← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 145 OF 242

Sashe 145

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Baby kai zaka aureni kuma?". Ta tambaya like bata gane me yake nufi ba........ "Yeah ko baki san hakan ne?". Ya jefa mata tambayar tare da É—an raba jikinsa da nata yana kallan face É—inta dan yaga reaction É—inta. Tafukan hannayenta ta kai ta rufe face É—inta tana murmushi.

Shammatarta ya yi ya É—auketa cak sai saman bed yana faÉ—in. "Kin É—aga mun hankali over, kin sa na ji wani irin, dan haka yanzu zo mu yi hira babu in da zan je, kwantar mun da hankali kamar yadda kika É—aga mun, yau i think ma a nan zan kwana". Ya kai karshen maganar yana kwanciya da ita a saman bed É—in.

A cikin kirjinsa ta tura kanta tana faÉ—in. "Zan ji daÉ—i idan ka kwana a nan, dama haka nike so, kwantar da hankali kuma yanzu kuwa zan kwantar maka".
Rungumeta sosai ya yi tare da ja masu bargo ya rufesu har kai. .............To baby sai dai mu ce asuba ta gari Allah yasa iya barci kawai baby zai yi....👀🥱

Bari mu leƙa wani part mu dawo muga ya za'a kwantarwa da baby hankali, sai mun bi kwakkwaf😅🥱

🔥🔥🔥BLACK WORLD.🔥🔥🔥

Yau ta kama Sartuday, bayan kwanaki biyar kenan da fara zuwan Sweetie school, daren yau za'ayi babban partyn su Ronnie. Tin safe ake ta shirye shirye, kayan da Black Tiger ya sayawa Ronnie da zai saka a wajen wannan party lallai ba'a taɓa wani ɗa da ya taɓa sanya kwantankwacin irinsu a faɗin birnin ba, dan kuɗin kayan kawai ya kusa kuɗin jirgi guda ɗaya cikin jiragen Black Tiger.

Tun kwana uku da suka wuce Ronnie da Sweetie suka haɗu suka zaɓi kayan da suke ga ya yi masu da irin design da suke so, kayan ya haɗu matuƙar haɗuwa, three-piece suit ce ajin karshe a tsada na Ronnien, cover shoes da zai haɗa da kayan ma almost hundred million take. Ita kuwa Sweetie dama wani irin daddatsetsen gown ya zaɓa mata wanda ya sha kwalliyar duwatsu na alfarma, kayan sun kai makurar haɗuwa, sai dai fa ita da Floris aka saya masu iri guda, kuma Ronnie ne ya ce hakan, dan shi har yau har gobe yana san Floris sosai, matsayinta bai canza a zuciyarsa ba, ita ce dai ta ja baya da shi.

Kayan nasu ita da Ronnie kalarsa É—aya, yadda kuka san amarya da ango, dikka milk color ne, sai murna Ronnie yake yi ana ta hidima, jama'a na ta kai koma, dama jiya za'ayi partyn fa, sai Sweetie ta ce da Ronnie a É—aga zuwa yau saboda girma da falalar ranar jumma'a bai kamata su yi party a ranar ba. Aminta ya yi da hakan shiyasa ya riko yayansa da a É—aga wannan taro zuwa yau, da yake Black Tiger bai san dalilin É—agawar ba sai ya yarda, da yasan saboda addinin Sweetie ne ba zai yarda a É—aga ba, saboda bayan san musulunci, a jininsa tsanar addinin take. Kada ku manta autan ruhohi ne shi É—in, kunga tsanar addinin a jininsa take.

Abin da baku sani bama, da Ronnie ya same shi da batun dakatar da halaccin luwaÉ—i a birnin sai ya ce kowa yana da Æ´ancin yin abin da yake so, dan haka shi ya halatta yin hakan, kada Ronnie ya kara zuwa mashi da wannan zance kuma kada ya kuskura ya hana kowa aikata luwaÉ—i ko zina, shi ya yarje masu su yi, su more rayuwarsu.
Da farko Ronnie ya damu sosai, har yake jin kamar ya gudu ya bar birnin saboda kyamar abin dake ransa, amma Sweetie ta tsaya tsayin daka wajen nusar da shi cewa ya yi hakuri watarana komai zai wuce, ba'a da'awa cikin sauki dama, kuma dama yadda suke ƙoƙarin nan dole shaiɗan ba zai so hakan ba, idan shaiɗan ɗin ya gwada ringayarsu ta ɓangarensu suka ki yarda Allah ya tsaresu daga sharrinsa, to sai ya koma masu ta wani ɓangaren, tana da tabbacin shaiɗan ne ya koma jikin Black Tiger yasa yaki yarda da wannan doka, dan haka ya kwantar da hankalinsa zasu yi nasara a kan big bro, da sun yi nasara kuma shikenan komai zai tafi yadda suke so, da kansa zai yarda da dokar, su zasu zama masu kafa doka kai tsaye ma ba sai sun ji ta bakinsa ba.

Da kyar dai Sweetie ta iya shawo kansa ya yarda, dik wani abin da Sweetie zata ce addininta ya yi hani da shi to shi kuma Black Tiger sai ya halasta wannan abin wa ƴan birnin, dik dan kiyayyarsa ga Musulunci, amma dik da haka Sweetie bata taɓa nuna ta damu ba, saboda tana koyi da annabawan Allah waɗan da suke da hakuri da juriya mai tarin yawa dan cinwa nasara...... ALLAH KA BAMU IKON YIN KOYI DA SU.

••••••••••••••••••••••••••••♥️

An ƙawata hall ɗin da za'a gudanar da wannan party matuƙa, yanayin tsarin hall ɗin hakika ya ƙayatar kuma kowa ya gani yasan anzubar da makuɗan kuɗaɗe ba kaɗan ba. Kayan Ado wato decorations masu zafi da tsantsar kyau. Yanayin theme na wajen launin white and gold ne, an zubawa gold ɗin kwayaye masu bata haske a in da suka kara haskaka wajen matuƙa, gold ɗin ya kara haske da ƙawata wajen.

A gabaɗaya wajen an ƙawata shi ne da wasu irin kyawawa kuma tsadaddun balloons, furanni masu kyau, da kujeru masu rufi (chair covers) da ribbons masu launin gold and white. A saman haɗaɗɗun tables dake wajen gabaɗaya akwai wasu centerpieces masu kyau irin su furanni, kyandiru da fitilu masu kyalli da suka kara ƙawata wajen.

Tables na wajen sun kasance a tsari mai kyau. Table da tsadadden kujerar da shugaban party zai zauna wato VIP table a gaban hall É—in yake, yana fuskantar kowa kenan. Wajen da aka shirya abincin da aka shigo da su dan rabawa a wajen part É—in yana É—an nesa da wanen tables É—in.

And manya manyan fitilu dake wajen masu duhu ne amma na alfarma, ga wani katan chandeliers mai wuta launika daban daban da ya kara ƙawata wajen a sama tsakiyar hall ɗin. Wajen kujerar zaman Ronnie namu and Black Tiger namu ya kasance da ƙarin haske na musamman don jama'a su samu damar ganinsa da kyau. My people's wajen nan ya haɗu, kuɗi sun yi kuka, tun daga kan tsarin wajen zaku gane ɗan gata kuma shalele ne zai yi party, abin ya haɗu fiye da tinaninku.

Shi kansa Black Tiger sai shirye shiryen zuwa wajen yake yi, dan tun karfe 4 na yamma za'a fara, kwana za'ayi ana yi. Ronnie kuwa tini ya gama shirinsa, dan yau rana ce ta musamman a garesa, yau zai shiga office É—insa a matsayinsa na babban Dr, apart from this hospital É—in gabaÉ—aya mallakinsa ne. Ku kunsan abin ba'a magana sai shiru!!.

Tin karfe uku Ronnie ya tafi wajen part da nufin Sweetie zata biyosa daga baya, dan ita ta ce sai 4:30 zata zo, zata ɗan yi barcin rana ne, ya so su jera a tare, amma taki yarda. Sam bai nemi Floris ba, saboda yana tinanin zata zo a tare da Sweetie. So sai ya yi gaba, ya sha kwalliyarsa, sai dai har yau yana saka waɗan nan chairs and ring ɗin, ga earing, a yau ma dik ya zubasu a jikinsa, ya yi kyau kam matuƙa sai dai haramun ne, amma ya yi wa Sweetie alkawarin a hankali hankali zai dai'na sakawa In Sha Allah, ta taya shi da addu'a. Kun san sabo da yin abu barinsa lokaci guda abu ne mai wahala

Sai dai kuma tana can part na master Devil ba tare da sanin kowa ba, akasi aka samu tsakaninta da master ya yi mata fyaɗe, ya yi mata fyaɗen kuma ta ji ciwon sosai da yasa ta rasa jini sosai, kun san ba za'a haɗata da master ba dama, shararren mai bawa ƴan Wrestling horo, zakwakuri kuma zakaran da ya buge kowa except Black Tiger and Ronnie a faɗin birnin, namiji mai ji da karfi da lafiya ita kuma ƴar yarinyar da bata wuce Sweetie ba, da kaɗan ta fi Sweetie fa, kun ga kuwa dole karonsu ba zai yi kyau ba, ya kuwa yi mata fata fata saboda bashi da imani da tausayi, ko da yake shigarsu na banza ya ja masu ai, yana kan network ta samesa, shi kuwa ya cika aiki ya rage zafi da ita, ɗan ikka, ko da yake ba laifinsa bane, dik maza masu yin gym shegen jarabar tsiya suke da shi, saboda gym da suke yin nan yana kara buɗa jijiyoyin jikinsu ya faɗaɗa halittarsu hakan yasa sha'awarsu yake yawaita matuƙa ta yadda ba zasu iya zama babu mace a kusa ba.

So master yana tsoron fitar da ita zuwa hospital dan a iya saninsa yasan cewa budurwar Ronnie ce ita, so fitar da ita zai iya haifar mashi da babban matsala mai girman gaske, hakan hasa ya turata cikin toilet É—insa, a cikin jacuzzi ya sanyata ya rufe kofa da key, jininta na ta zuba har ta rasa ranta ba tare da ya sani ba, shi a cewarsa sai dare zai É—auketa zuwa hospital a lokacin babu wanda zai sani, bai san cewa rai ya yi halinsa ba.

Sai dai fa dik abin da ya faru Black Tiger ya sani, amma ko a jikinsa saboda bashi da wata alaƙa da hakan, dama Floris Ronnie ya kawota empeir ɗin, dan haka shi ko cin namarta ɗanye ake yi ba abin da ya sha mashi kai, shi idan kunga yana magana a kan abu to fa ta shafe shi ne, idan bata shafesa ba ko kallo baya ɗaga idanu ya yi. So dik abin da suke aikatawa yana sane da kowa.
Chapter 145 · 0% Book details