Sashe 85
Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai dai kuma wani abin guda, dole ta tilastawa su commander Zafar yakar Daular Qahtaniyawa dik da a lokacin da suka dinfari wajen King Al-Mustapah ya sanar da su shi bai É—auki gimbiya Zunaira ba, kin yarda da shi suka yi dik da commander Zafar yasan gaskiya King Al-Mustapah ya faÉ—a.
Commander ya jima a fagen yaki, idan gaskiya ake faɗe ya sani, haka zalika idan karya ne ma ya sani, amma haka ya take wannan sanin dan basu da wata mafita da ya wuce su yakesu, a kan umarnin King Zuhair suke yanzu, dik wata hanya da Aunty MieMie ta buƙaci da su bi dan nemo Zunaira sun bi amma babu nasara, hakan ya tilasta masu dawowa kan umarnin King suka aiwatar da yakin.
Sai dai kuma kash, ko da suka yaƙi Daular Qahtaniyawa babu Zunaira babu alamarta a ciki, sun dai yi masu ɓarna na King karawa, King Al-Mustapah ya yi mubaya'a har ya gaji amma sam babu alamar King Zuhair zai karɓi nadamarsa ya kuma yafe mashi, kafiyar bala'i King Zuhair yake da shi wlh, idan ya tambara magana babu mai iya sanya shi ya canza ya yi ta kenan.
A ranar da Auntynsu Jawad da tawagarta suka bar Kingdom of power a ranar su commander Zafar suka kaddamar da wannan yaƙin tare da dawo da labari maras daɗi wanda sam King bai so ji ba shi ne babu gimbiya Zunaira a Daular Qahtaniyawa.
Sosai ran King ya sake sosuwa, hankalinsa ya tashi, yau shi da yake kwantarwa da Momma hankali a kan wannan case ɗin, sai yazamana ita ta juyo take kwantar mashi da hankali saboda bala'in ya kai mashi bala'i, ga ɓatar Hoorain assistant commander su, abin sai ya haɗe mashi biyu.
A can ɓangare kuma, wannan dai sadauki mai ɗauke da fuska kamar ta Hoorain namu ko ma muce Hoorain namu shi ya jagoranci tawagar mayakan Queen Zarina izuwa kingdom of power.
Tabbas ɗayan biyu ne, wannan sadauki ko dai tsafi suka yi amfani da shi wajen sanya mashi irin face ɗin Hoorain dan su firgitar da Kingdom of power, dan kunsan sun san komai ta hanyar mammie, so sun san bayyanar Hoorain a cikin mayaƙansu zai iya sanyawa su yi nasara a kan Kingdom of power, dan mamakin da dangerous warriors zasu shiga ganin Hoorain a cikin mayakan Queen Zarina shi zai iya tallafa masu su yi nasara sosai.
Abu na biyu kuma shi ne ko kuma robbot suka sanya mai irin zubin halittar Hoorain, ɗaya cikin biyun nan dole suka yi, dan sak Hoorain ɗinmu yake babu banbanci komai ƙanƙantarsa.
To shi dai ya jagoranci tawagar Queen suka nufo su King wanda a lokacin King Al-Mustapah yana ta neman ta yadda za'ayi su shirya da King Zuhair, hakan yasa dik da King ya yakesu bai sa ya janye kudurinsa ba, sai ya haÉ—a sauran mayakansa da suka rage ya fita ya tari rundunar mayakan Queen Zarina wanda already King Zuhair ya samu labarin zuwansu, sai kuma ya samu labarin King Al-Mustapah ya tare mashi yakin.
Abinku da jinin sarauta mai karfi, dik da ya ji hakan bai wani nuna mamaki ko kaÉ—an ba, sai ma ya nuna kamar bai san suna yi ba, ya umarci commander Zafar da ya haÉ—a kan wasu zataran warriors su fita su taya su King Al-Mustapah yaki dan su kaÉ—ai ba zasu iya da bala'in Zarina ba.
Hakan kuwa aka yi, suka fita domin tallafa masu.
••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥
Jawad bai zame ko'ina ba sai part na King da gudu, Jaish bai rabu da shi ba sai da ya bisa har can, dan yau ya ci alwashin sai ya kuntatawa Jawad ya ji idan da daÉ—i shi ma yadda ya ja mashi kima da mutuncinsa a kan titi.
Dai'dai lokacin King ya kammala shirinsa na nufar fada zai fito ya yi breakfast kenan. A bayansa Jawad ya laɓe yana haki yana hararar Jaish da ya tsaya ta gabansa yana bin daddyn nasu da kallo.
Abin ya yi matuƙar bawa Jaish mamaki ganin rama a tatare da King, tun da ya dawo dama basu wani zauna sosai ba, so bai wani san halin da suke ciki ba.
"Daddy ka ce wannan tuzurun ya rabu da ni, dan kawai na yi aurena na barshi shi ne yake jin haushina zai fasa mun baki yajawa amaryata asara". Cewar Jawad kenan, yana magana yana kara laɓewa a bayan King.
Bakinciki ne ya ƙara lulluɓe zuciyar Jaish, lallaima Jawad ya raina mashi wayo yake faɗe a cikin ransa. King da ya rasa abin faɗe ai binsu da ido kawai yake yi, a ransa yake faɗin tun suna yara suke wannan tsiya, har yanzu basu dai'na ba!.
" Ko ka zo ko kuma yau sai dai mu kwana a nan". Jaish ya faɗa ransa a ɓace, shi serious ya ɗauki abin, Jawad kuma wasa yake yi, shi fa da ace Jawad wata ya aura ba kanwarsa ba to da da sauki abin, amma tsabar cin mutuncin ya kama ya auri Chuchu da ya gama yi masu jan ido, yanzu haka kawai ya janyo mashi wani abin da ba haka nan ba, wlh ba zata saɓu ba.
Amma kuma a matsayinsa na yayan Chuchu ya ji mata daɗin ta samu mutumin kirki wanda yasan ba zata taɓa yin kuka ba a duniya, wani ɓangare na zuciyarsa ya so da ace Auta ma Jawad ya aura, kunga masoyiyar kanwarsa ba ita ba kuka, kuma har abada in dai tana matsayin matar Jawad shi zai cigaba da kula da ita.
Sai dai kash, tsakanin Jawad da Auta babu aure, shiyasa ma ya so Chuchu shi ma, da akwai aure kun san dole ita zai so shi ma, ko dan ya ramawa Momma alkhairinta a garesa, sannan kuma Auta ta fi Chuchu komai dik da ita ma Chuchun ba baya ba.
Amma babu halin ya aure Auta saboda ya sha nonon Momma a tare da Jaish, kunga babu aure a tsakaninsu, matsayin yaya yake a wajenta, kuma fa ba wani sosai ya sha nonon momma ba, kawai dai rabon auren ƴaƴan momman ne ya fita a ƙaddararsa.
"Malam bafa zan fito ka fasawa amaryata bakina ba, wai kai dan kana gwauro sai ka zalinceni ne? Daddy hasada yake yi mun dan shi bashi da wadda take son shi, ka canza wannan bakin halin naka sai ka samu koda kuyanga ce ta ce tana sonka a lallaɓata ku shiga daga c............."
Kasa kai aya ya yi sakamakon hannu da Jaish ya kai zai yi mashi wata capka ya zille yana harararsa. Ran Jaish ya ƙara ɓaci, lallai ma Jawad ya kai in da ya kai, shi yake faɗawa magana dan ya yi aure? Danasanin tafiyar da ya yi ya shiga yi, dan da yana nan wlh ba zai bari ayi wannan aure ba.
Sai yanzu na gane rabon auren Jawad da Chuchu ne ya kawar da Jaish daga kingdom of power, kun san rabo fa har kisa tana yi, babu abin da bata sakawa, so da alama rabo ta kawo sanadin wannan tafiya, dan kuwa tabbas da yana nan ba zai yarda ayi wannan aure ba, sai ya hana ya zuga a bawa Rizwan ita tun da shi Dubai zai wuce da ita.
Kaucewa capka da Jaish É—in ya kawo mashi ya yi, yana faÉ—in. "Daddy ka mun tsakani da wannan gwauron, ni yanzu ba class É—insa bane, haka kawai zai cutar dani ya zalunceni".
King da ya fahimci Jawad wasa yake yi Jaish kuma da gaske ya ɗauki abin sai ya yi ƙoƙarin yi masu tsakani kada faɗar gaske ta tashi, yasan halin kowannensu, waɗan nan kalamai na wasa da Jawad yake jifan Jaish da shi zai iya haifar masu da gagarumin faɗa, shi kuma Jawad ɗin sam bai lura da gaske Jaish ya ɗauki abin ba. Kuma kunsan akwai wani bakinciki a gefe na batun Mahnoor a zuciyar Jaish, sai abin ta haɗe mashi yazama haushin kowa da komai yake ji.
"Ya isa haka, menene yake faruwa?". King ya faÉ—a yana kallon Jaish da har idanunsa sun kaÉ—a sun yi jajir kawai dan ance Mahnoor ce matarsa.
Ransa a matuƙar ɓace ya zayyanewa King dik abin da yake faruwa, daga karshe ya rufe da cewa. "Ni daddy tun banga yarinyar ba i hate her, kuma bana san in ganta ma a rayuwata, ka ce da momma bana so ta mayar da ita in da ta ɗaukota in ba haka ba kome ya faru alhaki a kan wuyarku, coz i really hated her more than your expectations".
Kalamansa cike suke tab da gaskiya, tabbas ya ji ya tsani Mahnoor kuma baya san ganinta, kada kuga laifinsa, dik abin da zai faru bashi da laifi, ya sota ne a baya lokacin da yake matsayin Hamma wanda ko sunansa na ainahi bai sani ba, yanzu kuma yana amsa matsayinsa na Prince Jaish Zuhair Abdul Malik ne, kun san kuma babu ta yadda za'ayi ace Jaish ya karɓeta haka nan tun da dani da ku dik mun san halinsa a baya, kunga kuwa abu ne da ba zai yiwu ya yarda ba duba da yanayinta.
King yana ƙoƙarin yin magana ya katsesa da cewa. "And why daddy zaka aurawa Jawad Jannat? Meyasa?".
A É—an takaice King ya ce. "Coz he love her".
"Love". Ya maimaita kalmar yana dallawa Jawad wani irin kallon wanda idan ya yi wa su Chuchu shi na tabbata ko yawu ba zasu iya haɗiya ba saboda azaban tsoronsa. Izuwa yanzu Jawad ya fahimci da gaske ran ɗan uwansa a ɓace, kuma shi kansa ya ji ɗacin cewa da aka yi wannan ƴar kauye da Momma ta dawo da su ɗin ne matar ɗan uwansa, shi ya zaci ma wasu ƴan aikin momma ta je ta kwaso, amma kawai sai ace matan ɗan uwansa, ina gaskiya ko shi bai aminta da wannan ba, ransa ta sosu matuƙa, he feel he's blood brother pain, wannan ai ƙaskanci ne a ganinsa.
Lallai jikokin Akka sun rai'na capacityn Mahnoor sosai.........😅