← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 119 OF 242

Sashe 119

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna shigowa cikin parlourn saura kaɗan su zube ƙasa gabaɗayansu, a hanzarce momma ta miƙe ta taresu. Kuka ya kara sakawa mai sauti yana nunawa momma cikinsa babu bakin yin magana. Wlh idan ciwon guyson ya tashi sai kun tausaya mashi, ba karamar wahala yake sha ba...... WAI MENENE DALILIN WANNAN CIWO NA TSAWON SHEKARU HAKA? AKWAI AYAR TAMBAYA GASKIYA, TO MUJE DAI ZUWA.

GabaÉ—aya ya sakewa momma nauyinsa, saman sofa ta kwantar da shi tana tambayar lafiya tana kallan Mahnoor. Cikin natsuwa Mahnoor ta ce ita ma bata san me ya same shi ba, kawai ta gansa ne a bakin kofar shigo part É—in.

Riko hannayensa momma ta yi tana tambayarsa meyake yi mashi ciwo. Cikin tsananin ciwo da azaba ya fara nuna mata cikinsa yana kara tsananta kukansa.

Da yake momma tasan irin azaban da yake sha idan ciwon ya tashi sai hankalinta ya tashi sosai. Wayarta ta ce Mahreen ta miƙa mata, dama wayar tana kusa da ita.

Ɗauko wayar ta yi ta miƙa mata tana kallan guyson ɗin.
"Ji fa, kato da shi ne yake yin kukan ciwo, Adda Mahnoor kalle shi fa, wannan anyi wawa gaskiya". Tana magana tana harararsa. Ko kunyar idanun mommarsa bata ji ba take yi mashi wannan iskancin.

ÆŠan buge mata baki Mahnoor ta yi tana kallanta. Hannu ta É—aura a saman bakin nata ta hau murjesa tana faÉ—in. "To me na yi maki zaki buge mun baki?".

Momma dai hankalinta baya a kansu, ƙoƙarin kiran number Dr Raj kawai take yi. Ta kuwa yi sa'a bugu ɗaya ya ɗauka, a lokacin ya bi bayan Ramish yana faɗa mashi Leesharh tana da buƙatar karin jini idan ba haka ba zasu iya rasata, an gwada jinin Bilal and shi Dr Raj ɗin dik jininsu bai yi irin nata ba, o negative take da shi, ashe shiyasa take da shegen janircewa da taurin rai, jinin sojoji ke gareta.

Dr Raj ya yi iya yinsa a kan Ramish ya tsaya a gwada jininsa idan ya yi a sanya mata ya ce ba zai bata jini ba, dan yana jin nau'in jinin nata yasan irin nasa ne, bama sai an gwada shi ba, amma dai ya ce ba zai bayar ba, a sayi sabo a saka mata ko kuma a nemo ƴan uwanta dik a in da suke su zo su bata, dan ta bada ranta ta cecesa ba wai hakan yana nufin shi sai ya tsaya mata a kan komai ba, ya yi abin da yakatama ya yi, shi yanzu ma ya fara zarginta ne, dan da ya zauna ya yi tinani ƙwaƙwalwarsa ta basa dik yadda aka yi tana da masaniya game da komai, ashe banza kwanaki ya saketa, ya yi kuskure, dik yadda aka yi ta san komai, wannan abin ya baƙanta mashi da yasa ya ji ya tsani zuwa in da take.

Tun da ya sanya kafa ya bar ɗakin da ya cire mara bullet bai sake waiwayarta ba, Dr Raj yake kula da ita karkashin umarnin Bilal, abin kuma da baku sani ba shi ne, kamar Bilal ne yake kara tunzura Ramish a kan Leesharh, saboda Ramish ɗin ya ja baya da ita. Amma shi Bilal abin da bai sani ba shi ne, Ramish yana amsa mashi dik abin da ya faɗa mashi da fatar baki ne kawai, ba wai dan yana ɗaukar hakan a matsayin gaskiya ba, in short da Bilal da Leesharh dikka yanzu suna a karkashin sarrafawar Ramish ɗin ba tare da sun sani ba, dik yasa masu question mark, dik bincike yake yi a kansu ta ƙarƙashin ƙasa domin ya gane gaskiyar abin da yake faruwa.

Waɗan can guy da suka harba a hall ɗin nan da Ramish ya je ya gansu sai da ya razana matuƙa, domin kuwa ya sha ganin ɗayan guy ɗin a tare da Bilal several times, and akwai hotunansu tare da Bilal a wayar Bilal ɗin, hakan yasa Ramish ya kara tsananta zarginsa a kan Bilal matuƙa.

And kuma yaki bari Bilal yaga gawarwakin mutanen, hakan ma tana daga cikin aikinsa, lokacin da zai je h-q duba mutanen Bilal ya so su tafi tare, amma sai ya ce a'a zai je shi kaÉ—ai, ashe kuwa gara da ya tafi shi kaÉ—ai É—in, dan yana ganin mutumin ya ce ba zai bari Bilal ya fahimci komai ba, dan in da gaske Bilal yana da masaniya a kan komai idan yasan wanda suka kashe mutuminsa ne to zai iya katsewa Ramish yunkurinsa na gane suwaye suke da sa hannu a lamuran. Shiyasa ya canzawa kowa a gidan yanzu, ya kuma dai'na bari suna samun damar haÉ—uwa da shi, yanzu haka tin safe Dr Raj yake san haÉ—uwa da shi ya rokesa da ya taimaka ya bawa Leesharh jini amma ya gagara samun damar ganinsa, kuma yana cikin gidan, ganinsa ne ya hanasu dama.

Sosai Bilal ya shiga damuwa a kan É—auke mashi wuta da Ramish ya yi, yanzu haka tun jiya bai samu damar haÉ—uwa da Ramish É—in ba, ya yi ya yi su haÉ—u abin ya gagara.

A ɓangaren Ramish ɗin kuwa, wlh jinyar kansa yake yi sosai, domin kuwa dik wasu bincike da zai yi mutanen da zai zarga suna da sa hannu a yunƙurin kashesa sai ya gansu a tare da Bilal, duniya yau Ramish ya rasa me yake yi mashi daɗi, ya shiga tashin hankali da kunci da bai taɓa shiga makamancinsa ba, tun daga jiya kirjinsa take yi mashi wani irin azabbabben ciwo mai tsananin gaske har yau, haka yake daurewa yana aiki.

Wani lokaci sai ya ji kamar ya dakatar da binciken nan domin fargabar abin da zai iya cin karo da shi, yana tsananin fargabar abin da zai binciko, zuciyarsa tana rawa a kan binciken nasa, sai ya ji kamar ya haƙura kawai, gara ya zauna da Bilal ɗin a haka bai binciko gaskiya ba sai ya fi mashi, amma kuma yana san sanin gaskiya ta wani fannin.

••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

Cikin natsuwa Dr Raj ya yi picking call ɗin momma. Hankalinta a tashe ta fara zayyana mashi ciwon guyson ya tashi, ai yana daga zaune bai san time da ya miƙe tsaye ba, muryarsa a ɗan dishashe ya ce what.

A tinanin Dr ciwon Guyson zata É—auki a kallah shekaru biyu ko uku kafin ta sake tashi, amma sai suka ga akasin haka. A hankali ya koma ya zauna tare da haÉ—e natsuwarsa waje guda, sannan ya ce momma ta yi gaggawan kiran likitoci da wuri so zo, lokacin yi mashi aiki kuma bata yi ba, dan bayan shekara É—aya ake yi mashi, so da yin wancan aikin bai kai shekara ba yanzu, to me matsalar? Dr ya tambayi kansa.

"Bari in kira Jaish ko Jawad su yi gaggawar kiran Drs yanzun nan, idan Drs sun iso sai mu yi waya dan su duba mun shi su ji menene matsalar kuma". Cewar Dr. Jinjina kai momma ta yi tare da katse kiran ta dawo da hankalinta a kansa, a hankali ta fara tofa mashi addu'oi tausayinsa yana kara ratsa mata zuciya.

Zee da Mahnoor tun da suka ga Momma ta tashi hankalinta har haka sai suka fahimci lallai ciwon nasa babba ne ba karami ba. Ita ma Mahreen yadda taga momma ta tashi hankali sosai sai ta sha jinin jikinta, lokaci guda ta ji tausayinsa ya kamata, a hankali ta dawo kusa da momma ta zauna suka shiga tofa mashi addu'oi a tare.

"Mahnoor kira mun mijinki idan yana ɗaki". Cewar momma, ta yi maganar ba tare da ta kalli Mahnoor ɗin ba. A hanzarce ta amsa da to haɗe da miƙewa ta nufi waje. Gabaɗaya Zee jikinta ya yi sanyi, sai ta ji tausayin guyson ɗin ya kamata, barema yadda taga yake juyi kamar zai faɗo ƙasa daga saman sofar sai momma ta taresa, sam baya a cikin hayyacinsa, kuka kawai yake yi yana dafe da ciki. Kun san ciwon cikin maza babbar azabace babba sosai.

Dab Mahnoor zata shiga part ɗinsa uncle Abbas kuma yana fitowa, karo suka ɗan yi, baya ta yi da sauri tana sunkuyar da kai ƙasa. Cikin girmamawa ta ɗaga mashi gaisuwa. Fuskarsa babu annuri sam ya amsa mata gaisuwar, tsabar tashin hankalin da suke ciki ma sam bai lura da wadda ta ɗaga mashi gaisuwa ba, shi ya zaci Chuchu ce ma, bai wani tsaya ba, ya yi gaba ma kafin ya amsa gaisuwar tata.

Ciki ta shiga tana waigo uncle Abbas ɗin har ta kusa daka tuntuɓe. Bakinta a ɗauke da ɗan siririn sallama ta tura kofar bedroom ɗinsa, bata jira ya amsa ba ta shige ciki. Tana sauko kanta dai'dai lokacin ya miƙe tsaye yana zare idanunsa a kan screen ɗin wayarsa dake hannunsa, kamar dai wani abin tashin hankalin ya gani.

Me kuke tinanin ya gani?.

Jin an turo kofar yasa a slow ya ɗago da kallansa a kanta, ɗayan hannunsa na dafe da kansa dama, a hankali ya koma gefen bed ɗinsa ya zauna idanunsa a kanta, fuskar nan tasa kamar hadari. Sosai ta tsorata ganin halin da yake ciki, sai ta ji shakkar tinkararsa ta isar mashi da saƙon momma, kamar ta juya a guje ta fita, amma tina cewa sakon momma ce sai ta daure ta nufesa.

A gabansa ta tsugunna tana faɗin. "Barka da safiya Hamma".......... Wani irin kallan kasan idanu ya bita da shi, kansa ne yake sara mashi tamkar zai fashe, idanunsa sun kara tsananta ja sosai. Sam bai amsata ba, bai ma da niyar amsawa. Ganin hakan yasa ta kara yin ƙasa da murya cikin girmamawa ta ce. "Hamma momma ta ce kazo Yah Omar bashi da lafiya.........."

Zaro mata idanunsa da ya yi yasa ta yanke maganar tana sunkuyar da kanta ƙasa da sauri. Yau wani irin kallo yake binta da shi kamar bana lafiya ba, kamar kuma na haushi ko na tuhuma.
Chapter 119 · 0% Book details