← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 156 OF 242

Sashe 156

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Abbo dan Allah ka amsa mun, Hoonaira bata zo bane?". Ya faɗa cikin raunatacciyar murya. Jinjina mashi kai commander ya yi alamar e bata zo ba, ya kasa iya furta word, dan ba shi da abin faɗe. Tafukan hannunsa Hoorain ya buɗe tare da matsar da hannunsa kusa da hannun Abbon nasa, da yake commander yana zaune a saman chair na masu jinyar majinyata. Hannun Abbon nasa ya riko cikin nasa. Cikin wata iriyar wahalalliyar murya irin na wanda ya sha azaba, da kyar da kyar ya fara magana cike da dakiya da jarumta, wlh ba dan assistant commander ne shi ba, ya saba da wahala saboda irin horan da ya karɓa, Allah da ba zai iya ɗaukar wannan horo ba, ba'a taɓa sanya mutum a ɗakin duhu ya wuce kwana uku ya fito a raye ba, kwana ɗaya idan mutum ya yi aka fitar da shi sai ya sha jinya na satittika, kuma kafafunsa basa iya takawa, amma shi almost week, ya fito kuma bai yi wani dogon jinya ba ya farfaɗo, ba shakka yana da jarumta sosai, commander ya iya renon ɗan nasa, ya mayar da shi zaki ɗaya tamkar da dubu.

"Abbo ina san Zunaira, ina santa fiye da yadda nike san rayuwata, a da kafin in bayyana mata soyayyata a gareta ina jin kamar zan iya dannewa in mutu da santa, amma tin daga ranar da na bayyana mata na gane cewa tabbas ba zan iya hakuri na danne sonta har in koma ga Allah ba, please Abbo ka taimaka mun, dik wani hukunci da zaku yi mun ku yi mun na yarda, amma dan Allah kada ku rabani da Zunaira, ba zan iya jurar wannan zafin ba, gara mun zafin wuta a kan wannan zafi, ban taɓa neman wani abin a wajenka na rasaba, shiyasa a kullum nike kara yin alfahari da kai, a yanzu ma ga buƙatata na kawo maka dik da nasan kai ma baka da iko a kan hakan". Ya kai karshen maganar wasu zafafan hawaye da suka cika mashi idanu ne suka zubo ta gefe da gefen kunnensa saboda yana kwance ne. Idanunsa jajir kamar wuta, kirjinsa na suya matiƙa, yana jin zafi tamkar an ɗaura shi a saman wuta, ya rasa a ina zai sanya ransa ya ji daɗi.

Wani irin zabura commander ya yi, dan tin da yake da Hoorain bai taɓa ganin hawayensa (tin da ya yi wayo kenan ba tin yana jariri ba) lallai girman san da Hoorain yake yi wa Zunaira ya wuci misali, yau saboda santa ya yi kwallah? Innalilahi wa inna ilahir rajiun, yanzu da wani idanu commander zai kallesa da kudurinsa na rabasu?. Take commander ya ji ko mutuwa zai yi sai dai ya mutu amma ba zai iya cewa Hoorain ya rabu da Zunaira ba, ba shi da wannan kwarin gwiwa, Hasbunallahu wani'imal wakil, shi ne kalaman da commander yake ta mainaitawa a ransa.

A dai'dai wannan gaɓa guyson ya kawo mashi waya domin su yi waya da Auta, ai saboda farinciki Hoorain bai san lokacin da ya miƙe zaune tare da tsige drip dake manne a hannunsa ba, murna a wajensa ba'a magana. Yana magana da ita zafafan hawaye suna bin ƙuncinsa, wlh sai da guyson ya taya shi zubar da hawaye, ya tausaya masu matuƙa, sai yake jin tamkar ya ɗaura masu aure kawai, sai dai bashi da damar yin hakan, sai kawai ya hau tayasu da addu'a, ga azumi ya kawo kai, sai ya yanke shawara a cikin zuciyarsa a kan zai sanar da King zai tafi saudiya ya sauke farali, idan ya je ya yi alkawarin tun ranar da ya dira har ya dawo sunansu ne zai kasance a bakinsa, addu'a ba dare ba rana zai yi masu, wannan hali da suke ciki dole a yi saudiya da sunansu, in ba haka ba akwai matsala, shi yasan idan ba Allah ba babu wanda ya isa ya canza rantsuwar King a kansu!!.

Bayan sun gama magana da ita ko in ce wancan baturiya ta kwace wayar ne ya bawa guyson wayarsa tare da dawo da kallansa a kan Abbonsa. "Abbo ina wayata?". Ya faÉ—a yana goge hawayensa. Allah Akbar, my people's soyayya idan ba'ayi dace ba wlh musifa ce, yau assistant commander of dangerous warriors ne yake hawaye a kan mace? Macen ma under 15 ba wata macen azo a gani ba, innalilahi akwai matsala fa.

Kasa jurar ganin halin da yake ciki guyson ya yi, dan ya ga kamar Hoorain fa ya samu matsala, da gudu ya juya ya bar room ɗin, dan yana da raunin zuciya bawan Allah. Shi kansa commander ji yake yi tamkar ya taya ɗan nasa hawaye, dan wani irin tausayinsa ne ya kama shi matuƙa. Hannu kawai ya kai yana taya shi goge hawayen yana faɗin. "Hoorain ya isa kukan nan haka ka ji? In Sha Allah Allah yana tare da kai, idan gimbiya matarka ce babu wanda ya isa ya zama barazana ko shamaki a tsakaninku, ina da yakinin Zunaira matarka ce, ka yi hakuri".

Rungume Abbon nasa ya yi, cikin zafin zuciya da raÉ—aÉ—i ya ce. "Abbo dole waÉ—an nan hawaye ba zasu dakata daga zuba daga idanuna ba har sai na dakatar da na Hoonairata, saboda a cikin zuciyata na ji kuka take yi a yanzu, dan Allah ka bani wayata domin in kirata in dakatar da nata hawaye zaka ga nawa ma sun dakata". Out of control yake maganar. A dai'dai lokacin da ya yi wannan magana tabbas kuka Auta take yi, dan a lokacin tana bawa Smart labarin abin da yake a tsakaninsa da my heronta. Soyayyar gaskiya daban take, ya so ta tin tana jaririya ai dole ya iya fahimtar halin da take ciki.

Abbo ya fahimci Hoorain fa baya cikin hayyacinsa dan haka sai ya ce. "Ka yi shiru wayarka tana hannunsu Ansar, yanzu zan sa a karɓo maka, ya isa haka ka ji?..........".

Commander bai gama tufe baki ba sai ga sallamar Ansar and Anwar aminan kwarai sun shigo, da ka gansu zaka fahimci suna cikin damuwa da tashin hankali, ba jimawa suka bar hospital É—in, wanka suka je yi, dama suna a tare da shi suna taya commander jinya bayin Allan, su suka yi jinyar commander É—in ma har ya warke, yanzu kuma suna taya shi yin na Hoorain.

Hoorain yana ganinsu ya zabura yana faɗin su bashi wayarsa. Ansar ne ya ciro wayar daga aljihunsa tare da na Auta da yake wajensa ya miƙa mashi yana faɗin. "Our lion lafiya kuwa?".

Ai ina bai amsa masu ba, kunna wayarsa ya yi, jikinsa har yana ɓari ya shiga contacts, sai kuma me? Ya rasa wani number zai kira, dan bashi da numberta na Paris, wayarta ma ai gata a hannunsa. Da karfi ya ɗaga wayar tasa ya yi wurgi da ita dan takaici, sai dai Ansar ya yi gaggawar capke wayar bata isa kasa ba, da tarwatsewa zata yi, ransa ne ya kara jagulewa, zuciyarsa tana tafasa ya juya ya kifa kansa da jikin bango yana wani irin huci mai fita da karfi karfi.

Gabaɗaya sai da suka yi matuƙar tausaya mashi, take jikinsa ya kara tsananta zafi sosai, zazzaɓi ne ta rufesa sosai. Miƙewa tsaye daga kan chair commander ya yi tare da tallabo ɗan nasa da kyau domin ya taushesa, ya san shi da ɗan banzar zuciya, tsoronsa kada ya je ya haɗiyi zuciya dan ɓacin rai ya mutu su shiga uku, idan Hoorain ya mutu ina zai sanya ransa?. A gaggauce su Ansar suka matsa kusa da shi dan su taushi zuciyar zaki kada ta buga. Sai huci yake yi bai iya cewa komai, ya dai datse idanunsa gam alamar baya san ganin kowa. A dai'dai wannan lokacin kuma Smart yake rarrashin Auta yana yi mata alkawarin zata mallaki Hoorain while shi ma commander alkawari ya shiga yi wa Hoorain a wannan lokaci a kan in dai yana raye to da izunin Allah zai mallaki Zunaira, ya yi hakuri ya daure har ya samu lafiya. Sai dai ina, Hoorain bai iya amsawa ba, bayan wannan huci babu wani abin da zaku ji yana fita daga garesa.

A ɓangare guda kuwa, Chuchu dai ta lallaɓa ta gudu ta koma part ɗin Akka da zama, tun safe take can, har dare taki komawa part ɗinta, da yake yau Jawad ya je office to bai dawo da wuri ba, saboda aikin King na gina wasu makarantu dan marasa galihu, so wannan aiki ta tsayar da shi, sai ana kiran mangariba ya shigo gida. A gaggauce ya yi wanka ya wuce musque. Bai dawo ba sai da ya yi sallar isha'i a wajen, sannan ya dawo gida.

Part na King ya fara zuwa, sai da suka gaisa suka ɗan yi hira kaɗan kafin ya wuce wajen momma domin su gaisa, dan tun safe basu haɗu ba. Ita ma suka ɗan taɓa hira na kamar ten minutes, sannan ya yi mata sallama ya fito, yasan yana da mara lafiya, hankalinsa dik yana a kanta, dan ma dai ba laifi ta samu sauki saboda wadataccen kulawa da ta samu daga wajensa.

Bedroom ɗinsa ya nufo yana tinanin yadda zai yi da ita yau, dan gaskiya batu na Allah a matse yake, yana hannu, ita kuwa tsoronsa take ji, jiya ya yi ya yi da ita ta bashi haɗin kai, amma ta murje idanu ta ce bata san wannan zance ba, ko taɓata taki yarda ya yi, da ya taɓata zata saka mashi kuka, ya rasa me zai yi mata, ga shi su kuma jarabarsu fa ba irin wadda za'a iya dannewa ta dannu bane, shiyasa kuka ga suke yawan san shan cappuccino, dan yana ɗan sassauta masu, kun gano su ko?.

Ya yi mamakin ganin bata a cikin bedroom É—in, ya kuma san bata part na momma, dan da tana can momma zata ce mashi gata nan su wuce a tare. Toilet ya nufa cike da tinanin ina ta tafi? Wanka ya yi ya fito ya shirya cikin sleeping dress É—insa masu kyau. Waje ya fito sai tashin kamshi yake yi, kai tsaye ya nufi part na Akka, dan yasan bata wajen mummynta, bata cika zuwa can ba, in bata wajen momma to tana wajen Akka.
Chapter 156 · 0% Book details