← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 242

Sashe 16

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ya gyaɗa kansa sama alamar e, dama abin da yake ƙoƙarin ya gayawa uncle ɗin nasa kenan, amma tongue ɗinsa taki motsawa.

Miƙewa tsaye uncle Jahiz ya yi ya nufi cikin toilet, babynsa dai yaki ya kwanta, rike da shi ya shiga cikin toilet ɗin.

Ga shi dai katafaren hotel mafi tsada suka kama, amma sai gabaɗaya uncle Jahiz ya raina hotel ɗin, toilet nasu ko na bedroom ɗin Sarina bai kai ba, sam basu ji daɗin sauƙa a wajen ba, amma da yake a kan hanya suke sai ba su wani tashi hankulansu ba.

Shiga ya yi ya haɗa mashi ruwan wanka mai ɗan ɗumi, sannan ya fito, a lokacin babyn nasa ya yi barci, cikin dabara ya kwantar da shi a saman bed ɗin, tamkar ya iya reno, sannan ya matso domin taimakawa Jaish ya miƙe tsaye.

Ga dikkan alamu Jaish ya dawo dai'dai sosai, dan tambayoyi uku ne yanzu a cikin ransa, ina Momma da dad? Ina Jawad? Ina Auta? WaÉ—an nan su ne kawai damuwarsa, ya yi kewarsu.

Taimaka mashi uncle Jahiz ya yi, da kyar ya iya tashi zaune, har yanzu yana ganin jiri jiri, sanna kansa yana É—an sara mashi kaÉ—an kaÉ—an.

Hakika ya sha madarar mamaki na ganin irin yanayin kayan da yake a jikinsa, ko a mafarki bai taɓa ganin irin kayan ba, domin kaya ne na gargajiya wato shadda jampa da wando, shi dai yasan ba irin kayansu bane wannan, bai ma taɓa ganin irin kayan a zahiri ba sai dai idan a waya ya ci karo da videos na Hausawa, amma yau shi ne sanye da irin wannan kaya, to a ina ya samo su? Ya jefawa kansa tambayar da bashi da amsa, kuma bai iya magana bare ya tambayi uncle Jahiz.

Taimaka mashi uncle É—in nasa ya yi izuwa cikin toilet, ya fito ya bashi waje, ya dawo cikin É—akin domin haÉ—a masu kayansu jirginsu ya kusa É—agawa, dik abin da yake yi idanunsa na'a kan babyn nan na Khadija, da alamu ya kamu da kaunar yaron sosai sosai, kun san fa kyawawan koreans akwai madarar kyau ba kaÉ—an ba, dole su shi ga ran mutum ko baya so.

After some minutes. Like wow Jaish ya fito da kafafunsa É—aure da towel a kunkuminsa, ya samu kwarin jiki na wanka da ya yi, a take har ya fara komawa yaron mommarsa, dama ya É—an yi duhu zamansa a Yola.

Kayansa uncle Jahiz ya fitar three-piece suit ya miƙa mashi, sannan ya janyo zip ɗin echolac ɗin nasu ya rufeta.

Ba musu Jaish ya karɓi kayan domin ya shirya, uncle Jahiz ya fito waje dan ya sanar da securitys ɗinsu su juya kan motocin zasu wuce airport dan su koma ƙasar Tunisia yanzu.

Kafin ya dawo cikin ɗakin Jaish ya kammala shiryawa, like wow ya yi masifar kyau sosai, sai dai gashin kansa a jiƙe yake, bai busar da ita ba, ya zubawa babyn Khadija idanu yana mamakin a ina uncle ɗinsu ya samo wannan kyakkyawan yaro haka?.

"Jaish yaron ya yi maka kyau ko?". Uncle Jahiz da ya shigo a yanzu ne ya jefa mashi wanna tambaya.

To kun dai san halin yaron Mommarsa, ba sai na sake faÉ—a ba, dan haka yana jin uncle Jahiz amma bai amsa ba, ya yi banza da shi, sai ma ya wuce ya zauna a bakin bed tare da yin kasa da kai kamar mai nazarin wani abin, da alama kunyarsa da ya rasa a garin Jimeta yau ta dawo, halinsa dai sak ya dawo, an koma gidan jiya malam.

Da yake uncle Jahiz ya san halinsa sai bai wani damu dan bai amsa shi ba, ya ce. "Zamu iya tafiya a yanzu ko akwai wani abin da kake son yi?".

Miƙewa tsaye ya yi ba tare da ya iya gamana ba, alamar zasu iya tafiya kenan, maganar ce kawai ba zai yi ba, yana son tambayar uncle ɗin nasa a ina suke kuma me ya kawosu nan? Amma ina baya son yin magana yasa ya yi biris da zancen, da alama ma ya karo walaƙanci kaman ba shi ne ya gama shanyewa Mahnoor baki jiya ba, dik ya mance wanna!. Tashin sense, me kuke tunanin zai faru?.

ÆŠaukan baby uncle Jahiz ya yi ya nufi waje, yana fita yasa securitys da su shigo su kwasan masu echolacs É—insu, zasu fara zuwa asibiti su mayar da babyn Khadija sannan su jandadawa Dr da ya kula da su kafin su tafi.

Haka kuwa aka yi, karfe É—aya na rana dai'dai jirginsu ya É—aga sai kasar Tunisia cikin amincin........ Safe journey our Jaish and uncle Jahiz.

=====KINGDOM OF POWER======

Zaune take a saman sofa a part ɗin Mammienta, daga ita sai wani figaggiyr simi, wani riga ne mai siririn hannu wanda ya tsaya mata a iya gwiwowinta, fararen kafafunta suna cikin wani katan bowl mai ɗauke da ruwa launin orange color, skin ɗin Sarina kullum cikin samun gyara yake, ta iya kula da shi matuƙa.

Wata kuyanga ce durkushe a saman gwiwowinta a gaban Sarina tana aikin wanke mata kafafunta dake cikin ruwan.

Mammie na zaune a saman sofa kusa da ita, Sarina tana riƙe da wasu hotuna tana kallo tana sakin ƙayatattcen murmushi, da alama yau suna cikin matsanancin farinciki daga ita har Mammie ɗin tata, sai hira suke zubawa suna fara'a.

Ita kuwa wannan kuyanga kanta a kasa tana aikinta cikin girmamawa, ga dikkan alamu tana bala'in tsoron Sarina.

Fanan ce ta shigo cikin É—akin bakinta a É—auke da sallama. Babu wanda ya amsa sallamar a cikinsu face kuyangar nan, ita ma a cikin zuciya ta amsa, saboda tana tsoron Sarina ta hukuntata, zasu ce ai ba ita aka yi wa sallamar ba.

Wata kuyanga ce ta sake shigowa baki É—auke da ladabebben sallama.

Kusan a tare suka kariso ciki ita da Fanan, ita tana zuwa ta fara aikin shafawa Sarina kayan gyaran jiki a dik wasu sassa na jikinta, ita kuma Fanan saman sofa ta zauna tana haÉ—e rai kamar hadari.

"Lafiya kike wani kwaɓe fuska haka?". Cewar Sarina, ta yi maganar tana wani bin Fanan da kallo mai kama da harara.

"Ke Aunty Sarina baki san me yake faruwa ba ko?".

Ɗan taɓe baki ta yi kafin ta ce. "Me kuma yake faruwa?".

Mammie ma kasa kunne ta yi dan ta ji me yake faruwa.

Kara haÉ—e rai Fanan ta yi haÉ—e da alamar tausayawa a saman face É—inta ta fara magana.
"Baki san Yah Jawad yana can kamar zai mutu saboda an aurawa Yah Rizwan Chuchu ba ko?".

Siririn tsaki ta ja. "To ni me ya dameni da su?".

"Kai Aunty Sarina kin san fa Yah Jawad ne yake son Chuchu ba Yah Rizwan ba, ke baki ji tausayinsu bane?".

Yamutse fuska ta yi tare da haÉ—e rai. "Su mutu ma dikkansu idan suka ga dama, ni kinga in abin da ya kawo ki nan kenan tashi ki bamu waje".

ÆŠan zaro idanu Fanan ta yi like surprise haka. "Aunty Sarina su Yah Jawad ne fa!".

"To sai aka yi yaya idan su ne? Nace su mutu idan suka ga dama! Ni ki rabu dani da abin da nima yake rai'na".

Da sauri ta dawo da kallonta a kan Mammie. "Mammie kin ji abin da Aunty Sarina take faÉ—e ko? Su Yah Jawad take cewa su mutu fa".

Ta yi maganar cike da yakini da sa ran Mammie zata yi wa Sarina faɗa kuma ita ma ta ji babu daɗi a kan maganar, ina ai sai ta ga saɓanin tunaninta, dan kuwa ɗaure fuska sosai mammie ta yi kafin ta ce.

"To sai me dan ta ce hakan?".

Zaro idanun sosai Fanan ta yi, she was so surprised jin amsar Mammie tasu.

"Mammie ban gane ba!". Tana kara zaro idanu ta yi maganar.

"Ba zaki gane ba ai, mu kingan mun nan ba su Jawad bane a gabanmu, kowa ma a cikin Kingdom É—in nan in ya ga dama ya mutu!!". Cewar Sarina uwar rashin kunya.

Kasa yin magana Fanan ta yi, ta zuba masu ido tana mamakin jin furucinsu.

"Ke wai baki ma san dik abin da yake faruwa da su Mammie É—in ce ta haÉ—a ba ko?". Cewar Sarina.

A miliyan Fanan ta kara zaro ido waje tamkar kwayar idanunta zasu faɗi ƙasa haɗe da furta kalmar what!! Ba tare da ta san kalmar ta fita daga bakinta ba.

"Kwarai kuwa, mammie ce ta haÉ—a dik wanna cakwakiya, dan haka ki wuce ki bamu waje uwar Æ´an tausayi!". Cewar Sarina again.

Yadda kuka san ruwa ya cinye Fanan, tamkar babu ita a wajen ta yi shiru, al'ajabi ya kusa kasheta.

"Tashi ki fita ki bamu waje tattaunawa muke yi uwar masu tausayi". Cewar Mammie.

Tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki ta mike, sumumui sumumui ta nufi kofar fita.

"Sakarya kawai wadda bata san ina yake yi mata ciwo a jikinta ba, shashasha wai ke uwar tausayi! Zaki mutu babu wanda ya ji sautin kukanki in dai kika ce tausayi zaki yi a rayuwarki!!" Cewar Sarina dake binta da wani matsiyacin kallo.

Sarai ta ji abin da Sarina É—in ta faÉ—a, amma bata juyo ta tanka mata ba ta nufi waje kawai tana yi masu addu'ar shiriya.

"Ya isa haka my daughter". Cewar mammie ga Sarina.

"Allah Mammie Fanan wawiya ce wacce bata san ciwon kanta ba, ni bakanta mun rai take yi wlh".
Tana magana tana hararar kuyangar dake gabanta tana wanke mata kafa, kamar kuyangar ce ta yi mata laifi.

Kunsan Fanan a part É—in Momma take yawan zama dan ta sami soyayyar Jaish, da farko ita ma zuciyarta ya fi karkata a irin halin mammiensu, amma zamanta da momma ya canzata izuwa mutumiyar kirki, kunga kuwa ko bata auri Jaish ba ai ta sami babban abu da zai iya zame mata makamin tsira duniya da lahira, wato halayyar kirki haÉ—e da ilimin addini kenan, ai kunga ta tsira ta kuma ci ribar zamanta da Momma ko?!.

Tana barin part É—in nasu ta wuce King part, kai tsaye É—akin gyaran jikin su Aneesa da su Mama Haulat suke girka su a can ta nufa, jikinta dik a sake baiwar Allah.
Chapter 16 · 0% Book details