← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 242

Sashe 26

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Call É—in farkon ne ya katse na biyu ya sake shiga, Sharifat tana rike da hannunta É—aya, call É—in yana gab da katsewa ta sanya babban yatsarta zata É—auka.

Kamar daga sama aka bugeta ɗaya daga cikin jami'an da suka yi masu zobe, jama'a ne suka ture shi by mistake ya yi baya baya, to da yake ita da Sharifat ce a kusa da shi sai ya bugeta, ta ɗan yi baya ta bugi Sharifat wayar hannun nata ya faɗi ƙasa.

Ina cikin cunkosan jama'ar nan ba ta yadda za'ayi ta tsugunna dan ta É—auki wayar, tashin hankali iya tashin hankali ta shiga, ta rasa ya zatayi, ga shi wannan É—auka call É—in da zata yi shi ne aiki na karshe da zata yi wa masu nikaf a shirmenta wai sai su bata babanta.

Sosai ta shiga tashin hankalin da har bata san lokacin da hawaye suka fara wanke mata fuska ba.

A tunanin Sharifat saboda tashin hankalin da suka shiga a yanzu ne yasa take kuka, dan haka sai ta shiga bata hakuri tana gaya mata babu abin da zai samesu lafiya lou zasu koma gida.

Ina ai ita tasan me take tunawa, cigaba da kukanta kawai ta rinƙa yi tana jin zuciyarta tana yi mata zafi.

A haka aka fita dasu ta baya, babban tashin hankalinta na biyu bata taho da wayar ba, a tunaninta ta ina zata yi magana da masu nikaf ta ji ta gama aikin ne ko da saura?.

Tun da suka dawo gida take kuka ta ki ta yi shiru, Sharifat ta yi lallashi har ta gaji amma ina taki ta yi shiru.

Dan dole Sharifat ta rabu da ita ta je ta yi wanka tare da zuwa ta shirya cikin female arabs jallabiya, ta yi kyau sosai.

Wayarta ta zo ta É—auka domin ta kira number yayanta, dan hankalinta yaki kwanciya ganin ba'a tare da shi suka dawo ba, ta shiga damuwa sosai, dan dai kawai ba yadda zata yi ne.

Numbersa ta shigar ta fara kira. Wayar ta yi ringing har ta katse ba'a É—auka ba, Leesharh na kwance saman gado har lokacin tana murzan kukanta.

5 miss calls Sharifat ta yi wa Ramish amma bai ɗaga ba, hakan ba ƙaramin ɗaga mata hankali ya yi ba, dik sai ta ji kanta yana jujjuya mata, addu'a ta fara yi Allah Ubangiji yasa yana lafiya.

Miƙewa ta yi ta shiga toilet, alwala ta ɗauro tare da zuwa ta shinfiɗa dadduma, sallar mangariba ta gabatar tare da nafilfili ta shiga yi mashi domin Allah ya kare mata shi, wlh Sharrifat tana kaunar Ramish sosai.

Addu'oi sosai ta rinƙa yi mashi a cikin sujjada. Ta ɗauki almost 4 hours a saman dadduma tana karatu da addu'oi bayan idar da sallah isha'i da ta yi, har kwallah sai da ta yi mashi!.

Abin ya yi matuƙar ɗaga mata hankali.

Daga karshe bayan ta kammala ne ta miƙe ta dawo wajen gadon, a lokacin Leesharh ta dai'na kuka sai ajiyar zuciya take saukewa.

Wayarta Sharifat ta É—auka, number Abbie ta kira. Bugu É—aya ya É—auka. Kamar zata yi kuka ta ce.

"Abbie kana gida ne?".

Abu Abdussalam dake kishingiÉ—e a saman wani shinfiÉ—a tasa ta alfarma mai kama da shinfiÉ—ar sarakuna a cikin rest part É—insa ne ya amsa mata da yana gida kuma yana wajen hutawarsa.

"To Abbie gani nan zuwa".

Da okey ya amsa mata. Katse kiran ta yi tare da fara matsawa Leesharh a kan ta tashi zu je wajen Abbie.

Har da ce mata. "Tin da ni kin ki ki ji rarrashina zaki ji na Abbie ai, sarkin tsoro kawai, ke daga jin anyi harbi da bullet zaki wani fara kuka! A haka kuma zaki auri Yah Bilal kenan?".

Allah sarki Sharifat har ta bani tausayi, bata san cewa ba wannan ne a gaban Leesharh ba, hmmm wanna shi ne Sharifat tana goya yar kunama.

"Ni Sharifat ki tafi kawai babu in da zan je". Da kyar voice É—inta yake fita saboda kuka.

"Allah babu in da zan je ba tare da ke ba, kawai ki tashi mu tafi".

Make kafaÉ—a ta yi haÉ—e da tirjewa ita lallai ba zata je ba. Matsa mata Sharrifat ta cigaba da yi dan ba zata iya ganinta a cikin damuwa ta kyaleta ba.

Hannu ta kai ta riƙo hannunta tana ƙoƙarin janta ta mikar da ita tsaye dan dole.

Cikin ɗaga murya Leesharh da ranta ya gama ɓaci ta ce.
"Ki sakeni babu in da zanje nace maki! Wai ana dole ne?!"

Sam Leesharh bata san ta daka mata tsawa haka ba, ranta ne ya kai ƙololuwa wajen ɓaci.

Zaro idanu Sharifat ta yi ba tare da ta saketa É—in ba, nan take kuma sai ta ji zuciyarta ya tsorata da Leesharh, a take ta fara tunanin anya kukan tsoro Leesharh take yi kuwa? Anya babu wani abin a kasa kuwa? Kukan ne ya wuci na hankali yanzu kam.

Ganin Sharifat ta zaro idanu ne yasa ta fahimci abin da ta aikata, dan haka sai ta yi kasa da kantah haɗe da riƙo hannayen sharifat cikin nata.

"Ki yi hakuri sister, ban san na yi hakan ba".

Kamar wadda aka sanyawa battery Sharifat ta ce. "Leesharh kukan me kike yi?".............. Ta yi maganar idanunta a kan Leesharh babu ko kyaftawa!.

Nan fa Leesharh ta fara zazzare ido tana Æ´an kame kame, ta rasa me zata ce, ita da kanta tana neman tonawa kanta asiri.

"Am....... Ba........... Ba........ Babu komai". Ta faÉ—a murya a sarke.

"Tun da ni ba zaki faÉ—a mun ba tashi mu je wajen Abbie sai ki faÉ—a mashi". Cewar Sharifat.

Jinjina kai ta yi kafin ta amsa da. "Okey bari in yi wanka sai mu je".

Kamar zata ce mata su je kawai, sai kuma ta ce bari ta kyaleta ta yi wankan zai fi.

Toilet ta miƙe ta shiga dan ta yi wanka. Sharifat ta zauna a bakin bed tana jiran fitowarta.

A bakin wash hand base ta tsaya tana kallon kanta a cikin mirror, Allah sarki har idanunta sun kumbura saboda kuka, haƙiƙa Leesharh tana cikin tsaka mai wuya baiwar Allah, daga gidan yari ta wuce wannan ukubar kuma, Allah dai ya bata ikon cin jarabawarta.

Ta jima sosai tsaye tana kallon kanta kafin daga bisani ta wuce wajen haɗa ruwan wanka, dik jikinta a mace kamar anzare mata laƙa.

Sharifat na zaune tana ta istigifari tana rokan Allah da yasa Ramish É—inta yana nan lafiya, har Leesharh ta fito É—aure da towel ta sameta.

"Kisaka irin jallabiyata mu yi iri É—aya Abbie zai ji daÉ—in hakan". Cewar Sharifat, ta yi maganar dai'dai lokacin da Leesharh zata shiga dressing room É—insu dan shiryawa.

Jinjina kai ta yi haÉ—e da amsawa da okey sannan ta sa kai ta wuce.

In short a shirye Leesharh ta fito cikin kaya irin na Sharifat, tin bata karisa in da Sharifat take ba ta miƙe ta nufeta.

Hannunta ta rike suka nufi waje. Kai tsaye wajen Abu Abdussalam suka nufa.

Yana kishingiÉ—e saman shinfiÉ—ar ga kayan marmari a gabansa, yana sanye da white arabs jallabiya, dattijon arziki kenan.

Yana ganinsu ya miƙe zaune, a saman shinfiɗar suka zauna, Leesharh ta gefen damarsa Sharifat ta gefen hagunsa.

Sharifat tana rike da wayarta irin na Leesharh a hannunta.

"Barka da dare Abbie". Sharifat ta faÉ—a.

Bai kai ga amsawa ba Leesharh ma ta faÉ—i hakan. Cikin muryar dattaku ya ce.
"Yauwa Æ´aÆ´ana.............. Leesharh menene ya sami idanunki?"

Kasa ta yi da kai tana ƙoƙarin fara ƴan kame kame.

"Abbie tin daga wajen taron nan da taga anyi harbi ta fara kuka, nayi ta rarrashinta ina faÉ—a mata babu abin da zai sameta amma taki yin shiru har sai da muka dawo gida".

Tin da Sharifat ta fara magana kallonsa yake a kanta har ta dire, sannan ya dawo da kallonsa a kan Leesharh.

Yana ƙoƙarin buɗe baki ya yi maganar Ramish ya shigo wajen bakinsa a ɗauke da sallama.

A miliyan Sharifat ta kai kallonta a kansa, shi kuwa hankalinsa sam baya a kansu, yana sanye da sleeping dress riga da wando milk color masu bala'in kyau, ya yi kyau sosai, dik da bashi da fara'a kullum fuska a ɗaure, amma da kallo ɗaya zaka yi mashi ka fahimci yana cikin damuwa, ya ƙara tsuke fuskarsa sosai, ya haɗe gerar kasa da ta sama.

Saman sofas dake wajen ya zauna, sai wani kara tsare gida yake yi yana cin magani.

Wani irin mummunar razanannen faÉ—uwar gaba Leesharh ta ji a lokacin da ta É—aura idanunta a kan wayar dake hannunsa, tabbas wayarta ce da masu nikaf suka bata, to ya aka yi wayar ta zo hannunsa?. Ta jefawa kanta tambayar.

Dakatawa da yiwa Leesharh magana Abu Abdussalam ya yi tare da mayar da kallonsa a kan Ramish.

"My son ka dawo?".
Cike da ƙaguwa da san jin amsar da Ramish zai bashi ya yi tambayar, cike kuma da tsananin fargabar abin da zai ji.

Jinjina kai Ramish ya yi ba tare da ya yi magana ba.

"To meyafaru and kiran me suka yi maka?". Cewar Abu Abdussalam.
Ya jefa mashi tambaya cike da damuwa, dama tun É—azun Ramish ya dawo daga wajen taron suna tattaunawa da Abbie É—in nasu, yanzu ba jimawa jami'ansa suka kirasa a waya shi ne ya tashi ya tafi, ya ce da Abbie yana zuwa yanzun nan, dawowarsa kenan.

Wayar Leesharh dake a hannunsa ya miƙewa Abu Abdussalam.

Karɓa Abbie ya yi yana jiran a kora mashi bayani, shiru Ramish bai yi magana ba, kamar wanda baya san motsa lips ɗinsa, ya yi kasa da kai kamar mai tinanin wani abin.

Gajiya da ƙaguwa da Abbie ya yi da san jin bayani ne yasa ya ce. "My son meyake faruwa ne?".

Shiru Ramish ya kara yi har na tsawon good 2 mins.

Sai kallansa Leesharh take sata kirjinta na dukan uku uku, ji take yi tamkar zata mutu, gabanta sai mummunar faÉ—uwa yake yi, alamar rashin gaskiya ne karara ya bayyana a saman face É—inta, har wani zufa take ji yana keto mata.

Ita ma Sharifat sai satar kallonsa take amma ita kallon soyayya take yi mashi ba ta wata manufa ba, dan ma dai tasan baya san yawan kallo ne yasa take kallonsa a sace, da a sarari zata gansa.
Chapter 26 · 0% Book details