← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 179 OF 242

Sashe 179

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mamaki tamkar Ude zai sume a wajen ne ya bayyana a saman face É—insa, da kyar ya iya cewa. "Rishan ni yau kake kira da Ude?"....... Wani irin kallan kuna ya bisa da shi kafin ya yi wurgi da hannunsa da ya rike, sannan a gadarance ya ce. "Da kana da wani suna ne bayan Ude?". Babbar magana!.

Kum san menene yake tsakanin Ude da Rishma and Rishan? To Ude babban yayansu ne, ya juya masu baya saboda Queen Zarina, ba zaku taɓa fahimtar wani kulli bane a wannan masarauta sai nan gaba kaɗan, ta ya aka yi su Rishan suke matsayin musulmai shi kuma Ude dake matsayin babban yayansu yake katon krista? Ya aka yi Ude dake matsayin mijin Queen bai zauna a kujerar mulki ba sai ita? Meyasa yake biye mata kaman ita take da shi? Meyasa ya juyawa ƴan uwansa dikka baya ya bi addinin matarsa ya kuma damka mata ragamar garin a hannunta tana yin yadda ta so? Ina dattijo mahaifinsu Rishan yake? Menene dikka wannan rikicin. Gaba kaɗan zaku sha mamaki a kan wannan masarauta da kullin dake cikinta, akwai gagarumin case.

Sumar tsaye Ude ya yi, ya ƙasa yin wani ƙataɓus, bai taɓa zatan kannensa zasu juya mashi baya ba, su kuwa sun gaji da yi mashi nasiha ne, sun gaji da biye mashi suna sa ran zai juyo ya musulunta su koma yadda suke a da can baya, ya karɓi karagar mulkinsa ya cigaba da gudanarwa bisa adalci kamar a baya, sun gaji da dik abin da yake yi, yanzu babu wani sauran ɗaga kafa, dole su yi fito na fito da shi dan su samu salamar ciwon dake cikin zuciyarsu.

Wucewa Rishan ya yi ya riko hannun Rishma tare da janta suka fice daga cikin parlourn. Ko sau ɗaya Queen Zarina bata yarda ta ɗaura idanunta a kan Rishan ba, alamar akwai wata a ƙasa kenan, ta dai bisa da kallo da ya juya yana tafiya tana mamakin rikiɗewarsa..... A gabaɗaya kingdom of Justice ɗin nan, babu cikakken jarumi na cikin gida biyun Rishan, shiyasa suke shakkarsa, zance na gaskiya har Ude shakkarsa yake yi, idan yana magana a waje ba'a tankawa, namijin gaske ne. Har suka kurewa ganinsu Ude bai iya furta word ba, ya shiga ruɗani. Tsafin Zarina ya kasa yin aiki a kan mutane biyun nan, wato da Rishan da Rishma, kullum suna tare da Dattijo Muzaffar shi yake taimaka masu da shawari a kan dik abin da ya taso masu, su biyu suke rayuwarsu bayan juya masu baya da yayan nasu ya yi!.

Sai dai suka fice daga parlourn ne ya dawo da kallonsa a kan Zarina dake tsaye kamar bata a wajen, a hankali ya buɗi baki zai yi mata magana kenan ta yi saurin ɗaga mashi hannu. "Har yanzu yara ne, ka yi masu uzuri". Ta kai karshen maganar tare da wucewa fuuuuuu kaya na jan ƙasa, kamar wata kunfa ta wuce sama, tana wani taku mai kama da magic walk, sannan fuskarta ya nuna tabbas akwai wani abin, sai dai ita baka taɓa iya karantar ina ta dosa, baka sanin me zata aikata sai lokacin yin abu kawai kaga aiki da cikawa, ba shakka akwai abin da take da niyar yi a kan Rishan da Rishma, saboda yadda ta kallesu da suna barin parlon ba kallan lafiya ba. Matsawa kusa da stair case ɗin Ude ya yi yana cigaba da kallonta har ta kurewa ganinsa. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya juya ya koma fada.

🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥

Zaune suke cikin wani haÉ—aÉ—É—en park mai matikar É—aukar hankali, ya kaita yawace yawace sosai daga karshe ya biyo da ita a nan dan su É—an huta. Sai dai fa dik wannan yawon da suka yi taki sakan jiki da shi. Dik in da suka je tana takure waje guda, bata ma san motsawa, dan dai yana matsa mata ne yasa take yarda tana binsa.

Zaune take saman wani tsadadden kujera dake cikin park É—in ta gefe tana kallan yadda big girls suke nishaÉ—i suna kaiwa da komowa, ta yi nisa cikin tinanin mafita a gareta, so take yi dik ta yadda za'ayi ta guje mashi, dan ta É—aukarwa kanta alkawarin ko zata ci amanar kowa ban da Sharifat da Jasra na gidan AAJ, dan waÉ—an nan mutane biyun sune duniyarta, dan haka a kan ta auri Ramish gwara ta gudu ta bar gidan Abbie, ba zata zauna ba.

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
========🔥🔥🔥=========

MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

50

Zaune take saman wani tsadadden kujera dake cikin park É—in ta gefe, tana kallan yadda big girls suke nishaÉ—i suna kaiwa da komowa, ta yi nisa cikin tinanin mafita a gareta, so take yi dik ta yadda za'ayi ta guje mashi, dan ta É—aukarwa kanta alkawarin ko zata ci amanar kowa ban da Sharifat da Jasra na gidan AAJ, dan waÉ—an nan mutane biyun sune duniyarta, dan haka a kan ta auri Ramish gwara ta gudu ta bar gidan Abbie, ba zata zauna ba.

Tana can tana tinani shi kuma ya yi masu oder kayan sha mai tsabta, tsada da haɗuwa, bata san time da ya yi ba sai gani ta yi an ajeye mata abu a gabanta. A hankali ta ɗago da kanta ta ɗan saci kallansa ta ƙasan ido, while shi ma ita yake kallo, ya ga ta saci kallonsa, amma sai ya basar kamar bai gani ba ya ce mata bismilla ta sha mana. Kai ta ɗan girgiza mashi kafin ta amsa mashi da a'a ba zata sha ba ta ƙoshi.

Ƙasa sosai ya yi da murya, tamkar mai raɗa ya ce. "Please Aesh, ko kaɗan ne? Ba dan ni ba, dan Allah"...... Yunƙurawa ta yi zata yi mashi magana ya yi gaggawar sake cewa. "No Aesh, don't say anything please, kawai ki sha". Haɗiyi abin da ta yi niyar faɗa ta yi, sannan ta kai hannu ta rike stro dake ciki haɗaɗɗen cup ɗin, ɗan jujjuyasa ta yi kaɗan kafin ta ɗan duka ta sanya bakinta. A hankali ta ɗan zuƙa. Slowly ya ɗan lumshe idanunsa, dan har cikin ransa ya ji wannan zuƙa da ta yi, nisawa ya yi kafin ya ɗan kawar da kallonsa daga kanta yana mayarwa kan wayarsa dake vibrate. Call ɗin Bilal ne ya shigo, kamar zai yi picking sai kuma ya fasa tare da kashe wayar ma mai gabaɗaya, ya tura cikin aljihunsa sannan ya harɗe hannayensa a saman faffaɗar kirjinsa, gabaɗaya ya zuba mata waɗan nan dara daran idanun nasa yana kare mata kallo.

A hankali take cigaba da shan abin tana É—an tsuke fuska alamar ya yi mata sanyi sosai. Kamar ance ta É—ago ido tana É—agowa suka yi four eyes, É—an zaro idanu ta yi like wow and like kallan me kake mun?! Shi kuwa gera guda ya É—an É—aga mata kafin ya sauke ajiyar zuciya, abin gwanin birgewa sosai....... Wani irin kallo ta wurga mashi mai kama da harara, shi kuwa ya yi mata nuni da idanunsa izuwa kan cup É—in alamar ta cigaba da shan abin da take sha bai san iskanci.
Make kafaɗa ta yi tare da girgiza kai, sannan ta ɗan ture cup ɗin gaba alamar ba zata cigaba da sha ba kenan. Ɗan jinjina kansa ya yi like irin yarinya baki sanni ba ne. A fili kuma sake nuna mata cup ɗin da ido ya yi alamar ta cigaba da sha...... Wannan kallo dai mai kama da harara shi ta sake binsa da shi kafin ta nuna mashi cikinta da hannu alamar ta ƙoshi ba tare da ta yi magana ba, alamar dai yau ƴar kurma kurma suke jin yi. Ɗan kawar da kallonsa daga kanta ya yi kafin ya ɗan yi gyaran murya kaɗan, sannan ya ce. "Aesh you're giving me to much of headache".

Tamkar bata ji sa ba ta cigaba da binsa da wani irin kallo, har cikin zuciyarta take rasa natsuwarta a dik lokacin da take kallonsa, sai dai kuma bata wani É—aukar hakan a matsayin wani abin azo a gani, ta fi É—aukar abin ma a matsayin tsoronsa saboda abin da ya shiga tsakaninsu.

Suna a haka masu kawo oder suka sake sauƙe masu tsadaddun plate masu shake da kayan fruits kala kala very fresh a ciki. A gabanta yanzu ma suka sauke, kallansa ta yi cike da mamaki kafin ta ce. "Wannan fa?".... "Is yours". Ya bata amsa yana kallan yadda kankanar ta yi balai'n kyau, sun yankata shape of heart kanana da manya, gata jajir zata yi zaƙi.

"Ni gaskiya na ƙoshi mu tafi gida". Ta faɗa kallanta a kansa..... "Babu in da zamu je matsawar baki sha fruits ɗin nan ba". With full confidence ya bada amsar, irin da gaske yake yi ɗin nan. Bata da zaɓin da ya wuce dole dole ta sha, tamkar zata saka mashi kuka ta kai hannu saman plate ɗin, sai kuma ta ƙasa ɗaukar komai, saboda yadda aka yayyanka fruits ɗin shape of heart ya yi matuƙar birgeta, tamkar ance masu masoya ne suka yi oder, basu san waɗan nan abokan faɗa bane.
Chapter 179 · 0% Book details