← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 242

Sashe 91

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sun ci karfin dafiyar da suke yi, abu kaɗan ya yi masu saura su fita daga cikin wannan dajin, sai dai yamma ta yi masu sosai, Hoorain ya fahimci dole sake kwana a forest ɗin nan ya kamasu, dan haka tin kafin rana ya faɗi dare ya yi masu sai ya yi saurin samun waje mai tsaro, mai ƙawa da ɗaukar hankali ya tsaya. Daga in da ya dakata zuwa in da mammar Kamran take basu da nisa, kun tuna wajen zaman su Sweetie na farko kafin Sadauki ya canza masu? To a arear wajen ya dakata ya fara ƙoƙarin haɗa masu wajen da zasu kwana gobe da asuba su cigaba da tafiya.

Suna dakatawa Auta ta hau takura mashi da shagwaɓar yunwa take ji, hakuri ya bata har sai da ya gyara masu in da zasu kwanta ba tare da wata matsala ba, saboda kada duhu ya riskesa bai kammala ba. Waje mai kyau da haɗuwa ya gyara mata ita da Pretty kafin ya fara tinanin im da zai samo masu abin da zasu ci.

Cike da mama Auta ta ce. "Kai kuma ina wajen kwananka my hero?".

Idanunsa a kan kyawawan hannayenta ya amsa mata da. "Ko lokacin da muke gida ma ai bana da wajen kwana, kullun ina kasancewa ne a kusa da family part dan gadin abin da zuciyata ke muradi".

Dik da tasan ita yake nufi, amma saboda ta ji ya furta ita É—in da bakinsa yasa ta ce. "Wacece kuma ko mecece kuma abin da zuciyarka take muradi?".

Sarai ya fahimci Zunaira a kullum tana san ganin yana nuna irin zallar son da yake yi mata, hakan yasa take san jefa mashi ire iren waÉ—an nan tambayoyi. Allah sarki tana san taga yana nuna yana santa tare da yi mata kalamai masu zafi.

"Wata ce wadda zuciyata ke kauna". Ya bata amsa cike da tsoron abin da amsar zai haifar, dan yasan halin kayassa.

"Ban gane wata ba! Wakenan?". Ta yi maganar tana É—an É—aure fuska.

"Wata kyakkyawa mai kyan fuska dake É—auke da lallausan murmushi mai kwantar da hankalin assistant commander, murmushinta yana sakani manta in da nike, murmushinta yana sawa in ji kamar an bani kyautar gida a aljanna, tauraruwar zuciyata wanda haskenta ya haske kirjina dikka, shekin haskenta ya wuci tinaninki, tin daga nesa idan ta doso haskenta yake disashe hasken dikkan wasu halittu dake gefenta, tauraruwar da bana jin za'a samu irinta".

Tin da ya fara waɗan nan zafafan kalaman ta tsaresa da idanu tana kallan kyawawan lips ɗinsa yadda yake ɗan motsasu, yana magana one by one, bata san tana sakin cool murmushi ba ma, ta nitsu tana jin ta a wani duniya da babu hayaniya babu wata yana da zata yi mata tsakani da farinciki. Haƙiƙa akwai tsananin daɗi masoyi ya aika saƙon kalamai ga zuciyar da yasan tana matsanancin kausarsa, tabbas zai ɗarsa bishiyar yarda da kauna mai zafi da bata da iyaka a wannan zuciya.

Ganin tana zuba sanyayyar murmushi ba tare da tasan tana yi bane yasa bai san lokacin da ya kashe mata ido É—aya ba. Sai ganinta ya yi ta É—an zaro idanu tana É—age mashi gera ta kuma faÉ—aÉ—a murmushinta.

"Murmushinki abin so ne har ga makiyanki gimbiyata, dik wanda baya san murmushi tabbas bai ga naki bane sarauniya............".

Katse shi ta yi da cewa. "A fadar birnin zuciyar my Hero" . Wato sarauniya a fadar birnin zuciyarsa kenan, ta ƙarisar mashi da maganar.

Ajiyar zuciya ya sauke yana jin wani irin sanyi tana ratsa zuciyarsa.

"My Hero kasan me?". Cike da farinciki ta yi maganar. Kai ya girgiza mata alamar a'a ba tare da ya yi magana ba. "Kalli cikin idanuna bari mu yi magana". Ta faÉ—a tana kallansa.

Girgiza mata kai ya yi kafin ya ce. "A'a ba zan iya kallan cikin idanunki ba". In a silent talk mai kama da raÉ—a ta furta. "Why?".

Ƙasa sosai shi ma ya yi da murya kafin ya amsa da. "Saboda sirrikan da kyawawan idanunki suke ɗauke da su zasu sa zuciyata ta kasa iya shanyewa, ba zan iya ɗauka ba"................. Pretty dai kallansu kawai take yi, yo ita da bata ma gane me suke faɗe, ai gani take yi wani sabon haukan ne suke yi.

"Kai da kake matsayin jarumi, namijin gaske, sadaukin da dauloli suke tsoron jin an ambaci sunansa a cikin mayakan da zasu kai masu hari, sadaukin da ya ciri tuta ya kafa tarihin da ba'a taɓa kafa irinta ba a kaf faɗin kingdom of power, sadaukin da sunansa ke firgita manyan maza yasa hantar cikinsu ta kaɗa, kai fa assistant commander ne na gabaɗaya dangerous warriors, shi ne zaka ce kana jin tsoron kallan cikin kwayar idanu na? Meyasa?". Cike da kwarin gwiwa ta yi maganar.

Nisawa ya yi kafin ya ce. "Ranki ya daɗe dik ajiye wannan a gefe, mata suna da kwarjinin da dik wani girman namiji da ji da kansa yana jin shakkarsu, ga su dai sune ƙasa da mu, amma Allah ya basu wannan dama a kanmu, wlh wannan gaskiya nike faɗa maki, dik namiji yana jin shakkar mace, sai dai ya danne kawai, dik bama wannan ba".............. Ƙasa sosai ya yi da murya kamar sillent talk, sannan ya cigaba da cewa.

"Ke idanunki daban suke da kowace mace, tsoron ganin cikinsu nike ji kada ki hanani yin barci yau". Cikin nitsuwa ya yi maganar................Siririn murmushi ta sakar mashi. "Zan iya samun sunan love apart from ranki ya daÉ—e?".

Unexpect garin amsa mata idanunsa suka sauka a cikin nata. Wani irin azabbabben shock ya ji tin daga tsakiyar kansa har izuwa tafin ƙafarsa dake cikin takalmarsu na mayaƙa. Cikin sauri ya zare idanunsa unexpext ya sake sauke kallansa a saman kyawawan laɓɓanta da ta ɗan ciza na kasan kaɗan hakan yasa ya kara pink sosai.

Oh god, zuciyar maza ne ta amsa, nan take ya ji shi a matse kamar yana ƙoƙarin shiga out of control, wani irin jan numfashi ya yi mai cike da fassarori dayawa. Ƙasa iya amsa mata ya yi, sai ya ji gabaɗaya kamar an ɗaɗɗaure mashi tongue ɗinsa.

"My Hero lafiya?". Ta yi mashi tambayar bisa famintar da ta yi na ya shiga wani hali. Nisawa ya yi kafin da kyar ya iya buɗan baki yana ɗan girgiza kai ya ce. "Babu komai Hoonaira". ......... Hoonaira ta maimaita sunan tana kallansa, har cikin ranta ta ji wannan lallausan suna mai daɗin ambato, sai ma da ya faɗa da bakinsa ne ta ji wani irin daɗi na daban. HOORAIN AND ZUNAIRA SHI NE YA BADA HOONAIRA LIKE WOW, ABIN YA ƘAYATAR.

"Zan iya tafiya in je in samawa gimbiyata abin da zata ci?". Ya jefa mata tambayar yana kallan gefenta a zahiri, amma a bayan fage face É—inta yake kallah.

"Ni dai a'a ban yarda ba, ni sai ka kalli cikin idanuna sannan zaka tafi, idan ba haka ba ni bazan ci abinci ba". Kamar zata yi kuka ta yi maganar.

Ɗan jinjina kai kawai ya yi, shagwaɓaɓɓiyar nan tasa tana san ɓallo mashi ruwa ne yana zaman lafiyansa. "So kike yau ki hanani barci ko?"........... Kai ta ɗan girgiza mashi. "Zaka yi barci In Sha Allah in dai muna tare".

"To amin afuwa na je na kawo wa sarauniyata abincin dai tukun nan, idan na dawo sai ki tsareni ki sakani yin dik abin da kike so"........ Jin in ya dawo ta saka shi yin dik abin da yake so yasa ta aminta da ya je to. Cikin zafa ya wuce yana taku cike da jarumta.

Bayansa ta bi da kallo har ya kurewa ganinta, sannan ta riko hannun Pretty suka zauna a wajen da ya tanada masu, cike da tsananin kaunarsa ta fara bawa Pretty labarin irin tsantsar madarar san da take yi mashi.

Shi kuwa neman masu abin da zasu ci ya tafiyi dokinsa na biye da shi a baya. Dai'dai zai gifta tsakanin wasu dogayen bishiyoyi ya hango kamar mutun kuma mace tana ƙoƙarin jan abu a kwando. Da yake yana da zuciya mai kyau sai ya nufeta domin ya taimaka mata.

Ba kowa bace face mammar Kamran, ta ɗebo kayan lambunta dayawa a cikin irin wannan kwando da Kamran yake ɗebo mata ɗin, kwandon yana da girma sosai hakan yasa take jansa da kyar, dan ya yi mata nauyi. Allah sarki Kamran mai yi mata hidimar baya nan, daga ganinta bata da ƙoshin lafiya, da alama tsananin damuwan rashin Kamran ya haifar mata da ciwo, ta yi rama sosai tamkar ba ita ba, shiyasa ma ta kasa iya ɗaukar wannan kwando, jikinta har wani kerma yake yi.

Taimaka mata ya yi ya É—auka mata suka haura saman tsauninsu, kun san Mamma bata yarda da baki, dan haka shi ma bata aminta da shi ba, sai dai shi ko da ya nufota bai yi mata magana ba, kwandon kawai ya É—auka mata da hannu É—aya ya haurar mata sama, a bakin kofar kogonsu ya ajiye mata ya juya ya sauka, bai yi mata magana ba ya wuce abinsa.

Dik yadda bata san mutane yau karo na farko da aka taimaka mata ta ɗan ji a ranta ashe ba dikka mutane bane na banza, ashe akwai na kirki? Ashe akwai masu taimako? Bata taɓa zatan akwai wanda zai iya taimaka mata ba a rayuwarta, Allah mai iko, yau ta ga sabon abu.

Shi kuwa yana sauka ya bazama nemanwa gimbiyarsa abinci, bai dawo ba sai da duhu ta fara yi, sannan ne ya dawo É—auke da kala kalan kayan cima da za'a iya samu a wannan dajin. A lokacin Pretty da Auta sun yi alwala sun yi sallah suna zaune a waje guda suna hira.

Suna ganinsa suka miƙe, a gabansu ya dire masu kayan da ya kawo masu, Auta ce ta kallesa cikin ido. "My Hero muna godiya da kulawan da kake bamu, Allah ya barmun kai ya kare mun kai da kariyarsa".

Ƙasa ƙasa ya amsa da amin tare da miƙewa yana faɗin. "Zauna kici ko? Kinga tun ɗazun kika ce kina jin yunwa". "To kai ina zaka je ba zaka zauna mu ci ba?". A shagwaɓe ta yi maganar. "Ba zan jima ba, yanzu zan zo". Ya faɗa cike da san ya tafi.
Chapter 91 · 0% Book details