← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 242

Sashe 82

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya sha wahala sosai kafin ya samu ya ture damisan daga kansa, sannan ya miƙe cike da jarumta, da gudun gaske damusan ya yi kansa dan ma kada ya bashi wata damar kara karfafa kansa kenan. Juyawa ya yi da gudu damisan ya rufa mashi baya. Tsalle ya yi ya taka wata bishiyar ɓaure dake kusa da su sannan ya juyo da karfi haɗe da haɗa hannayensa dikka biyu da karfi sosai ya dakawa damisan duka a tsakiyar kai, nan take damisan ya durkushen kafafunsa a kasa yana sakin wani irin kurnani mai ban tsoro da kuma ban tausayi, alamar Hoorain ya ji mashi ciwo a kai.

Ko kaɗan Hoorain bai yi niyar kashe shi ba, ganin ya yi ƙasa ya yi mubaya'a yasa ya rabu da shi, a hanzarce ya wuce ya nufi in da take yana sauke numfashi a hankali hankali.

Da hannu ɗaya ya ɗagota bayan ta duƙa. Kai tsaye wajen koramar ya nufa da ita. Cikin nitsuwa ya kwnatar da ita a saman dutse, ƙarisawa gaban koramar ya yi haɗe da tarar ruwa ya fara wanke jininsa da damusan ya fidda mashi, har lokacin sai jan numfashi kamar haki yake yi alamar wanda ya gaji.

Sai da ya wanke jikinsa tsab kafin ya dawo kusa da ita, cak ya sake ɗaukarta suka ƙarisa gaban koramar. Gabaɗayanta ya sanyata cikin ruwan.
Da ihu ta farka tana sambatun damusa zai cinyeta. Shi ma ruwan na jiƙasa, dan kusan a tare suka shiga cikin koramar, sai dai shi ta ɗan baki baki ne, da kyar ya iya ambatar sunanta da ranki ya daɗe.

Ina ai bata ma san yana yi ba, ihu ta cigaba da yi tana ƙoƙarin kwatar kanta, da alama bata cikin hayyacinta. Ƙanƙameta sosai ya yi, cike da tausayinta ya matsar da face ɗinsa ɗan dab da ita, sannan ya ce ta nitsuwa damusan ya gudu.

Jin hakan yasa ta yi saurin waro idanunta, ganinta a hannunsa kuma cikin indoron ruwan dake kwaranya yasa ta yi saurin juyar da kanta izuwa gefe da gefe tana neman ina damusan yake.

"Ki kwantar da hankalinki baya nan, ya tafi". Cike da so da kauna ya faÉ—a.

A tsorace sosai ta ce. "Ina ya tafi Hoorain?". Ta yi maganar tana kai hannunta saman face É—insa.
"Bai yi maka komai ba ko?" Ta sake tambaya tana shafa kumatunsa".

Jinjina mata kai ya yi haɗe da cewa. "Babu wata barazana ranki ya daɗe". Ɗan daure fuska ta yi haɗe da turo baki, a shagwaɓe ta ce. "Hoorain wai kai baka iya soyayya bane sai wani ranki ya daɗe kamar wani bosawa? Babu ko irin sunan love ɗin nan?".

Shiru ya ɗan yi tare da matsawa baya kaɗan ya fitar da ita daga cikin ruwan kenan, sannan ya rabata da jikinsa ya sauketa ƙasa a kan kafafunta.

"Hoorain baka bani amsa ba". Wannan karan murya a É—an kasashe ta yi maganar.

"Na iya soyayya, sai dai ina tinanin abin da zai je ya dawo shiyasa nike ja da baya, bana san dik abin da zai iya jawo mana matsala da ni da ke".
"Ban gane nufinka ba". Cike da mamaki ta yi tambayar.

Gyara tsayuwansa da kyau ya yi, cikin nitsuwa ya fara warware mata komai dan gane da abin da yake jiwa tsoron yasa baya san zurfafawa a soyayyarsu, baya san sakin jiki sosai.

"Ke da kanki kin san ƴan uwanki ba zasu taɓa yarda da ni a matsayin masoyinki ba, ba zasu taɓa karɓata ba, sannan kin san matsayina da naki daban daban, ke kanki ina jiyewa zuciyata tsoron ki juya mata baya, na san daddynki ba zai taɓa yarda ya bani ke ba, kema kuma kin san da hakan, idan muka cigaba da soyayya na tabbata wahala zamu sha, and nasan ke ba zaki iya jura ba, idan kin ji wahala kaɗan zaki guji zuciyata ki barni a wahale, wannan shi ne kaɗan daga cikin abin da nike guje mana".

Tabbas ta fahimci dalilansa, sannan kuma ta gamsu dalilai ne masu karfi da dole zasu iya sanya shi ja da baya, tasan King ba zai taɓa yarda ba, bama azo ga King ba, ko guyson ba zai yarda ba, ranar iya ganinta kawai ya yi ta kusa da part na mayaka ji yadda ya tashi hankalinsa bare kuma ace ya ji tana san assistant commander? Tab ai babu wanda zai goya mata baya, ko Chuchu ba zata bi bayanta ba a wannan gaɓar.

Amma dik da haka sai ta kallesa ido cikin ido, cike da tsantsar makauniyar soyayyarsa ta fara magana masu zafa kamar haka.

"Tabbas dik abin da ka faÉ—a haka ne, kuma ka fini gaskiya, amma akwai kalma É—aya da ka faÉ—a wanda ba hakan bane kuma ba zan lamunta ba!!".

Tattara mata hankalinsa a kanta ya yi yana sauraronta, cike da sa ran zata kawo masu mafita.

"Abin da ka faɗa ba daidai ba kuma shi ne cewa da ka yi idan na ji wuya zan juyawa zuciyarka baya, ka yi kuskure! Ban ga wata wahala da zata sa in juya maka baya ba a duniya, soyayyar gaskiya nike yi maka ba ta yaudara ba! Kada ka manta nasoka ne tin ban taɓa ganin kamanninka ba, tun da na taso a rayuwata bani da abin san kalla sama da kai, ka yarda dani, mu haɗa hannu zamu yi nasara! Na yi maka alkawarin a kai'na kuma dalilina dik ƴan uwana zasu canza su karɓeka a matsayin zaɓina hannu bibbiyu, ka mun alkawarin dik halin da zamu shiga ba zaka taɓa ja da baya a kan soyayyarmu ba?".

Ta kai karshen maganar tare da buɗe tafin hannunta ta miƙo mashi. Da yake jajirtacce ne babu tsoro a tatare da shi sai bai yi wani tinani ko ya damu ba, shi ma ya buɗe tafin hannunsa ya ɗaura a saman nata.

"Na yi maki alkawarin babu gudu babu ja da baya kome zai faru ina kan bakata na ina sanki!".

Ajiyar zuciya ta sauke, cikin sanyin murya ta ce. "Tabbas ba zan baka kunya ba, kuma na yi maka alkawarin sai dai a zare raina da soyayyarka a kirjina, ba zan taɓa san wani ba kuma ba zan taɓa yarda a haɗani da wani ba".

Wani irin bargon farinciki ne ya lulluɓe zuciyarsa, ya ma rasa abin faɗe, sai dai kawai ya yi shiru yana jin wani sanyi tana ratsa zuciyarsa.

"Yanzu meyakamata mu yi?". Cewarta kenan. "Gida zamu tafi yanzu, hanya zamu É—auka, gobe zamu iya isa".

"Har na ji bana san mu koma yanzu, kamar mu kara kwana biyu a nan, wajen akwai daÉ—i sosai". Cike da yaranta a word É—inta ta yi magana.

Kai ya girgiza tare da riko hannunta da kyau a cikin nasa, ƙasa ƙasa ya ce mu je. Bata yi musu ba ta bi bayansa suka tafi wajen Pretty, har lokacin sai barci take zubawa.

Kamar zai tambayi Auta su tafi da Pretty ko su barta a wannan dajin tun da ta faÉ—a mashi a nan suka sameta. Sai kuma ya ji ba zai iya tafiya ya barta ba, tin da suka ganta haka bata da kowa kenan, dan haka su tafi da ita kawai.

"Jirani ina zuwa, ki tashi Pretty kafin na É—auko dokina". Yana kai karshen maganar ya sake hannunta, bai jira amsarta ba ya wuce da sauri izuwa É—an baya da su kaÉ—an.

Ita kuma ta wuce ta tashi Pretty daga barci, yana dawowa suka hau saman dokin da dik wani abin da zasu buƙata, wajen da suka yi faɗa da damusan nan ya koma ya ɗauki takobinsa, sannan suka kama hanya, Auta a gaba Pretty a tsakiyansu shi a baya, ba komai yasa yaki saka Auta a tsakiyansu wato kusa da shi ba face kaucewa sharrin shaiɗan.

Auta ta manta da tana jin yunwa, haka suka kama hanyar nufar Kingdom of power..... To sai dai mu ce Allah ya kaiku lafiya.

•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥

🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥

2:30am.

Dare ta tsala sosai, ko'ina ya yi tsit, dik wani na kirki yana cikin gidansa, banda kukan karnikan Ramish su bisho dake tashi babu wani abin da zaka ji.

A hankali karan Acn É—akinta yake tashi. Kasancewar bata da nauyin barci ko kaÉ—an hakan yasa in abu ya motsa a kusa da ita tana ji kuma yana farkar da ita, dama dik wanda ya yi zaman gidan yari da wuya ya iya nauyin barci.

Ta yi nisa cikin barcin da take yi cikin kwanciyar hankali, yau tana farincikin ta amayarwa masu nikaf kunan da ya daɗe yana babbaka ranta, yau ta samu sai'da da salama, har ta ji bata taɓa yin barci mai daɗin wannan ba.

Can a tsakar kanta ta ji kamar an taɓa mata kofar ɗaki, dik da tasan ba ita kaɗai take kwana a ɗakin ba, amm tasan yau Sharifat bata nan, kuma da wuya ta dawo cikin wannan daren.

A karo na biyu ta sake jiyo an mai da kofar nata an rufe tamkar wani ne ya shigo ya rufe, kamar a mafarki ta ji ana datse keys na kofar wanda tun da suke daga ita har Sharifat babu wanda ya taɓa datse wannan kofar da keys ɗinsa.

Hakan yasa ta zabura ta miƙe zaune, ɗakin duhu bakin kirin, dan yau ko lamp dama bata kunna ba. Wani irin ɗan motsi ta ji kamar alamar tafiyar jami'i a yakin sunkuru, ko kaɗan bata tsorata ba, dan ba ƙaramin abu yake tsoratata ba ita.

Cikin dabara ta laluɓa ta sauko kasa daga saman gadon, tamkar wata hawainiya ta fara taka kafafunta ta nufi switch. Unexpect ta isa wajen ta kunna wutar ɗakin, nan take haske ya gauraye ko'ina.

Ya ilahi ya lilliahi, wani irin mahaukacin razana ta yi. Idanuwanta ne suka yi mata tozali da wani tsayayyen namiji cikin shigar ban tsoro, baka iya ganin komai daga jikinsa, from up to down gabaɗaya bakaken kaya ne a jikinsa, fuskarsa rufe yake da tactical mask, ba zaka taɓa iya gane wanene bane, kafafunsa na sanye da combat boots masu karfin gaske. Ga shi a tsaye a tsakar ɗakinta, ya rufe kofar ɗakin kuma da key babu halin gudu ta fita.

Sosai ta razana, da karfi ta waje baki zata zunduma ihu kamar walkiya haka ya wurga mata wani abu mai kamar da karfen star a baki.
Chapter 82 · 0% Book details