← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 242

Sashe 38

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zata yi magana idanunta suka sauka a kan uncle Jahiz dake bayansu, kai ya girgiza mata a kan kada ta faÉ—a mashi komai.

Dan haka sai ta rabu da shi a in da ta ce mashi babu komai. Ya yarda da babu komai É—in, sai ya ce mata.
"Momma zan je in yi wanka, and then am feeling hungry".

Cike da kauna ta ce yanzu za'a kawo mashi abinci a bedroom É—insa, ya je ya yi wankan. Har ta É—an samu sassauci a ranta.

Yana san tambayar ina Auta, sai dai tamkar an É—aura tongue É—insa, ya ji ta yi mashi nauyi ya kasa tambaya, haka ya wuce bedroom É—insa ba tare da ya tambaya ba, sai dai cikin ransa tunanin Autar ce kawai.

Momma kuma ta koma saman bed ta kwanta.

••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

A ɓangaren mutanen fada kuwa, neman Hoorain aka shiga yi babu kakkautawa, a nan warriors dake bakin gate suka isar da sakon ai ya fita baya a cikin kingdom ɗin.

King ne ya umarci warriors guda huɗu da su bi bayansa cikin gaggauwa su sanar da shi King yana buƙatar ganinsa.

Sosai commander Zafar ya shiga tsananin tashin hankali na abin da yake faruwa, har wani irin kaiwa da komowa yake yi a cikin Kingdom É—in, ya gaza zaune ya gaza tsaye, ya rasa sukuninsa, damuwarsa É—aya a nan ita ce meyasa Hoorain zai fita daga kingdom of power? Ina kuma ya tafi?.

MY PEOPLE'S AKWAI GAGARUMIN MATSALA! ME KUKE TUNANIN YASA HOORAIN YA GUDU? KENAN YA ZAƁI DA YA BAR MAHAIFINSA CIKIN WAHALA A KAN SHI YA KARƁI HUKUNCI?.

==========================🔥

•••••••••••••JIMETA YOLA•••••••••••🔥

A yau ne bappa ya miƙa sadakin Mairo dan cikar burinsa. Katuwar bujumar saniya ya bayar a matsayin sadakin.

Tun safe Nanne take faman zazzaga masifa tana aikin aika mashi da tsinuwa da bakaken maganganun. Amma yadda kuka san an shuka dusa a gona, ko kaɗan bai nuna alamar kamar yasan da wata halitta ita wai Nenne a duniya ba, sai hidimar gabansa yake yi, nan da kwana uku za'a ɗaura aure dan Mairo ba budurwa bace, ta taɓa yin aure sai dai bata taɓa haihuwa ba, mijin nata ne ya rasu aurensu da wata biyu.

So ba wani bikin da za'a gudanar mai tarin yawa dan dikkansu ba yara bane kuma ba saurayi da budurwa bane.

Wunin yau a gona bappa ya wuni shi da Mahreen da Mahnoor, sun bar Nenne da shakan kayan takaici.

Tun da suka je gona da safe har yamma suka dawo, tun kuma da suka je Mahnoor bata furta ko uppan ba, tana dai zaune shiru.

Da kaga idnaunta zaka san tana bala'in jin barci, dan har sun É—an kumbura sun yi jajir, jiya yadda taga rana haka taga dare, ta kasa yin barci, Jaish ne kawai a cikin ranta, tana manne da kayansa a kirjinta har wayenwan gari.

Da kyar ta iya gabatar da sallar asuba, tun da ta yi sallah kuma ta fito ta kama yin aikace-aikacenta tamkar yadda ta saba yi, bata ma jira sai Nenne ta zo ta yi mata tashin cin mutumci ba, sai ta koma ruwa kawai gwanin ban tausayi.

Yanzu haka tana zaune a cikin gonar nan gyangyaÉ—in barci take yi, sai barcin ya yi kamar zai É—auketa sai kuma ta zabura ta farka kamar wadda aka razana.

Dik abin da take ciki bappa yana sane, ya dai yi shiru ne kamar bai ganta ba, bawan Allah bashi da abin faÉ—e.

Yanzu so yake yi ya samu Arɗo su yi magana a kan wannan aure nata, tabbas Arɗo zai iya warware wannan aure, dan matsayin alkalin kauyen yake, da ace mijin Mahnoor ɗin sun san shi, sun san tushensa, sun san asalinsa ne ya tafi bai dawo ba, to wannan addini ya bada damar a jira na tsawon shekaru biyar, wata mas'haban ta ce shekaru uku in bai waiwayeta ba sai a raba auren, amma basu san shi ba, basu san daga ina ya fito ba, mutum ne ko aljani dik basu sani ba, kaddara tasa aka aura mashi ita, daga baya ya ɓace daga ganinsu to wannan a musulunci wakkwaran bincike za'ayi domin a tabbatar da mutum ne shi ko aljani, idan kuma babu ta yadda za'ayi a bincika kamar dai shi Jaish ɗin to wannan alkali yana iya raba auren!.

To yau da daddare ya shirya zai je ya samu ArÉ—o su tattauna.

••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

Zaune take karkashin bishiyar mango, ta buga uban tagumi, a zahiri zaku ga kamar tana kallon bappa da Mahreen dake aikin cire kananan ciyayin da suke fitowa bappa wajen masararsa.

Amma a baÉ—ini tunanin kyakkyawan mijinta take yi, ganinsa kawai take yi a idanunta yana yi mata gizo.

Kamar daga sama ta ji an ce............

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
=========🔥🔥🔥===========

MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

Kamar daga sama ta ji an ce. "Mahnoor".

Kin ɗago kai ta yi, dan tasan tabbas Hamma Faisal ne, voice ɗinsa ba zai taɓa ɓace mata ba.

Bai damu ba dan bata amsa mashi ko ya ɗago ta kallesa ba, sai ya nemi waje kusa da ita ya zauna yana ƙoƙarin sake yi mata magana haɗe da kai hannunsa kusa da face ɗinta da nufin zai goge mata guntun hawayen dake face ɗin nata.

Ai a miliyan ta miƙe tsaye daga kusa da shi yadda kuka san wadda aka kawowa wuta kusa da ita.
Mamaki ne sosai ya kama shi, bai taɓa tunanin zai zauna a kusa da ita ta guje shi ba, ita kuma auren da yake kanta take karewa mutuncinsa, tana daraja kanta, aurenta da kuma mijinta, so bata ga dalilin zama kusa da wani ba ko da ɗan uwan nata ne, bare kuma shi da ya taɓa santa a baya, babu wannan magana.

Miƙewa tsaye ya yi shi ma dan ya yi magana da ita. Sai dai bai kai ga buɗe baki ba da gudu tasa kai ta bar mashi wajen, dama lokacin komarsu gida ya kusa, sai kawai ta nufi gida wani irin zafafan hawaye suka fara zubo mata, ɗacin zuciyarta ya yi mata, yau da Jaish yana nan ai Hamma Faisal ba zai zo kusa da ita har haka har ya nemi yi mata magana ya nemi taɓata ba, gaskiya ta yi babban rashi matuƙa.

Da gudu Faisal ya bi bayanta, dik abin da ya faru a kan idanun bappa ya faru, ita kam Mahreen tana zaune ta buga uban tagumi, dik abin da ake yi bata da labari, ta shiga duniyar tunanin ina Jaish yake?.

Hmmmm Mahreen ma ta damu da Jaish haka bare Mahnoor da suka saba kwana É—aki É—aya, ya yi ta gwada mata soyayya, ai dole ta yi kukan rashinsa wlh.

Bappa ya kawosu gonar nan ne domin su rage damuwa, amma ina sai suka zo suka buga mashi uban tagumi suna kuncin abin da yake faruwa.

Tana shigowa cikin gida ta wuce É—akinsu da gudu, a lokacin Nenne tana cikin É—akinta, so bata ga shigowarta ba.

Kusan a tare suka shigo da Faisal É—in, da yake hankali bata gama isarsa ba, sai ya bita har cikin É—akin mijin nata, shi a dole zai rarrasheta.

Saman mattress ta faÉ—a tana cigaba da kukanta kamar wadda aka yi wa wahayin hakan.

A kan kayan Jaish da bappa ya bata ta kwanta tana jin kamshin jikinsa a jikin kaya, gani take kamar shi ne a wajen.

Kamar daga sama ta ji mutum a kusa da ita yana magana ƙasa ƙasa. Ai a zabure ta miƙe zaune, ido cikin ido ta kalli Faisal da yake dab gadan yana kallonta.

A miliyan ta miƙe tsaye, bata yi zaton ya biyota ba, tana san cewa ya fita mata a cikin ɗaki, amma kuma ta kasa yin magana, dan haka sai ta wuce ta raɓa gefensa zata fita waje.

Da sauri ya riƙo hannunta dan ta tsaya ya rarrasheta, Allah sarki, shi har yau har gobe yana santa bawan Allah.

Wani irin fisge hannunta daga rikon da ya yi mata ta yi da karfi, a zuciye cikin ɓacin rai haɗe da ɗaga murya ta furta.

"Ka sakeni Hamma Faisal!!".

Ya yi mamakin jin tsawarta a garesa, amma santa ya rufe mashi idanu da baya ganin laifinta, a baya ko ɗaga murya a magana Mahnoor bata yi, idan ma baka da nitsuwa ba zaka iya jin magana ba idan ta faɗa, tsabar yadda take magana a hankali ƙasa ƙasa cikin nitsuwa, amma yanzu rashin Jaish yasa ta fara faɗa.

"Mahnoor na ji na sakeki, amma dan Allah ki daina yin kuka kin ji? Ki yi shiru dan Allah sai ki faÉ—a mun meyasameki, meyasa kike kuka?".

Raɓawa gefensa kawai ta yi zata wuce, domin kuwa bata san ya tsaya mata a cikin ɗaki.

Bata kai ga fita ba ta tsinkayo muryar Jumma yar Inna Rabi wato amarya tana yin sallama a tsakar gida. Ai da gudu ta ƙarisa fitowa waje.

Suna haÉ—a ido da Jumma ta karisa da gudu ta faÉ—a jikinta tana kara karfin kukan da take yi, rungumeta Jumma ta yi, dama abin da ya kawota kenan, Inna Rabi ce ta turota da tazo ta jajantawa Mahnoor É—in, sannan ta rarrasheta, Allah sarki Inna Rabi tana kaunar Mahnoor sosai, dik yadda aka yi sun yi zaman amana da mamar Mahnoor sosai.

Wani irin mummunar faÉ—uwar gaba Jumma ta ji ganin Faisal ya biyo bayan Mahnoor ya fito daga cikin É—akin shi ma, ga Mahnoor É—in kuma tana kuka, abin ya yi mugu mugun bata mamaki, to me ya kai shi cikin É—akin matar aure kuma? Jumma ta jefawa kanta tambayar.

Sai ta ji kirjinta ya buga, tasan mutanensu fa wasun su ba hankali ne da su ba, kada ace wani abin ya je ya yi wa Mahnoor da yasa take kuka haka tamkar ranta zai fita.

Koke kokensu ya ja Nenne ta fito daga cikin É—akin, basu ga fitowarta ba sai dai suka ji murya tamkar saukar aradu ta daka masu wani irin uban tsawa.
Chapter 38 · 0% Book details