← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 242

Sashe 22

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mirrornsa da ya fashe Black Tiger ya mayar da shi yadda yake, chandelier ta koma mazauninta tamkar bata taɓa motsawa ba, amma a haka Ronnie ya fahimci akwai abin da ya faru a ɗakin!.

Cigaba da bayani Sweetie ta yi kamar haka. "Al-Qur'ani littafi ne wanda Allah ya saukar wa Annabi Muhammad (SAW) ta wurin Mala'ika Jibril. Shi ne kalmar Allah tsarkakakke ba tare da canji ba tun lokacin da aka saukar da shi, kuma ya kasance jagora ga dukan al'umma".

"Injila. Asalin Injila da Annabi Isa ya kawo an saukar da ita ne da harshen Aramaic, wanda shine yaren Annabi Isa. Amma Bible na yau an rubuta shi ne da Greek da Latin kafin a fassara shi zuwa wasu harsuna. Wannan ya haifar da bambance-bambance masu yawa da kara tsaurara banbanjin tsakanin injila da Bible".

"Al-Qur'ani an saukar da shi da harshen Larabci na asali, kuma har yanzu yana nan daidai kamar yadda aka saukar. Wannan yana tabbatar da tsaronsa ba tare da canji ba!".

"Injila ta kunshi wa'azi na Annabi Isa, da alheri, da darussan soyayya, da imani, da sanin girman Allah da ranar kiyama. Amma rubuce-rubucen Bible na yanzu sun haÉ—a tarihin Annabi Musa, annabawan da suka gabata, da wasikun manzanni da su irin su Bulus, wanda ba sahabi ba ne na Annabi Isa (A.S.) Wannan ya sanya kiristoci suna samun akida mai É—an rikitarwa".

"Al-Qur'ani ba wai wa'azi kawai ba ne, cikakken tsarin rayuwa ne wanda ke jagorantar Musulmi wajen ibada, mu'amala, siyasa, dokokin shari'a, da zamantakewa, hukunci kan lahira, mutuwa haɗe da kwamciyar kabari, hisabi da dai sauransu. Ya kunshi hukunci masu ma’ana da shawarwari kan dukkan bangarori na rayuwa, Alqur'ani mai girma ya haɗe komai da komai".

"Injila ta asali (Injil) an yi mata canje-canje da yawa bayan Annabi Isa. Bible na yanzu an rubuta shi shekaru da dama bayan barin Annabi Isa duniya, kuma kiristoci suna da nau'o'i daban-daban na Bible, misali, Catholic Bible da Protestant Bible, wanda ya nuna rashin tabbaci kan ainihin littafin, Alqur'ani mai girma shi kaÉ—ai ne babu wani kala daban daban, kai ko suna ba'a sake mashi ba, yana nan a Alqur'aninsa kamar yadda ya sauka!".

"Al-Qur'ani ya kasance tsarkakakke tun lokacin da aka saukar da shi har yanzu, ba tare da wani canji ba. An adana shi a kwakwalwa da rubuce-rubuce daga lokacin Annabi Muhammad (SAW). Wannan ya tabbatar da tsaronsa daga duk wani ruÉ—ani".

"Annabi Isa ya kira mutane zuwa tauhidi, wato bauta wa Allah shi kaɗai a cikin injila ta ainahi Mark 12 verses 29. Amma a cikin Bible na yanzu akwai akidun Triniti (Trinity) da suka bayyana Yesu a matsayin Ɗan Allah ko wani ɓangare na Ubangiji. Wannan yana da saɓani da asalin saƙon Annabi Isa a Musulunci!!".

"Al-Qur'ani yana nan daidai da saƙon tauhidi na Annabawan da suka gabata, yana tabbatar da cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. Suratul Al-Ikhlas 112. Ya kuma kawo bayani kan matsayin Annabi Isa da sauran annabawa".

"Injila sakon tauhidi ne ga bani Isra'ila daga Annabi Isa, amma Bible na yanzu ya haɗa da bayanan da suka sha bamban da asalin saƙon Allah".

"WANNAN SHI NE BANBANCIN ALQUR'ANI DA INJILA DA KUMA BIBLE INA FATAN KUN GAMSU SOSAI?".

Ta yi tambayar tana rarraba idanunta a kansu. Babu wanda ya iya furta uppan a cikinsu.

Sai dai a lokacin da ta zo wannan gaɓar Ronnie ya ji zuciyarsa ta ɗan yi sanyi, saboda shi kansa yasan suna da Bible kala daban daban wanda rubuce rubucen cikinsu ma yake kala daban daban! Kamar yadda ta ce akwai Catholic Bible da Protestant Bible, yasan da hakan, so sai ya ji kamar ta ɗan faɗi gaskiya a wannan gaɓar.

Ganin kamar zuciyar Ronnie ta É—an sanyaya ne yasa ta kara jin kwarin gwiwar zata iya cin nasara a kansu, dan haka sai ta cigaba da bayaninta.

Tana ƙoƙarin cigaba da yin magana Ronnie ya katseta da cewa. "Shekara nawa ne tsakanin rasuwar annabi isa da kuma bayyanar Bibles na yanzu da kiristoci suka kaddamar a matsayin injila?".

Zaro idanun Floris ta yi haÉ—e da mamakin Ronnie, ta ji kamar ya gamsu da zancen Sweetie ne.

Sosai Sweetie ta ji daÉ—in wanna tambaya da Ronnie ya yi mata, dan tana ganin kamar ta fara cin nasara ne, dan haka cikin farinciki da zumuÉ—i ta amsa mashi da.

"Tarihin rubutun Bible, musamman Sabon Alkawali (New Testament), yana nuna cewa akwai babban tazara tsakanin lokacin da Annabi Isa (A.S.) ya bar duniya da lokacin da aka rubuta kuma aka tattara wannan littafi. Bari dai na yi maku dallah dallah dan ku fahimta".

Kara nutsuwa Ronnie ya yi dan ya saurareta da kyau, da alama zuciyarsa ta fara yarda da maganganunta, dan komai ta faÉ—a tana kawo hujja mai karfi wanda dole ka yarda, kamar a baya yadda ta faÉ—i ayayon Alqur'ani da za'a je a duba dan tabbatar da gaskiyarta, hakan yasa ya fara gasgatata.

"A tarihin Kiristanci, ana tsammanin Annabi Isa ya bar duniya, daga hangen nasu an ce an kashe shi, amma a Musulunci ba a kashe shi ba, Allah ya É—aukaka shi zuwa sama kamar yadda na faÉ—a a baya. Wannan lamarin ya faru kimanin shekarar 30-33 AD".

AD wato Anno Domini yana nufin bayan haihuwar Annabi Isa ne, BC wato before Charist yana nufin kafin zuwan Annabi isa duniya kenan, to shekarun ake kira da BC, bayan zuwansa kuma AD.

Cigaba da bayani Sweetie ta yi cikin sani da kuma kwarin gwiwa. "Bayyanar Sabon Alkawali (New Testament). Rubuce-rubucen farko na Sabon Alkawali, waÉ—anda aka ce wasikun Bulus ne (Paul), sun fara bayyana kusan shekaru 20-30 bayan É—auke Annabi Isa daga duniya da Allah ya yi, kimanin shekarar 50 AD bayan zuwansa duniya kenan".

"Injiloli guda huÉ—u ko in ce Bible É—inkuna yanzu guda huÉ—u wato Matthew, Mark, Luke, John. An rubuta su kusan daga 60 AD zuwa 110 AD. Injila na Markus wato Bible mark ana É—aukar shi mafi tsufa, an rubuta shi kusan shekarar 60-70 AD. Sauran injiloli (Bibles) suna tafe daga bayansa".

Izuwa yanzu jikin Ronnie ya yi sanyi, saboda jin yadda take zayyano tsawon shekaru baya, ko mai san zuciyar mutum ya ji wanna bayanai nata dallah dallah sai ya san gaskiya take faÉ—i, sai dai idan yaki aminta da hakan dan san zuciyarsa ne! Amma irin wanna shekaru da take ambata ai babu karya!.

"A lokacin shekaru 325 AD bayan haifar Annabi Isa kenan, a taron Council of Nicaea, a karkashin Sarki Constantine, aka fara tsara da tantance irin waɗanda za su shiga cikin Bible na yanzu, kuma wannan ya ƙarfafa canje-canje na ra'ayi da tsarin Kiristanci, kun dai ji Bible naku na yanzu sarakunar da ne suka shirya abubuwan da za'a rubuta a ciki, so ni nasan ba laifinku bane zamanku kiristoci, laifinku a nan shi ne rashin faɗaɗa bincike da neman sanin gaskiya bayan Allah ya baku dama da baku yi na shi ne laifi, kun dogara da littafi guda ɗaya wanda tsara maku shi aka yi ba zancen Allah bane!".

"Injila ta gaskiya da Annabi Isa ya kawo ta ɓace na tsawon lokaci, hakan yasa saƙon Allah bai isa ga mutanen yadda yakamata ba. Wannan ne yasa Allah ya saukar da Al-Qur'ani Mai Girma don ya zama tabbataccen jagora wanda ba zai taɓa sauyawa ba, wasu gungun kafurai sun jima suna shuka tsiya da rashin son gaskiya a duniya, amma Allah ba'a yi mashi wayo, da suka ɓatar da injila ta gaskiya sai ya sauko da Alqur'ani wanda wane mutun ya iya canza rubutun cikinsa, karya mutum yake, tsawon shekaru har yau yana nan yadda aka sauke shi!!".

Ta kai karahen maganar idanunta a kan Ronnie tana kuma sauke nannauyar ajiyar zuciya, sai fatan take yi Allah yasa su gane gaskiya.

Floris ta rasa abin faÉ—e, sai idanu kawai take binsu da shi, ta ji abin da ya girmewa shekarunta.

"Shin kana da wata tambaya dan kara tabbatar da gaskiya ta da gaskiyar addinanina ne ko dai ya isa haka?".

Ta jefawa Ronnie tambaya idanunta a kansa.

Zuciyarsa ta gama yarda da zancenta dikka, amma dik da haka dan kara tabbatarwa sai ya ce.
"Shekara nawa Annabi isa ya yi a duniya.............. and tare da mahaifiyarsa ya yi rayuwa? Sannan akwai wani dalilin da yasa bai yi aure bane?. And ya rayuwarsa ta kasance a cikin al'umma a lokacin da ya bayyana bai da uba? Ya fisakanci kyara ko tsangwama ne daga mutane? Ko dai a addininki Annabi isa yana da baba ne ɓoye mana aka yi kamar yadda aka canza mana komai?".

Ta ji matuƙar daɗin jin wanna tambaya tasa, ranta ya yi sanyi sosai.

With full confidence ta ce. "Tarihin Musulunci da Kiristanci ya nuna cewa Annabi Isa (A.S.) ya rayu a duniya na kimanin shekaru 33 zuwa 34 kafin Allah ya É—aukaka shi zuwa sama. Wannan yana nufin bai mutu ba a hannun mutane, kamar yadda Musulunci ya bayyana Surat An-Nisa shafi na 4 aya na 157-158 Allah ya yi wanna bayani".

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta É—aura da cewa.
"Annabi Isa ya taso ne a ƙarƙashin kulawar mahaifiyarsa, Nana Maryam, wacce Allah ya zaɓa kuma ya tsarkake ta daga zunubi. Ya zauna tare da ita yayin ƙuruciyarsa har lokacin da ya fara wa'azinsa. Mahaifiyarsa ta kasance ginshiƙi da gatansa, musamman ganin cewa ba shi da uba".

Ronnie fa ya ji abin da bai taɓa ji ba, ga shi maganganunta dai ba zasu karyatu ba, shi kansa yasan gaskiyar take faɗe, saboda idan ba gaskiya bane taya tana karamarta haka ace zata tsara irin wanna dogon karya? Ai ba zata taɓa yiwuwa ba.

Cigaba da bayani ta yi. "Dalilin da yasa bai yi aure ba, Allah ya aiko Annabi Isa (A.S.) da takamaiman manufa, isar da saƙon tauhidi ga Bani Isra'ila da warkar da zukatansu daga zalunci da ruɗi. Rashin yin aurensa ba tare da shakka ba ya haɗu da wannan manufar, don ya mai da hankali kan aikin annabci ba tare da wata tangarda ba!".

"Al'ummar da Annabi Isa ya fito daga cikinta tana cike da tsangwama da adawa ga saƙon Allah, kuma rayuwarsa ta kasance cike da ƙalubale. A irin wannan yanayi, yin aure ba zai yiwu ba, domin tsangwamar mutane za ta iya shafar iyalinsa idan ya kasance da su".
Chapter 22 · 0% Book details