← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 242

Sashe 75

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai ƙasa komawa mazauninta ta yi, sai kawai ta tsaya a wajen cak tare da rushewa da kuka mai tsuma zuciya, dama a kusa take, kiris take jira ta fashe dama.

Da saurin uncle Jahiz ya miƙe ya nufota, cike da gimamawa ya fara faɗin. "Sarauniya momma ayi mana afuwa, na tabbata ɗauki ganin babyn yasa ta rasa control ɗinta, and bana tinanin tasan in da take shiysa dik ta yi wannan shirmen". Ya kai karshen maganar yana rike hannunta.

Baya kaɗan ya jata izuwa in da ta miƙe, cikin nitsuwa ya mayar da ita ya zaunar.

Momma da tausayin Zee ya gama narkar da zuciyarta ne ta umarci da su rabu da ita ta matso taga É—anta, ai jini ba wasa ba. A tinanin momma Zee ita ce uwar É—an.

Ai Zee tana jin an bata dama ta yi saurin miƙewa ta isa gaban momma, jikinta har rawa yake yi wajen kai hannu, tin ba'a miƙo mata shi ba ta karɓesa. Aunty MieMie ma tausayinta ta ji ya kamata, Allah sarki jini ba wasa ba, sai kerma hannunta yake yi ta rike yaron gam idanunta suna ciccikowa da kwallah.

Momma mace mai dattaku, hannu ta kai tana dan shafa kanta da yake Zee ta zube gwiwowinta a ƙasa gaban momma ɗin ne da ta karɓi yaron. Rarrashinta momma ta fara yi tare da ƙara mata kwarin gwiwa a kan ta koyi jajircewa.

Aunty MieMie ma data ga hakan sai ta tsoma baki suka fara rarrashinta a tare. Uncle Jahiz ne ya fayyace masu cewa Zee fa ba ita ce uwar yaron ba, sisterta ce uwar yaron. Dik da suka ji hakan sun tausayawa Zee sosai, dan daga yadda ta nuna reaction É—inta a kan yaron nan alamu sun nuna akwai damuwa.......... Wai dan ma basu san tarihinsu ba kenan, da sun sani sai yaya kenan?. Ai su Zee su suga rayuwa, sun sha gwagwarmaya kam ba kaÉ—an ba.

Shiru parlourn ya ɗauka na ɗan lokaci, sai shessheƙar kukan Zee ne yake tashi a hankali hankali gwanin ban tausayi.

Aunty MieMie da ta lura kamar akwai yunwa sosai a tattare da Zee sai ta ce yakamata a kawo mata abinci ta ci. Momma ma ta lura da hakan, sai ta amsa da yakamata kam.

Aunty MieMie ce ta mika hannu ta karɓi babyn daga hannunta, sannan ta ce uncle Jahiz ya sanya a kawo mata abinci ta ci. Sam bata tambayi wacece Zee ba, dan su suna da ɗabi'ar dik wanda suka gani a tare da ɗan uwansu to fa zasu bashi mahimmanci. Tun da suka ganta tare da uncle Jahiz sun san ba banza take ba, saboda su basa kula abu idan ba ya kasance ya shafesu ba.

Miƙewa uncle Jahiz ya yi ya nufi waje. Jim kaɗan ya dawo tare da wasu kuyangu guda biyu da suke ɗauke da tampatsetsan tray mai girma, shake take tap da abinci launika daban daban da a kallah zasu kai kala goma. Kun san larabawa da yawan girke girke kala kala.

Kai tsaye saman dining table na momma suka nufa suka shirge abincin, ga kayan drinks kala kala, ferfesu kaji dana É—awisu, kun san gidan sarauta suna da É—awisu sosai, ga dahuwar Chinese rice kala daban daban, kai waÉ—an nan tray sun haÉ—e komai, har da kayan marmari.

Umartar Zee ya yi da ta tashi ta je ta ci abinci, da yake parlourn yana da girma, daga wajen da table É—in yake zuwa in da suke akwai tazara mai tsayi.

Da yake yunwa baiwar Allah take ji sai bata musa ba ta tashi, jikinta har ɓari yake yi ta nufi wajen table ɗin. Da kallo suka bita har ta kai wajen, sannan suka dawo da kallonsu a kan uncle Jahiz dan jin wacece ita daga ina kuma ya samosu.

Yasan abin da suke wa binsa da kallo, karin bayani suke jira ya kora masu. Dan haka cikin nitsuwa ya yi gyara murya kafin ya fara kora masu dik abin da suke tsumayan jira daga garesa. Ya yi masu bayanin ne kuma ba tare da ya bawa kowa damar jin abin da ya faÉ—a ba, zance ake ta sirri!!.

Ko ita Zee dake zaune saman table bata ji abin da suke tattaunawa ba, ita dai ta zauna shiru tana bin kayan abincin da kallo, Allah sarki taga duniya, ta rasa da wanne zata fara, yunwa take ji over, dan ma Allah yasa ita ba wawiya bace, da ɗan wayewarta, amma dik da haka sai da ta yi kauyanci a ɓoye, dan kuma kun san zaren ba kalar yadin bane.

Dikkansu babu wanda fuskarsa bai nuna alamar mamaki ba a lokacin da uncle Jahiz ya gama basu wannan labari da ya É—auko É—an sanar da su su wacece Zee, a fili momma ta furta.
"Dikka wannan zalincin su kaÉ—ai?".

Jinjina masu kai ya yi ba tare da ya yi magana ba. Aunty MieMie da ranta ya gama ɓaci har idanunta sun kaɗa sun yi jajir ne ta ce. "Gaskiya ba zata saƙu ba, dole mu kwatar masu ƴancinsu".

Jinjina kai momma ta yi alamar tabbas kuwa. Shi ma jinjina kai ya yi alamar haka ne. Da alama labarin tarihin su Zee ɗin ya basu, dan tabbas ya lallaɓa Zee a asibiti, ya gwada mata fifikon shekaru a in da ya yi mata dabara har ta yarda ta bashi tarihin rayuwarsu.

Amm kuma sai dai akwai wani abin da ya sanar da su momma bayan tarihin su Khadija ɗin, dan yanayin mamakin da ya bayyana a kan fuskokinsu abu ne mai girma da ya fi tarihin su Zee suka ji, dole akwai wani sirri da ya sanar da su wanda baya buƙatar a ji........... Ni kam nace koma dai me ka sanar da su idan lokaci ya yi ruwan ta yi tsami ni da my people's ai zamu ji ko? Sai kwan ta fashe In Sha Allah mun ji komai ato, mu je dai zuwa.

"Gaskiya akwai azzalumai a duniya, yanzu ko ta ina zalinci kawai ake yi, ya ilahi ya lillahi, wannan musifa dame ta yi kama". Cewar Momma da alamar jikinta a sanyayye.

Ita ma Aunty MieMie ta yi laushi, kamar wanda ya sheka masu ruwan sanyi, dik da alamar karyewar zuciya da tausayi a tattare da su.

"Uncle Jahiz taki cin abincin fa, ko zaka je ka yi mata dabara ta ci tun da kun saba da ita". Cewar Aunty MieMie da ta farga da Zee bata cin abinci.

Miƙewa tsaye ya yi, ya nufi table ɗin yana faɗin. "Dama kullum sai mun kai ruwa rana da ita take yarda ta ɗan tsakuri abincin ai, bari na gwada yanzu ma".

Momma ce ta karɓi zance da cewa. "Ai dole ne ta shiga damuwa Jahiz, amma In Sha Allah damuwarta ya zo karshe, bari daddunsu ya sarara da musifar da muke ciki na ɓatar Zunaira, tabbas za'a biwa yaran nan hakkinsu, sai mun tsaya masu In Sha Allah".

Jinjina kai Aunty MieMie ta yi, kun san tana san jinin ƴan Nigeria ita, saboda jinin mummynsu ne, dan haka ta kudurta a ranta wlh ba zata sarara ba a kan wannan case na su Zee, sai ta ɗaukar masu fansa, kai jama'a jinin modarawa ake magana, su da basa yafe ko harararsu ka yi........😅

Saman table chair dake kusa da ita ya zauna, su momma kuma suka miƙe izuwa cikin bedroom ɗin momma dan su tattauna wani sirri nasu, momma tana mugun shiri da Aunty MieMie sosai, ta su ta zo ɗaya, kun san sai hali ya zo ɗaya ake abota, batu na Allah aunty MieMie mutuniyar kirkice number ɗaya.

Chinese fried rice ya zubawa Zee, sai kallan face ɗinta yake yi, ta yi ƙasa da kai tana ɗan murza ƴan ƴatsun hannunta. Cikin harshen turanci ya ce da ita. "Bari in baki abincin a baki to tin da ba zaki iya ci ba".

Da sauri ta girgiza mashi kai alamar bata buƙata.

"Baki san zuwa ki kalli Khadija ne?". Da sauri ta buɗi baki ta amsa da tana so. "To in dai kina san zuwa wajen Khadija lallai ki ci abincin nan, idan kika ƙoshi sai in kira Fanan ta kaiki ɗaki ki yi wanka sai in kai ki wajen Khadija".

Kamar zata yi kuka ta ce. "Zan ci ko dan in ga ƴar uwata, amma dan Allah ka faɗa mun kasan Khadija ne? Ya kai sati kenan ina yi maka wannan tambayar sai ka ce mun ni kaɗai ka sani baka san ta ba, nace maka a ina kasanni ni ɗin ka ce mun a Nigeria, ka fayyace mun komai yadda zan fahimta kuma kaki". Da kyar ta iya karisa maganar, saboda wani irin kwarjini da yake yi mata, kuma ita gaskiya abin yana cinta a rai tana san samun amsa, tabbas ita hotonsa ta gani a hannun Khadija, wlh ko ratsuwa ta yi ba zaga yi kaffara ba shi ne, sannan shi ma da ya ganta ya ce ta yi mashi kama da wata da ya taɓa gani sai dai ya manta a ina, to da waye zata yi kama idan ba Khadija ba?.

Bugu da kari shi da bakinsa ya ce babyn Khadija yana kama da shi, ga shi likitoci sun hanasu ganin Khadija saboda condition da take ciki, an yi mata aiki a ciki baiwar Allah, ashe matar nan da ta basu wajen zama a gidata a Abuja ita ta cucesu lokacin haihuwar Khadija bai yi ba ta bata maganin tasar da naƙuda, dalilin haka mahaifar Khadija ya tsage, sai da aka yi mata aiki yanzu, Allah ma yasa tana da rabon shan ruwa a gaba, ai da ta jima da mutuwa saboda irin jinin da ta rasa, amma Allah ya ƙaddara zata rayu.

"Zee ni har yau ban ga face É—in Khadija ba bare in san nasanta ko ban santa ba, sannan kuma na faÉ—a maki ke na sani kawai, ki ci abinci, likitoci sun ce mun zuwa yamma zan samu damar ganin Khadija, idan muka je sai in ga ko na santa".

Shiru Zee ta É—an yi, ita dai wlh tasan shi ne na jikin hoton nan, sai ma da ta gansa a zahiri yanzu ta kara yarda, amma bari Khadija ta farfaÉ—o komai zai bayyana ai.
Chapter 75 · 0% Book details