← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 198 OF 242

Sashe 198

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bobo ya gano cewa dik sarakunan da suka gabace sa, rawanin ya mai da su masu mugunta, yana rage musu tausayi kuma yana ƙarfafa su su yi zalunci ba tare da rashin jin daɗi ko kunya ba. Wannan yana nufin idan har shi ma ya sanya rawanin to zai zama azzalumi kamar su. Babbar magana! Ya shiga ruɗani mai girma gano cewa yana da yaya namiji da mahaifinsa ya kashe domin ɗale kan kujerar mulki, ya sadaukar da jininsa ga BLOOD CROWN kenan, bala'i iya bala'i Bobo ya shiga a wannan lokaci, nan fa ya fara tinanin mafita a garesa dama ƴan uwansa bakiɗaya, dan ba zai taɓa iya bada ko mutum ɗaya daga cikin huɗun nan ba, ba kuma zai iya bari a cigaba da wannan ɓarna ba, saboda a lokacin shi ya musulunta ba tare da saninsu ba, a makarantarsu ya karɓi musulunci daga abokinsa wato Smart, tare suka yi karatu a ƙasar France, a lokacin da aka ce ya karɓi mulkinma hutun school ya dawo, daga nan suka rikesa wai karatun ya isa haka, lokacin hawansa gadan mulki ya yi! Dama shi ya matsa yana san karatun!.

Daga nan Bobo ya fara shirin wargaza mulkin zalunci. Sai dai hakan yana da gagarumin hatsari da barazana ga rayuwarsa da ƴan uwansa. Sama da sau goma ƴan majalisar masarauta tana yin zama a kansa, sun tursasa mahaifinsa a kan ya sanya shi dole ya ya zaɓi wadda ya fi kauna ya kasheta a karawa CROWN ɗinsu karfi, dan da alama zasu iya fuskantar marazana daga wasu masarautun idan basu yi gaggawar bada jini sun karawa RAWANIN karfi ba. Sai dai dik yadda za'ayi da Bobo anyi yaki buɗar baki ya ce ga wadda ya fi so, da zarar an yi mashi magana sai ya ce su ɗan kara mashi lokacin. Ya yi kokarin canza dokokin masarautar, amma ƴan majalisar masarauta sun dakatar da shi game da daka mashi zazzafar warning a kan zai iya rasa ransa idan ya yi kuskuren taɓa doka guda ɗaya daga littafan dokokinsu, dole ya bi komai kamar yadda ya ganta a rubuce, tsawon shekaru suke a kan wannan tsari. UHM ABIN TAKAICIN MA WAI WANDA YA FI KAUNA ITA ZA'A KASHE, WLH BASU DA IMANI KO KAƊAN MUTANEN NAN!!.

Bobo ya yi iya tinanin da zai yi, amma ya kasa samawa kansa mafita, saboda sun fi karfinsa, bai isa ya yi fito na fito da su ba, sun fishi yawa, hakan tasa ya koma gefe ya yi shiru dan tinani a natse ko za'a samu mafita. Daga karshe ya yanke shawarar fitar da sirrin familynsa ga abokai ko zai samu maslaha, hakan yasa ya kira Smart a waya ya sanar da shi ga halin da yake a ciki, ashe dama sarautarsu ba ta Allah da annabi bace, sosai Smart ya yi mamakin jin hakan, a lokacin suna a tare da Zash, dan su ukun a tare suka yi karatu.

In short dai Smart ya ce da Bobo ya ɗauki ƴan uwan nasa ya bar ƙasar, dan faɗa fito na fito da su lokaci guda ba zai yiwu ba, dole sai sun yi shiri, idan kuma ya ce zai zauna a tare da su har su yi shiru zasu iya matsa mashi, idan bai biya masu buƙatarsu ba zasu iya kashe shi, dan ya rigada ya san sirrin RAWANIN JINI. Wannan dalilin yasa Bobo ya shirya makirci cikin dare ya ɗauke mom ɗinsa da kannen nasa dikka biyu ya gudu da su zuwa kasar France, Smart ne ya tsaya mashi tsayin daka sosai, mom ɗinsa dama a tsananin tsorace take, hankalinta a mugun tashe, tana cike da fargabar waye ɗanta zai zaɓa ya fiso, tsoronta kada ace ita ce, kun san wanda baya tsoron Allah da shegen tsoron mutuwa, wlh billahi dik wanda baya tafarkin Allah shegen tsoron mutuwa ne da shi kamar me, dik wanda yake da karfin imani baya tsoron mutuwa, dan already yasan sai ya mutu, kuma idan na kwarai ne shi yasan lahira ta fi mashi duniya sau miliyoyin miliyoyi, dan haka zai so ya tafi lahira ma sai ta fi mashi.

Mom ɗinsa tana tsorace, dan ita tasan wannan al'ada, amma kannensa mata basu san wannan al'adar ba. Lokacin da ya shirya ya ɗaukesu daga kasar ba karamar daɗi mom ɗinsa ta ji ba, sai dai kuma taki ta musulunta har wa yau, ba yadda bai yi da ita ba, har ya faɗa mata cewa saboda addinin musulunci yasa bai yi sadaukarwar jini ba, musulunci yasa bai zaɓeta an kasheta ba, dan haka ta musulumta shi ne addinin gaskiya, amma matar nan ta ce babu wannan magana, ba zata musulunta ba, har da cewa Allah ya yi wa Musulunci albarka da ya kuɓutar da su, amma dai ita ba zata musulunta ba, Smart ya ce mashi ya cigaba da binta a hankali kamar yadda shi ma yake lallaɓa mom ɗinsa ta musulunta, idan suna da rabo watarana za'a dace, to haka dai suka yi, kunji kaɗan daga tarihin Bobo. Amma fa har yau har gobe neman Bobo suke yi dan su kashe shi, ya karya alkawari da dokokin BLOOD CROWN, suna nemansa kamar hauka, yanzu an dai'na tinanin ya hau mulki ma, tinanin kashe shi kawai ake yi, jininsa za'a baiwa BLOOD CROWN! Tashin sense, kai akwai cakwakiya fa, bamu fara wasan ba, ku jira bayan bikin Auta balbalin kura zai taso daga sararin samaniya, gobara zata taso daga kogi, wanda kwantar da wannan bala'i sai Allah kawai!!.

Kada ku ga laifin mahaifiyar Bobo na kin musulunta, saboda mijinta ya taɓa hawa gadan mulkin BLOOD CROWN, kamar yadda mijinta ya sanya wannan RAWANI imani da tausayi ya fita a ransa, haka zalika ita ma majalisar dokokin masarautar masu alhajin kula da BLOOD CROWN suka cire mata dik wani tausayi da imani, shiyasa bata yi wa su Bobo da sauki, wlh barema Bobo, yana shan wahala a hannunta, tana tauye masu hakkinsu, bata san barinsu su sarara, harta ƴaƴanta mata, tana da bakar zuciya na mugunta sosai, kafin su iya samu ta dawo na kwarai to fa sai ranar da aka ruguje BLOOD CROWN!!. UHM AKWAI RINA A KABA!!.

INTERMISSION. NAN SHI NE TAAKIYAR LITTAFIN RAWANIN ZALINCI.🔥♥️

--------------------------------🔥♥️

To fa, mun zo dai'dai wani gaɓar da dikka masarautu biyar na RAWANIN ZALINCI suka gama bayyana, zan lissafo maku su sai in baku aikin zaƙulo stars ɗinku daga kowacce masarauta. Na farko akwai KINGDOM OF POWER, na biyu CROWN OF INJUSTICE wato BLACK WORLD, na uku akwai KINGDOM OF JUSTICE, masarautar Queen Zarina kenan, na huɗu akwai EVIL KINGDOM, masarautar su Yusuf, na biyar akwai, BLOOD CROWN, masarautar su Bobo, dama na ce maku masarautu biyar ne, kuma dik mugan abokan gabane da basa shiri kwata kwata, kuna dai gani yakar juna suke yi, RAWANIN ZALINCI ya zo da sabbin salo na daban, stars na littafin nan su bakwai ne zuwa takwas, kowanne kuma zai fito daga ɗaya daga cikin masarautun nan, KINGDOM OF POWER ce kawai take bada stars guda biyu, yanzu aiki ya ragunmaku, dikka masarautu biyar sun bayyana, saura a fara ainahin yakin bayan bikin Auta kenan, dama in da nike ta fatan in iso kenan, kuma Allah ya kawo mu!. A yanzu ba zan kira maku Stars da kowacce masarauta zata bayar ba, daga matansu har mazansu, saboda kuna tare da dayawansu ne baku san daga ina suke ba, idan kuka san daga in da suka fito a nan ne zan bayyana maku kowani masarauta da stars ɗin da ta bayar, amma ku cigaba da canki cankanku...... 🥱😅

(Kam bala'i, gaskiya RAWANIN ZALINCI ya zo da salo na daban, wai har yanzu laluɓar stars ake yi! Tab to akwai show a nan gaba, ku mu je dai zuwa, zaku sha mamaki fa.😅 To amma a Black world dai mutum biyu muke da su da zasu iya zama star, akwai Ronnie da King Lucian, amma bamu sani ba ko wani zai bayyana a gaba, sannan a masarautar Queen Zarina akwai Rishan ko kuma Ude, na gaba, a masarautar evil kingdom akwai Yusuf da Adam.🥱😅 Masarautarsu Bobo wannan kun rigada kun sani na faɗa maku cewa Bobo na daga cikin stars guda shiddan nan, a kingdom of power kuma waye kuka zaɓa a matsayin star? Wannan fa ba zaɓina bane, zaɓin ƴan special grp ne, ni tukun nan ban zaɓa maku stars ɗin ba, ku jirani bayan bikin Auta da Abdussalam akwai tada tarzoma, dan lallai kwakwalwarku zata yi caji fiye da tinaninku, muje zuwa cikin labari my people's)

----------------------------------------🔥🔥🔥

Kwanciya Bobo ya yi a saman sofa yana kallan Zash dake latsa waya, shi ma Smart Zash ɗin yake kallo, kamar suna zargin ya ɓoye masu wani abin ne. Shi kuwa hankalinsa gabaɗaya a kan wayarsa. Bobo zai yi magana phone ɗinsa ta gara ringing. Cikin natsuwa ya cirota daga aljihunsa yana ɗan lumshe Amber eyes ɗinsa kamar yana jin barci, lovely sis shi ne sunan dake yawo a saman screen ɗin, picking ya yi tare da matsar da wayar can gaba domin su ji daɗin ganin juna da kyau, video call ta kirasa. Wata kyakkyawar yarinya ce mai kama da shi sosai, idanunta starry Eyes ne masu bala'in kyau, kwayar idanunta Jade ne, suna wani walkiya kamar ruwan hawaye ne kwance a cikinsu, kuma haka suke, shi kuma Bobo phoenix Amber eyes yake da shi, shi ne ya banbanta shi da ita!, hancinta sharp nose take da shi, ga yawan eyebrows very thick dark brown.

Yana picking kuka ta saka mashi cikin shagwaɓa har sai da tasa Zash da Smart suka juyo da kallonsu a kan Bobo ɗin. Shiru ya ɗan zuba mata ido yana kallan yadda take kukan, kamar wacce aka sanya dole ta yi kuka. A tausashe sosai ya ce. "Pinkish lafiya kike kuka?".
Chapter 198 · 0% Book details