← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 242

Sashe 9

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɗago kai Sweetie ta yi da nufin ta bata amsa unexpect idanunta suka sauka cikin nashi. Girgiza mata kai ya yi a kan kada ta faɗawa Floris yadda aka yi da kuma yadda yayansa yake, ya ɗaura yatsarsa ɗaya a saman lips ɗinsa alamar ta yi shiru, hakan yasa ta mayar da kanta ƙasa ta rasa abin cewa, ita ga shi ba karya ta iya yi ba.

"Sweetie ki amsa mun mana". Cike da ƙaguwar son jin amsa Floris ta sake tamnayarta.

Hakan yasa Ronnie ya katsesu da cewa. "Let's go beb".
Ya yi maganar tare da miƙawa Floris hannu a kan ta tashi su tafi.

Miƙa mashi hannu ta yi ya kamata ta miƙe tsaye, tana matuƙar son ta ji amsa amma ya hanata ta hanyar janta suka nufi waje yana yi wa Sweetie bye bye haɗe da ce mata kada ta kuskura ta fita waje, ta zauna a ɗaki by 7 zasu dawo.

Da okey kawai ta bisu har suka fice, gyarawa ta yi ta kwanta tana tunanin rayuwa haÉ—e da masoyinta Kamran, true love never end, har yau har gobe soyayyar Kamran yana ranta, soyayyar gaskiya take yi mashi, ga shi bata san kamanninsa ba, a haka dai take balai'n kaunarsa, shi kuma kada ku manta soyayyar a mutu yake yi wa Pretty, dan tun faÉ—owarta duniya sonta ya dasu a ransa, ko yaya wannan abin zai kasance? Mu je dai zuwa.

===========🔥💘============

IDAN MUKA WAIWAIYA FRANCE KUWA.

SMART🔥🕊️

Tsulundun yake tsundume a cikin jacuzzi cikin toilet ɗinsa, har saman lion chest ɗinsa ruwan take, haɗaɗɗen kunfa fari tas ne cike a cikin jacuzzin, hakan ya hana damar ganin tsiraicinsa, ya jiƙa haɗaɗɗen dark black hairnsa da ruwa, hakan yasa gashin ya kwanto mashi rabi a gefe gefen face ɗinsa, rabi kuma a bayan wuyarsa, face ɗinsa gabaɗaya a jike yake da ruwa, zara zara eyelashes ɗinsa suna jike, hakan ya bada damar kyansa ya kara bayyana sosai.

Tinanika kala kala ne cike a cikin ransa, wani irin binciken kwakkwafi a kan wani technology da zata ciyar da duniya gaba yake yi, a part from duniyar wata da yake shirin zuwa yana nan yana wata aiki ma dan kara bunƙasa kimiya.

So yake ya leƙa duniyar karkashin ruwa bayan idan ya dawo daga duniyar wata, ya sa ana shirya kashi nautilus, wato wani katafaren jirgin ruwa ne wanda zai kai ka karkashin teku cikin kwanciyar hankali, yana dawowa daga duniyar wata yake son afkawa can, burinsa a kullum ya kawo wata kimiya da zata tashi kan duniya, ga shi da bala'in iya zurfafa tunaninsa a kan dik wata aiki da yasa a gaba, ga dogaro ga Allah hakan yasa yake yin nasara a dikkan lamuransa, dayawan masu fikira daga wajensa suke samun fasaha, nutsuwarsa da bin komai daki daki shi ke kara bawa mutane mamaki, jan ajinsa da halin ko in kulansa, bai ɗauki komai matsayin wani abin a zo a gani ba, wasa da makaman kare dangi kamar mai wasa da dunkulen wasa yakan ɗaga hankulan jama'a matuƙa, musamman wasa da rocket da yake yi, yana ɗaga hankulan makusantansa, saboda suna tsoron rasashi, shi kuwa lafiya lou yake komai ɗinsa.

Ya ɗaga kai sama idanunsa a lumshe, da alama ba ƙaramin daɗin ruwan yake ji ba, kuma ga dikkan alamu tunaninsa da yake faɗaɗawa tana tafiya mashi yadda ya dace duba da yadda ta nutsu ya nutsa cikin tunanin nasa.

While ita kuma mom suna can gym ita da dad suna motsa jiki, mom tana bawa furenta ruwa, kun san ta kware a wannan harkar, wajen gym É—in gabaÉ—aya kewaye yake da tsaro na ban mamaki, amma hakan bai hana mom soyewanta da É—an dattijon mijinta ba. Su fa sam basa tsufanwa soyayya.

A hankali ya waro idanunsa jin alamar shigowar mutum cikin room É—insa. Kamar wanda baya son motsawa ya juya idanunsa izuwa saman katafaren Tv dake manne da jikin bango a cikin toilet É—in.

Heleena ce tsaye a tsakiyar room É—in nasa tana bin ko'ina da kallo, ta kwana biyu rabonta da ta shigo cikin É—akin, yanzu ma sai da ta je ta taso dad a gaba tasa ya yi amfani da laptop É—insa ya cire mata door securityn sannan ta shigo.

Tana nan dai cikin wannan É—an iskan shigar tata, sai dai yau abin ta taazzara, dan fa cibiya a waje ne yau, ga wasu Æ´an iskan breast É—inta kamar............ Bari na raga mata kada nan gaba kaÉ—an ta zama matar Smart in shiga uku.

Yau wandon ma tsabar iskanci bai kai kaurin kafafunta kamar na Nennen Mahreen É—in nan ba, hannunta na É—auke da tray mai shake da small chop, ita dai ta dage sai ta kawowa Smart small chop É—in nan, anya ma ba wani abin ta banka a ciki ba kuwa?

Baiwar Allah bata san ma kyamarta yake ji kamar ya yi amai idan ya ganta ba, ta bi ta matsawa kanta a kan son shi da son kyatata mashi, ina ga sai mun taimaka mata da tsayuwar dare kila ta dace, matsalar dai taki musulunta ne ita da mom.

Ji ya yi tamkar zai yi amai na ganinta da ya yi, ko bai tambaya ba yasan dad ne ya buÉ—e mata door É—in nan, to ya zai yi da dattijon nasa? Ai sai hakuri kawai.

A hanzarce ya kawar da kallonsa daga kanta tare da mayar da idanunsa ya lumshe su, cikin ransa ya fara tunani wanda shi kaÉ—ai ya barwa kansa damar sanin me yake tunawa.

Kamar wanda yake mafarki ya furta. "Am coming for it soon". Ya yi maganar tare da sauke ajiyar zuciya.

A hankali ya miƙe tsaye tare da zuro kyawawan kafafunsa kasa, ya fito daga cikin ruwa ya nufi ɓangaren towels dake shirye cikin show glass tamkar shop na sayar da su ne.

Wata fara kal ya É—auko mai É—an girma wadda ta tsaya mashi dai'dai kaurinsa, sannan ya É—auki wata mai É—an girma ya nannaÉ—o hair É—insa a ciki domin tsane ruwan. Gaban wash hand base ya nufa. Tsayuwa ya yi a wajen tare da kurawa kansa kallo a jikin mirror dake wajen.

Kamar wanda bai san ya face É—insa take ba haka ya kafe kansa da waÉ—an nan idanun nasa.

Ya É—an É—auki lokaci a wajen kafin ya nufi fita waje, shi da kansa yasan shi É—in smart ne na gasken gaske, gifted ba.

Jin motsin fitowarsa daga cikin toilet É—in yasa Heleena yin saurin ajiye mashi tray dake hannunta ta juya da sauri, har da haÉ—awa da É—an gudu ko É—ar bata ji ba na wannan uban high heel dake kafanta, tana son sanya shi a idanunta amma tafi jin tsoron haÉ—uwa da shi sama son kallonsa da take, dan a kullum hata kyau, ita ake bari da dakon danasani in suka haÉ—u.

Sarai ya ga fitarta, amma ko a karkashin sillpers É—insa ya wuce izuwa dressing room. Jim kaÉ—an ya fito shirye cikin tsadaddiyar jogger a jikinsa ta kasa, ta sama kuma round neck polo shirt ce, dikka white colors ne.

Hanunsa na É—aure da wata dankareriyar Rolex-pnd wanda a kalla kuÉ—insa ya kai 18 million dollars. Sai tashin kamshin perfume É—in Mf yake yi, wanda kuÉ—in wanna perfume É—in ya wuci tunaninku.

Wayarsa ya É—auka ya nufi waje a gaggauce, ko kallan abin da Heleena ta kawo bai yi ba, ya fice.

Kamar dai yadda dad ya saba saka mashi takunkumi na idan zai fita sai da tsaro gaba tsaro baya, hakance ta kasance, da ya ce wa dad shi fa yanzu ba yaro bane dan Allah su kyalesa ya shakata, shi jarumi ne ba rago ba.

Da sauri mom ta karɓi zancen da cewa shi yaro ne kuma dole ta saka idanu a kansa.

Ni dai nace mom bata san dik saka idanunta a kansa na banza bane, domin kuwa shi da dad dai sun mata wayo, sun gwada mata kwarewa suna can bayan fage suna sharholiyarsu da rocket.

Kamar zai yi masu gardama, amma farincikinsu shi ne nasa, dan haka ya raba masu sumbatar kauna a kumatu tare da wucewa ya nufi jerin gwanon motocin da aka jera domin shi.

Sai dai kamar kullum gidansa ya je ya baro securitys É—in ya É—auki tsadaddiyar motarsa ya wuce World É—insa, wato duniyarsa, dan yana bala'in kaunar wannan rocket factoryn nan nasa fiye da komai, nan ne duniyarsa, yana alfahari da baiwa da ilimin da god ya bashi.

Yau ta kama saturday ne, garin ya yi shiru sosai, kowa yana makale a gida, ga wani uban sanyi dake zuba kamar ana watso dissa, a haka kuma bai sanya jacket a gida ba sai da ya je gidansa ya É—auki wani katan puffer jacket ya sanya.

Weekend ba aiki ba zuwa office, kowa yana cikin gida, su kuma a yau ne suke gwada lunching manya manyan makamansu da suka É—auki tsawon watanni suna haÉ—asu, sun yi aiki tukuru domin tabbatar da ingancin dik abin da zasu haÉ—a, sun sadaukar da lokutansu ba dare ba rana suna aiki, fatan komai ya dai'daita yadda suka tsara kawai suke yi.

A lokacin da ya isa world É—in nasa har an gama shirya komai na tashin makamin, shi kaÉ—ai ake jira da ya zo ya saita in da zata nufa ya saketa, shararren makami ne wanda ya É—ara bmt-59 a girma, a kullum burin Smart ya kirkiran wasu makaman da babu masu kwatankwacin haÉ—arinsu a duniya, ya zamana su ne na farko da zasu mallakesa, to yanzu ya yi nasarar kirkiran kala É—aya wanda ya sha wahala wajen kirkirota, ya kuma É—auki tsawon watanni, yana fatan yanzu idan ya gwadata ta tafi yadda yake so.

Babban yaronsa a wajen mai suna Robbert ne ya fara isowa garesa ya tarbesa domin sanyaya mashi ransa. A tare suka ranƙaya izuwa room na GUIDANCE SYSTEMS COMPUTER'S.

Wato É—aki ne mai cike da na'urorin controlling na nuclears É—in da suke kyarawa, wasu irin mahaukatan systems ne masu ban mamaki, masu aiki babu kama hannun yaro, babu batun sanyin battery ko tsufa, dik bayan kwana uku ake zubo sabbi saboda tsaro, dan kuskure kaÉ—an idanun suka yi an shiga É—ari ba uku ba, so suna da karfin aiki fiye da tunaninku, dan ba kamar sauran systems da kuka sani bane.

Gaban wani dankararen guidance system computer ya tsaya.
Chapter 9 · 0% Book details