← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 184 OF 242

Sashe 184

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsit wajen ya yi, sun mace da kallan juna, cikin salo ya É—an motsa romance lips É—insa da nufin ya yi mata magana ba tare da ya kawar da kallansa daga kanta ba, sai ta rigasa da cewa. "Please our big bro ka faÉ—a mun ina Floris take?". Ta yi maganar tana É—an hauro da hannunsa izuwa saman lion chest É—insa ta cikin ruwan kenan. Babu riga a jikinsa fa, daga shi sai Swimming short, ya cire bathrobe É—in.

Tamkar wanda bakinsa yake yi mashi ciwo, baya san motsasu haka ya ɗan motsasu wajen cewa. "She died". Idanunsa a cikin nata ya yi maganar....... A razane ta wani irin zaro mashi eyesball ɗinta tamkar kwayar zasu firfito su faɗi ƙasa, tana ƙoƙarin yin magana cike da tashin hankali ya yi saurin sanya hannunsa ya rufe mata baki, a hankali ya girgiza mata kai alamar a'a ta yi shiru. With his lion voice ya fara yi mata bayani wanda bai bawa kowa damar sauraron abin da yake faɗa ba, sai da ya kai karshe daga nan ga rufe maganar nasa da cewa ta san yadda zata yi da Ronnie kada ta bari ya birkice sosai, ta taya shi ɓoye mutuwar Floris har zuwa wani ɗan lokaci, kada su sanar da Ronnie.

Ai yadda kuka san ruwa ya cinye Sweetie, ta kasa motsawa daga in da take, tamkar wadda ta sume, idanunta a kansa kuma babu ko kyaftawa.

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
========🔥🔥🔥=========

MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

51

🔥🔥🔥🔥BLACK WORLD🔥🔥🔥🔥

Kurawa face ɗinta idanu ya yi, sai yau ya tabbatarwa da kansa cewa Sweetie kyakkyawar gaske ce, ta sume mashi amma idanunta a buɗe, ɗan lumshe idanunsa kaɗan ya yi tare da sake buɗesu a kanta, hannunsa ya ɗago, tafukan hannun nasa ya ware tare da shafa face ɗinta da shi, take ta ja doguwar numfashi, da alama magic ya yi mata ta farfaɗo. Kamar mai raɗa haka ya fara raɗa mata cewa kada ta bar Ronnie ya fahimci abin da ya faru, ta yi mashi dabara, daurewa ta yi ta yi ta mazan cewa sai dai idan shi ma zai yi mata wani alkawari, in ya yi mata hakan ita kuma ta yi mashi alkawarin Ronnie ba zai taɓa shiga wata damuwa ba izinin Allah.

Jama'a ku tafawa addu'a, lallai ne addu'a bata taɓa faɗuwa ƙasa banza, sai dai jinkirin amsawa, da izinin Allah addu'ar Sweetie a kansa ta karɓu, black heart ɗin ta fara sassautawa!.

Jinjina mata kai ya yi alamar ya yarda da batunta tin ma bai ji wani irin alkawari bane, Ronnie amanarsa ne, kun san da cewa amana mahaifinsa ya bar mashi Ronnie? Kun san da cewa sai da ya rokesa da kada ya bar hawayen Ronnie ya zuba a banza?. Kun san da cewa kafin mahaifinsu ya rasu ya yi wa baban nasu alkawarin in dai yana numfashi to ba zai taɓa barin hawayen kanin nasa ya zuba ba? Shiyasa kuke ga zai iya aikata komai a kan kanin nasa, kuma yana bala'in sansa na haƙiƙa shi ma, ba wai dan iya alkawarin da ya ɗauka bane yasa yake kula da shi, yana kaunarsa sosai.

Ɗaga ƴan kafafunta ta yi tana san kai tsawonsa dan ta yi mashi raɗa a kunne, sai dai ina, bata iya kaiwa tsawonsa ba, ya fita nesa ba kusa ba, yana da tsawo sosai. Ganin hakan yasa ya rage tsanwonsa ya ɗan rankwafo kanta, hannu tasa ta saƙalo wuyansa kafin ta gwada sake ɗaga kafa ko zata kai. Sai dai kash bata kai ba, hakan yasa ya ɗagata cak sai saman lion chest ɗinsa, hakan ya bata damar kwanto kanta a saman shoulder ɗinsa, ta kai ɗan bakinta saitin kunnnesa, nan ta fara yi mashi raɗan yarjejeniyar da zasu yi kafin ta yi mashi aikin kula da Ronnie, idan ya aminta tabbas zata kula da Ronnie sosai wajen sanya shi farinciki.

Hakika maganganunta sun zo da tsauri, sai dai kuma farincikin Ronnie ya fi mashi komai, kuma babu in da Ronnie ɗin yake samun farinciki na wuce misali face a wajenta, dan haka yazamar mashi dole ya aminta da wannan yarjejeniya in ba haka ba akwai matsala. Shiru ya yi yana tinanin ya amince ko kuwa ya daure ya juri tashin hankalin da Ronnie zai shiga?. A wannan hali Ronnie ya shigo wajen ya samesu, fuskarsa ɗauke da damuwa matuƙa ya ƙariso in da suke.

Ai yana sauke kallansa a kan yayan nasa da Sweetie bai san time da ya saki cool murmushi ba, sun yi matuƙar burgesa, da sauri ya tsugunna a gaban pool ɗin, cikin sanyin murya ya ce. "Wow you guy's looks so very cute and amazing"....... Maganarsa ya fargar da Black Tiger har ya yi saurin zare kallansa daga kanta, kamar wani maras gaskiya ya yi saurin saketa ya kuma ɗan yi ƙasa kaɗan ya kara lumewa a cikin ruwan kaman mai san ɓoye wani abin. Ita kuwa, da tsantsar tashin hankalin da take ciki yaki ɓoyuwa a kan face ɗinta ne ta juyo da kallanta ga Ronnie, tamkar zata yi kuka, ta ƙasa yin magana, dan yanzu ganinsa yasa wani irin tausayinsa ya kamata.
Take yanayin face É—in Ronnie ya canza, dan ganinta cikin damuwa bai yi mashi ba, kamar mai tsoronta ya ce. "Lovely sis big bro ya yi maki wani abin ne?". Ya yi maganar yana satar kallan Black Tiger ta wutsiyar ido.

Kai kawai ta iya girgiza mashi alamar a'a ba tare da ta yi magana ba. "Big bro me ka yi wa lovely sis ɗita?". A ɗan shagwaɓe ya yi maganar. Banza da shi Black Tiger ya yi, sai ma ya kara lumewa cikin ruwan, tamkar bai san da su a wajen ba, da alama kuma akwai abin da baya san su gani a jikinsa shiyasa ya yi ƙasa a cikin ruwan........ Ronnie fa ya zo da kokensa ne a kan bai ga iyayen Floris ba, ya tambayi mutanen birnin kuma kowa ya ce mashi bai gansu ba, shi ne ya dawo wajen yayansa da kokensa dan ya nemo mashi su, amma yana tarar da su cikin wannan yanayi ya tsinci kansa a cikin farinciki maras misaltawa.

Rarrashin Sweetie ya hau yi yana ce mata ta yi hakuri zai rama mata idan ma yayansa ne ya yi mata wani abin, ita dai da okey kawai ta amsa mashi, amma na ciki kam yana ciki. Sai da ya tabbatar ya sanyata ta yi murmushi, sannan ya juya ya ce da Black Tiger. "Big bro ina iyayen Floris?". Ai Sweetie bata san lokacin da ta ce mashi. "Sun gudu sun bar birnin nan wai saboda big bro ya kona masu Æ´an uwa".

Ɗan zaro idanu Black Tiger ya yi jin ta fitar masu da hanyar da bai zata ba, dama yana tinanin abin faɗawa Ronnie, gaskiya Sweetie she was very smart, ya jinjinawa ƙwaƙwalwarta wajen iya fito da mafita cikin ƙanƙanin lokaci, sannan ransa ta sanyaya matuƙa da samun mafitarsu. Shi kuwa Ronnie ido ya zaro, kamar zai ɗaga murya, sai kuma yasa kukan shagwaɓa tare da cewa shi lallai bai yarda ba! Dole big bro ya nemo mashi in da suke, dan shi yana kaunar Floris, yana san ta dawo su cigaba da rayuwa kamar da. Nan ne fa Black Tiger ya samu damar ce mashi zai nemo mashi su soon ya kwantar da hankalinsa, yana magana yana satar kallan Sweetie da ta tsare lip's ɗinsa da kallo.

Ajiyar zuciya Ronnie ya sauke, ya ji sanyi a ransa za'a nemo mashi su. Sweetie ce ta riko hannunsa ɗaya cikin nata, kamar mai raɗa ta ce matso ka ji wani abu lovely bro. Matsar mata da face ɗinsa ya yi yana ɗan murmusawa. Matsowa ta yi dab kunnensa, raɗa ta fara yi mashi tana sakin murmushi,. A hankali hankali murmushin dake saman face ɗinsa ta fara faɗaɗa alamar kalamanta akwai sugar, suna shigarsa yadda yakamata. Satar kallansu Black Tiger ya fara yi yana mamakin irin shakuwar dake a tsakaninsu, a yanzu fa Ronnie ya fi farinciki idan yana tare da ita sama da idan yana tare da shi, abin akwai mamaki. Tsabar daɗi da murnar jin kalamanta bai san lokacin da ya afka cikin ruwan ba shi ma, a jikinta ya faɗa hakan yasa suka yi kasan ruwan, dan bata da karfin ɗaukarsa. Shi dai Black Tiger abin ya birgesa matuƙa, suna kashe shi idan suna tare!.

Juyawa Ronnie ya yi cikin sauri ta dawo saman jikinsa, sannan suka É—ago saman ruwa, take ta fara jan numfashi da karfi karfi, saboda ta dannu kam. Riketa Ronnie ya yi yana faÉ—in ta tsaya ya hura mata numfashinsa dan nata ya daidaitu. Sai dai bai kai ga yin hakan ba take ta dawo daidai tamkar wadda aka yi wa magic, runguneta Ronnie ya yi yana faÉ—in sorry a gareta. ÆŠan rungunesa ita ma ta yi kafin ta amsa mashi da ba komai. Cikin wasa ya ce. "Let play a game". ÆŠan zaro idanu ta yi, game kuma a cikin ruwa, ta jefawa kanta tambaya a cikin zuciya.
Tana can tana tinani Ronnie ya zaro hanki (handkerchief) daga aljahinsu, dik ta jiƙe da ruwa, ɗaure mata idanu ya yi kafin ya saketa, ya sumbaci lallausan kumatunta sannan ya ce to ta kama shi a cikin ruwan idan ya kirga one to ten. A cikin ranta ta ji da biyu Ronnie ya ce su yi wannan wasa, amma ba zata ki yi ba ko dan alkawarin da ta ɗaukawa yayansa na sanya shi farinciki na musamman, so zata yi dik abin da yake so matsawar bai saɓawa shari'a ba.
Chapter 184 · 0% Book details