← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 160 OF 242

Sashe 160

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kazalika a cikin Suratul Ma’ida sura ta biyar 5 aya ta 32 Allah ya sake yin magana a kan haramcin kashe rai. Allah ya yi gargaɗi mai tsanani ga al’umma da suke kashe juna da zalunci, a cikin Suratul Baqara sura ta 2 aya ta 195, manzan Allah ya ce kisa yana ɗaya daga cikin manyan zunubai".

Da alama tashin hankali ya rufe mata idanu da take zazzaga mashi waÉ—an nan karatun, ta mance a in da take, a wannan karon shi ma Ronnie sam bai yi gigin hanata ba, dan burinsa ta kowacce hanya su dakatar da Black Tiger daga kashe waÉ—an nan mutane, shiyasa ya kyaleta ta faÉ—a mashi girman Allah ko zai saduda ya hakura zuciyarsa ta sanyaya.

Sai dai kash, kamar babu alamar saduda a tattare da shi, dan kuwa babu alamar zatukanta sun ratsa ƙwaƙwalwarsa, sai ma juyawa da ya yi ya cigaba da yin abin da yake yi, babu alamar mutanen birnin zamu samu koda kwayar zarra na sassauci daga garesa.

Ganin hakan yasa suka kara shiga tashin hankali matuƙa, Ronnie ya shiga damuwar da har idanunsa sai da suka ciko da kwallah, ita kuma Sweetie a cikin zuciyarta ta sha alwashin yau ko mutuwa zata yi sai da ta mutu amma ba zata barshi ya cigaba da wannan bakin zalinci na CROWN OF INJUSTICE ɗin ba, yanzu ne lokacin da zasu rinƙa fito na fito da shi dan faɗa mashi gaskiya sai dai komai zai faru ya faru, dik wata rufa rufa da tsoro yanzu zasu ajiye a gefe su yi shahada su yi fito na fito.

Dan haka tana ganin bai wani saurareta ba ya cigaba da yin aikinsa a matsayin ta shiga tsakaninsa da laptop ɗin, hannayensa dikka biyu ta riko cikin nata, tsabar tsoro sai kerma jikinta yake yi, amma tausayin mutanen birnin ya rufe mata idanu a in da ta zaɓi mutuwa dan cetonsu. Cikin dakiya ta ce. "A gaskiya ba zaka kashe kowa ba big bro, ya isa haka nan, zunubin da ka kwasanwa kanka a baya shi muke ƙoƙarin ganin ka tsarkaka daga shi, dan haka Allah ba zaka sake kwasanwa kanka wani zunubi ba, dan muna kaunarka!". A wannan karan cikin sanyin murya ta yi maganar, dan ta lura dik wasu tada jijiyoyin wuyarta a banza yake tafiya, shi Black Tiger ma wlh idan ka yi mashi magana cikin natsuwa da tausasa kalamai ka fi cin riba a kansa sama da idan ka ɗaga murya, in ka ɗaga murya ma ai sai dai ka ci azaba a hannunsa ba dai riba ba.

My people's me kuke tinanin zai faru? Black Tiger zai janye kudurinsa a kan mutanen birninsa kuwa? Zai yafe masu? Shi da Sweetie da Ronnie waye zai yi nasara?. Muje zuwa.

🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥

Washegari da safe, sai almost karfe 8 Ramish ya iya farfaɗowa daga sumar da ya yi bayan wannan aika aika da ya aikata, yana gama samun natsuwa dama ya sume kwance kusa da ita. Bilal ya buga wayarsa tun da daɗin rai har ya fara shiga tashin hankali, ya ƙasa zaune ya kasa tsaye, dan haka gari na wayewa ya fita gidan da sunan ya je nemansa, ko kaɗan bai kawowa ransa cewa Ramish na sama ba, sai ya yi waje nemansa.

A lokacin da ya farfaÉ—o ji ya yi jikinsa tamkar ba nasa ba, gabaÉ—aya ya canza, kansa ne take sara mashi tamkar zata fashe, wani irin jiri yake gani sosai, da alama har yanzu maganin nan bata gama sakinsa gabaÉ—aya ba bawan Allah, idanunsa tamkar wuta saboda ja, har lokacin jijiyoyin jikinsa a tsaitsaye basu koma sun kwanta ba, arab hairnsa tamkar wanda aka kwato daga bakin kura, gabaÉ—aya a hargitse yake, idan ka gansa sai ka tausaya mashi, shi ma kenan, to ina ga Leesharh kuma? Ya kuke tinanin zata kasance?.

Ya sha madarar mamakin ganin babu tufafi a jikinsa, ɗan waige waige gefensa ya fara yi, ai a miliyan ya zaro idanunsa waje lokacin da ya ga Leesharh kwance a gefensa cikin jini, ga sofar da suke kai ɗin fara ce tas, hakan yasa gabaɗaya jini ya yi kaca kaca da waje. Dafe kansa dake barazanar tarwatse mashi ya yi, idanunsa ya datse gam, take ƙwaƙwalwarsa ta fara tariyo mashi abubuwan da suka faru daren jiya. Tsab ya tina komai, innalilahi wa inna ilahir rajiun shi ne kalmar da ya rinƙa maimaitawa a ransa, ya maimaitata ya fi sau hamsin a in da yake zaune, tamkar wanda ya yi mangaribar jemage, lokacin guda jikinsa ta yi mugun sanyi, da karfi ya dafe forehead ɗinsa, wani irin ihu ya kurma da karfi wanda bai san dalilin yinta ba, ga dikkan alamu zafin da zuciyarsa ta ɗauka ne yasa hakan.

Dama na faɗa maku dik ihun da za'ayi a cikin wannan ɗaki na waje ba zai iya ji ba, bangon wajen tamkar soundproof yake. Miƙewa tsaye ya yi, yana tangal tangal tamkar wanda ya sha barasa ya bugu ya nufi gaban computers dake wajen, da kyar ya iya ƙarisawa wajen, hannayensa dikka biyu yasa ya dafe dest ɗin, wani irin huci ya fara fitarwa da karfi karfi, numfashinsa na fita da wani irin ɗumi mai ban tausayi.

(Abin akwai ciwo gaskiya, ace tin da ka taso baka taɓa zina ba, baka taɓa sha'awar yinta ba, hasalima kyamatarta kuke yi, rana tsaka ka tsinci kanka da aikatata! Wlh dole ya ji zafin hakan, yanzu ya zai yi? Da wani ido zai ganta? Shin zai iya gane me ya janyo mashi aikata hakan? Idan ya gane wani mataki zai ɗauka? Shin zata yi mashi uzuri ta yarda ba halinsa bane?.)

Ƙwaƙwalwarsa ce ta sake tariyo mashi yadda ya haikewa yar mutane a daren jiya, take ya tuno kalamanta da take faɗin. "Yah Ramish kada ka yi mun irin wannan hukunci, ka yi mun dik abin da kake so da ya danganci azabtarwa, amma dan Allah kada ka rabani da mutumcina, wlh ni marainiya ce da bani da kowa, bani da iyaye, mutuncina shi ne kawai abin da ya rage mun mai daraja a tattare da ni, ka dubi girman Allah kada ka lalata mun rayuwa, ni ban karɓi wannan aiki saboda na cutar da kai ko wani abin makamancin hakan da gangan ba".

Tana kuka hawaye sharɓa sharɓa tana kora mashi waɗan nan jawabin. Ai hankalinsa ne ya kara tashi, ransa ya kai ƙololuwa wajen ɓaci, cikin fitar hayyaci yana huci ya sake kurma ihu da karfin gaske, cikin zafa yasa hannun da karfi ya fara watsi da gabaɗaya computers dake wajen, da karfi ya ɗaga dest ɗin mai gabaɗaya ya yi watsi da shi komai dake kai suka zube ƙasa suka tarwatse watsa watsa, dunkule hannunsa ya yi ya fara bugun jikin bangon wajen da karfi karfi yana huci har sai da ya yi raga raga da yatsun hannunsa ya jiwa kansa ciwo, gwanin ban tausayi ya zube gwiwowinsa a kasa a wajen tare da haɗe kansa da jikin bango, a dik lokacin da ƙwaƙwalwarsa ta tina mashi cewa Leesharh ta gansa tsirara kuma har ya yi abinga da ita sai ya ji tamkar ya rataye kansa, ya ji kamar ya yi ta buga kansa da bango har sai rai ya yi halinsa, zuciyarsa na azalzala mashi da ya yi ajalin kansa kawai, sai dai shi ɗin mai addini ne yasan hukuncin wanda ya kashe kansa.

Lokaci guda mugu mugun tausayin Leesharh ya rufesa, kalamanta dake yawo a cikin kansa shi ne cewa da ta yi marainiya ce ita, hakan yasa ya ji wani irin kululun bakinciki ya tokare mashi maƙoshi, da kyar ya miƙe tsaye hannunsa na zubar da jini, in da take ya nufa har lokacin yana tangal tangal kamar zai faɗi.

Kallo ɗaya ya yi mata ya yi saurin kawar da kansa, kasancewar babu tufafi a jikinta sannan gata cikin jini. Gabaɗaya ya ji ya tsani kansa, Innalillahi wa inna ilahir rajiun. Shiru ya yi ya rasa madogara, dan kuwa ko kayan da zai saka a cikin wannan ɗaki babu, wancan kayan nasa kuma ya yagesu gabaɗaya ya zubar. Ya jima tsaye a wajen saboda rashin madogara, daga karshe dai ya laluɓo wayarsa can kusa da computers da ya farfasa, Allah ya cecesa wayar bata yi komai ba.

Uban tilin miss calls ya samu wanda ciki na Bilal ya fi na kowa yawa, ga na Ummie da ta yi ta kiransa daren jiya dan jaraba, wai so take ta tambayi ina yake sai ta je ta same shi, bata san a lokacin baya duniyar nan ba, yana can duniyar mercury. Sam bai bi ta kan miss calls ɗin ba, number Sharifat kawai ya laluɓo ya dannawa kira. Bugu ɗaya ta ɗauka, cikin kuka ta yi mashi sallama, yau karon farko a rayuwarsa ya ji faɗuwar gaba ta riskesa, tamkar yasan me Sharifat take yi wa kuka, wato ta nemi Leesharh bata ganta ba, kun san tun daren jiya take nemanta.

Daurewa ya yi ya yi ta maza wajen cewa. "Ki je bedroom É—ina ki É—auko mun pjs set biyu ki kawo mun wajen stair case na É—akin bincikenmu dake sama, ki ajiye mun a wajen ki tafi". Yana kai karshen maganar ya yi gaggawar katse kiran dan ma kada ta kawo mashi zancen dalilin kukanta, dan yasan kwanar zancen.

So ba karya ba, tana bala'in sonsa hakan yasa ta iya gane baya cikin kwanciyar hankali da natsuwarsa, ta tabbatar yana cikin tashin hankali daga jin voice ɗinsa, dan haka ita ma nata hankalin ne ya kara tsananta tashi, ta rasa ina zata sanya ranta ta ji daɗi, ga shi ta tambayi Ummie ko taga Leesharh Ummie ta ce mata kada ta sake yi mata batu kan Leesharh, gabaɗaya ta rasa wanda zata je wajensa ta ji sanyi a ranta, Abbie baya nan ya fita. Miƙewa ta yi jiki ba kwari ta fito waje, da yake tana cikin tashin hankali sai bata wani damu da ta yi tinani a kan me Ramish zai yi da pjs har set biyu ba, kawai ta nufi bedroom ɗin nasa.
Chapter 160 · 0% Book details