girgiza alamar bata san Chuchu ta yi ciwo, amma bata iya yin magana ba. Kara matsawa kusa da ita Chuchu ta yi, ta buɗe baki zata yi magana kenan sallamar Abdussalam ya katseta. Sanye yake da arabs jallabiya dark ash, shi ma ya rame sosai, saboda ciwon nata. Ganinsa yasa Chuchu ta miƙe tana faɗin. "Zan dawo zuwa anjuma". Ta kai karshen maganar tare da ficewa daga ɗakin.
A in da Chuchu ta tashi ya ƙarisa ya zauna, a hanzarce Auta ta ɗan ja baya tamkar wadda aka matsowa da wuta kusa da ita. Ajiyar zuciya bawan Allah ya sauke, cikin sanyin murya ya ce. "Zunaira ki faɗa mun dalilinki na guduna? Na tabbata yansu kam na ciwo bane! Dole akwai wani dalili, dan kin samu sauki"......... Kin yi mashi magana ta yi, sai dai har cikin ranta ta ji wani irin yadda ya kira sunanta, bai taɓa kiranta da Zunaira ba, kullum my wife yake cewa, da alama yau hakurinsa ya kare ne!.
"Ki yi magana kin ji? Ki kalleni a matsayin yayanki ba miji ba, ki faÉ—a mun damuwarki, ni kuma zan tsaya a wajen ganin na fitar dake daga damuwar"........... "So nike kawai ka sake ni, shi ne damuwata". Abin da ta faÉ—a kenan ba tare da ta É—ago da kanta ba, da kyar muryarta yake iya fita saboda kukan da ta sha. Wani irin zaro idanu Abdussalam ya yi, a hankali ya maimaita kalmar saki kafin ya ce. "Ai ko wata bare na aura ba zan saketa ba Zunaira bare ke da kike matsayin kanwata, ke da nike tsananin kauna tin kina yarinya, Allah ya mallaka mun ke ya cika mun burina kuma yanzu ki ce in sakeki? Tukun nan ma saboda me?".
Shiru ta yi mashi dan tasan ko zata mutu ba zai taɓa sakinta ba, aurensu ai babu saki, su a ƙaidar familynsu ma ba'a saki, babu wacce aka aura aka saka, ko bare suka aura nasa saki bare na gida, ai kun san wannan aure ba mai mutuwa bane!. Ganin ta yi shiru ne yasa ya kai hannunsa ya riƙo nata. Zabura ta yi zata kwace kanta ya yi gaggawar riketa da karfi, dan dole ta natsu bata iya kwacewa ba. Cikin taushi da tausasawa ya ce. "Zunaira please, ki tausaya mun, ki ji kan zuciyata, wlh ina sanki, kuma kome kike so zan yi maki, dan Allah ki faɗa mun menene yake damunki, Zunaira kalli yadda na rame fa saboda ke, please my wife, Yah Abdussalam ɗinki ne fa? Ko kin manta ne? Kin dai'na so na ne? Please kada ki bari zuciyar da bata san komai ba face sonki ta cutu, bata san komai ba sai begenki, please my wife help me and accept me as your husband, na yi maki alkawari zan sanyaki farinciki koda ni zan kuntata". Tamkar zai yi kuka ya kai karshen maganar.
Shiru ta yi idanunta suna zub da zafafan hawaye, take kalaman Hoorain suna ratso mata cikin brain É—inta a in da yake ce mata. "Hoonairata kada ki yarda ki yi magana da wani namijin a bayan idona, ki rike mun amanar kanki, ke tawace ni kaÉ—ai". Tina hakan yasa ta kai kallanta a kan hannunta da Abdussalam ya rike, take zuciyarta ya buga da karfi, ba iya magana da wani ba har hannunta ta bari ya rike.
Wani irin kuka mai tsuma zuciya ta fashe da shi tare da kwace hannunta da karfi, da gudu ta miƙe ta fito parlour, ƙasa iya cigaba da tafiya ta yi, da ta so ne ta fita waje, amma sai ta ƙasa saboda jiri, bata gama samun lafiya ba, a tsakiyar parlourn ta zube gwiwowinta a kasa, rushewa ta yi da kuka mai sauti, cikin kukan ta fara sambatu kamar haka. "Am so so sorry my Hoorain, yau na karya alkawarin da na ɗauka maka, na bari wani namiji ya taɓani, ba zan yafewa kai'na ba har sai ka yafe mun, ni taka ce kai kaɗai, kai kaɗai kamar yadda kake nawa ni kaɗai". Cikin fitar hayyaci take wannan magana, sam bata lura da Chuchu dake zaune a saman sofa a cikin parlourn ba. Allah sarki Chuchu, ta kasa komawa family part ta bar autar ne, shi ne yasa ta zauna a parlourn tana jiran idan Abdussalam ya fita sai ta koma su cigaba da yin hiran.