← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 242

Sashe 64

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ina wayata take?". Ta gefa mashi tambaya.
Shiru ya ɗan yi, yana tinanin a ina wayar take, shiga tashin hankalin da ya yi a sanadiyar ɓatarta ya ja ya mance ina ma wayar tata yake.

Ganin yana tinani yasa ta fahimci ya ajiye wayar a in da ya manta ne, dan haka sai ta kawar da zancen da cewa. "Hoorain ina san ka mun wata alfarma guda É—aya kafin mu koma gida".

A kanta ya tsayar da idanunsa, sannan ya É—an jinjina mata kai kafin ya amsa da. "Wace alfarma kenan gimbiya?".

"Ina san idan ba damuwa dan Allah ka bari in kalli face ɗinka ko da sau ɗaya ne a rayuwata kafin mu koma gida, ina san kallanka sosai"............ Shiru ya ɗan yi lallai Zunaira ta zo da babbar magana, ga shi a wannan gaɓa ba zai iya yi mata gardama ba, saboda ta kuresa a yanzu, alfarma ta nema wanda ta wuci hakan a wajensa, innalilahi wa inna ilahir rajiun, shi ya zai yi yanzu? Tun yana ɗan shekara bakwai ya fara sanya hulunan yaki yana rufe face ɗinsa, kunga kuwa tin ba'a san za'a haifeta ba kenan, babu wanda ya taɓa matsuwa da ya ga face ɗinsa sai ita, dan haka bashi da kwarin gwiwar kallanta ya ce ba zai iya yi mata wannan alfarma ba, ransa dai bai so ba, amma ya zai yi tin da farincikinta yake so!.

"In Sha Allah ba zamu bar cikin wannan daji ba har sai kin kalli face É—ina ranki ya daÉ—e, na yi maki alkawari, amma ba yanzu ba dan Allah, kin ji ko?".

Jinjina mashi kai ta yi alamar to, sannan ta ce. "Ina Abbo?".

"Yana gida na barosa"....... Shiru suka É—an yi kamar babu mutane a wajen.

"Hoorain". Ta ambaci sunansa a hankali. Ba tare da ya dawo da kallonsa a kanta ba ya amsa mata da na'am.

"Meyasa baka san kallona kai tsaye sai dai ka rinƙa satar kallona kamar wanda bashi da gaskiya?".
Ba tare da ya juyo da kallan nasa a kanta ba ya ce.
"Saboda in kina tare da ni bana iya É—aukar minti É—aya ba tare da na ganki ba, ba zan iya zuba maki ido in yi ta kallanki kai tsaye ba kamar yadda ba zan iya daure ban kalleki ba, shiyasa nike kallanki a sace".

Haka kawai baiwar Allah ta ji murmushi ya kubce mata, wato shi baya shakkar faÉ—ar gaskiya fa, bawan Allah. Sosai ya ji daÉ—i harda sauke nannauyar ajiyar zuciya lokacin da ya kalli ta yi murmushi, har ya ji ransa ta sanyaya sosai.

"Meyafaru kake sauke ajiyar zuciya?". Ta jefa mashi tambaya.
"Saboda kin yi murmushi shiyasa na ji sanyi a rai'na, ban ma san na sauke ajiyar zuciya ba sai da kika yi magana".

Allah sarki zuciyar masoya, sai ta ji wani irin daÉ—i ya kara ratsata, har tana ji kamar ta kasance da shi a cikin wannan yanayi a wannan waje na har abada, ita jin daÉ—i da daular da suke da shi ba shi ne a gabanta ba, Hoorain shi ne kawai damuwarta, in dai zasu zauna cikin wannan yanayi mai daÉ—i yana ganinta tana ganin shi to ta gwammaci zama a wannan daji fiye da ta koma wajen Æ´an uwanta.

Wato soyayya fa hegiyar aba ce, ko da yake ayoyi sukutum ne da ita a cikin Alqur'ani mai girma, dan haka zata yi fin hakan ma in dai so ce, Allah dai ya taimakemu kada ya bamu damar san waÉ—an da basa sanmu, Allah ya haÉ—amu da masu sanmu na gaskiya!!.

••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

Sun jima a wannan waje suna hira, tun yana amsa mata kai tsaye har ya dawo binta da okey da kuma e or a'a, dan shi bashi da yawan magana, sai jansa da hira suke yi, dan yanzu Pretty ma ya ware ta fara tayata.

Sai da rana ya tsaga ne ya ce masu su zo su koma wajen da ya tanada masu bari ya nemo masu abin da zasu ci. Basu yi mashi musu ba, suka miƙe da kyar Auta tana jan kafafunta a ƙasa.

"Ranki ya daÉ—e ina neman wata alfarma". Ya faÉ—a yana kallan Æ´an fararen kafafunta.

Jinjina kai ta yi. "Ina jinka". "Dan Allah ki bani damar in É—aukeki zuwa wajen". "Meyasa?". Ta sake jefa mashi tambaya. "Saboda bana san ganin kina shan wahala".

Wani irin daÉ—i ta ji ya ziyarceta a ranta, tabbas bata cire ran Hoorain zai sota ya kuma bayyana mata soyayyarsa ba a yanzu.

Jinjina mashi kai ta yi alamar ta bashi dama, ai tin kafin ta gama zayyana ta bashi damar ya É—auketa cak sai saman kirjinsa na zakunan mazajen nan, ya riko hannun Pretty suka kutsa cikin dajin, suka koma in da suka fito, wato wajen da ya gyara ya tanada dominta, waje mai cike da yanayin soyayya da nishaÉ—i.

•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

A ɓangare guda kuwa, Sadauki kusan hauka ya yi a lokacin da ya kawo masu ziyara bai samesu a wajen ba, yau a karon farko sai da ya durkushe gwiwowinsa a ƙasa, dik da ba'a iya ganin face ɗinsa sai idanu, yau sai da tashin hankali ta bayyana acikin idanun nasa mai firgitarwa.

Cike da tashin hankali da damuwa ya fara kewaye arear wajen yana nenan ta ina zai gansu? Damuwarsa ma yadda Auta take da ciwo a ciki bata warke ba, hakan ta kara É—aga mashi hankali sosai, jikinsa har kerma yake yi yana tsuma. Ya É—auki a kallah mintuna 30 yana kewaye a yankin yana nemansu, dan gani yake suna nan a wajen basu yi nisa ba.

Wani irin damuwa ya ƙara shiga a lokacin da ya yardanwa kansa basu nan, basu wannan yankin kwata kwanta sun yi nisan zango, ga shi babu wata makama da ya gani wanda zai iya hasashen meyafaru da su? Innalilahi wa inna ilahir rajiun, shi ne kawai kalaman da yake ta maimaitawa, ya shiga damuwa na wuce misali.

Da kyar ya iya jan kafafunsa ya kutsa cikin dajin da ya je ya cigaba da nemansu a can ko Allah zai sa ya gansu.

•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

After some minutes, rana ta take sosai, zaune Pretty da Auta suke a saman dutse kusa da wata bishiyar gwaiva, hannunsu rike da ganyen ayaba mai É—an faÉ—i, gasassun kifi ne a saman ganyen ayabar wanda Hoorain ya kawo masu, ga kayan fruits a gefensu, basu san daga ina ya samo kifin ba, su dai ya ce masu su yi zaman jiransa yana zuwa, shi ne ya dawo masu da kifi gasassu kuma ya sake tafiya ya barsu ya ce yana zuwa.

Sai rarraba idanu Auta take yi tana jiran taga ta ina zai ɓullo, ta gaji da jiransa, dik bayan second ɗaya kara ɗaukin san ganinsa take yi, bata gajiya da shi, a kullum tana san taga tana a tare da shi.

Ita kuwa Pretty tinanin kifin kawai take yi, kunsanta ita da ci akwai amana, sai tinanin kifin take yi, ya bata sha'awa, ta yi mamakin ganin irin gashin da ya yi masu, tana da yakinin a wajen wancan wuta da ya kunna mata dan jin É—umi É—azun nan ya gasa masu, ya kamo kifin a kogi kenan ya gasa a can.

Gajiya da gafara sa bataga kaho ba Auta ta yi, dan haka sai ta miƙe tsaye, a hankali ta ce. "Pretty zauna ki jirani ina zuwa".

"Ina zaki je ki barni?". Ta jefa mata tambaya.............. "Ke dai ba zan yi nisa ba kuma ba zan wani jimaba, ina zuwa yanzu".

Jinjina kai Pretty ta yi tana cigaba da gutsirar kifinta tana kaiwa baki abinta sarkin ci kawai, har yanzu dai bata canza hali ba a fagen ci.

Saukowa kasan dutsen Auta ta yi, sannan ta miƙi hanyar da take tinanin yana ta wajen. Tana tafiya tamkar mai tsoron taka ƙasa, saboda ciwonta idan ta yi sauri zai fama. Tafiya a hankalin yasa bai ji zuwanta ba, yana tsaye saman dutsen dake gaban wannan koramar, yana ƙarisa wanke takobinsa da bai samu ya yi ɗazun ba.

•••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

Tin da ta doso wajen ta hangosa daga nesa tsaye saman dutse, gabanta ne ya yi wani irin faɗuwa sosai, kirjinta ya bada dukan uku uku, bata san time da ta ɗaga kafarta da sauri wajen ƙarisawa garesa ba. Sam bai ji alamarta ba, ya bawa hanyar da take zuwa kuma baya yana karisa wanke wanke takobinsa da bai ƙarisa ɗazun ba. Ya kuma ɗauro alwala dan ya yi sallah.

A wani irin slow ta ambaci sunan cike da salon da bata san ta iya shi ba. "Hooooooooooraiiiiiiiiiiiiin" haka ta faÉ—i sunan.

Da karfi ya juyo domin ya ji abin ne kamar almara, kamar voice É—inta kamar kuma ba nata ba, sai ya ji kamar mafarki kamar kuma gizo, hakan yasa ya yi saurin juyowa da karfi.

Juyowa da ya yi da karfi yasa kyakkyawar dark black curly hairnsa ya watse kamar wata mace kamar kuma wanda aka hurawa gashin iska ya watse haka.

Ya ilahi ya lilliahi! Mutuwar tsaye ta yi tana kallansa, kamar wadda aka zarewa rai, ta kame kam. Shi kuwa cikin zafa ya diro ƙasa daga saman dutsen, da wani irin gudun gaske ya nufota. Zaro idanunta ta yi tana mamakin me zai yi mata da ya nufota da irin wannan uban gudun kuma? Ga lafiyayyar takobinsa a hannunsa.

Ku me kuke tinanin zai faru? Yau dai ta ganshi babu hular yaki, ko ya kamanninsa take? Meyasa ya nufeta da gudu dan ta gansa bai rufe fuska ba, meyasa ta yi sumar tsaye dan ta gansa? To ni dai bari in leƙa Black world muga me suke ciki kafin in dawo muga me zai yi mata kuma mu ga ya kamanninsa yake da yake ɓoyewa tsawon shekaru, yau dai komai ta bayyana..........🥱

••••••••••••••BLACK WORLD•••••••••••••🔥

A wani irin razane Ronnie ya juyo da kallonsa a kan yayan nasa. Wani irin razana ya yi ganin yadda Black Tiger ya É—aure fuska tamau alamar babu tausayi babu imani.

Nan take wasu irin zufa suka fara keto wa Ronnie babu kakkautawa, shikenan yau Sweetie ta ja mashi yanka kazar wahala, watar azabarsu ce ta tsaya.
Chapter 64 · 0% Book details