← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 242

Sashe 127

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cigaba da magana cikin bada umarni King ya yi yana mai kara kausasa murya. "Daga rana irinta yau ko parlourn nan na haramtawa Zunaira fita, zata kasance ne a cikin ɗakin mahaifiyarta, dakin takalma ban yafe ta yi domin fitowa waje ba, sannan na taraku a nan ne dan ku shaida na bawa Abdussalam aurenta, (Abdussalam ɗin Abu Abdussalam kenan) ko taki ko ta so shi ne mijinta, kuma ba zan jira wai sai ta girma ba, dan girma ya kare tin da har tasan ta je wajen Hoorain, har tasan tana san Hoorain, cikin ƙanƙanin lokaci za'ayi auren ya wuce da ita Dubai!!!!".

Da alama ran King ya kai ƙololuwa wajen ɓaci, dik cikin parlourn babu wanda bai tausayawa Auta ba, har momma ta ji tamkar tasa kuka, amma ta daure tana jin zafin hukuncin King a ranta, amma fa Mammie ta ji daɗin hakan, dan ita burinta ta gansu cikin kunci a kullum.

Ƙasa ɗaukarta kafafunta suka yi, durkushewa ƙasa ta yi a saman gwiwowinta a gaban King, tana kuka tamkar ranta zai fita, ta kasa yin magana sai kerma da jikinta yake yi, lokaci guda jikin nata ya ɗauki zafi raw kamar wuta, alamar zazzaɓi, kanta na sara mata da karfi karfi, tana san rokon King da ya yi hakuri ya yi mata afuwa amma ta kasa iya buɗan baki ta yi magana.

Lokacin guda wani irin lallausan kamshi ya daki hancin kowa dake cikin parlourn, gabaÉ—ayansu sai da suka shaki wannan kamshi suka lumashe idanu. A miliyan Auta ta kai kallanta a kan kofar shigowa cikin parlourn.

Da karfi ta furta. "Yah Omerish". Ta yi maganar ne ba tare da taga kowa a wajen ba, da alama kamshin perfume ɗinsa da ta ji ne ta furta sunansa. Lokaci guda gabaɗaya parlourn suka kai kallansu a kan kofar shigowa ganin taga wajen ta kuma furta sunan da basu taɓa jinsa ba.

A miliyan Sarina ta miƙe tsaye tana cigaba da kallan kofar shigowa tana shaƙar wannan daddaɗar kamshi da yake buga mata hanci.

Ruɗewa Auta ta yi ta fara ƙoƙarin nufar kofar fita. Tsawan da King ya daka mata ne yasa ta dakata cak kallanta a kan kofar shigowa.

A hankali aka turo kofar parlourn, Jaish ne ya sanyo kai kafin Smart namu na kasar France ya rufa mashi baya. Ihun sunansa da karfi Auta ta yi Yah Omerish sannan ta tafi da gudun gaske ta faÉ—a jikinsa tana sakin kuka mai sauti.

Gabaɗaya parlourn zaro idanu suka yi suna kallonsa. A miliyan momma ta miƙe tsaye tana dafe saitin zuciyarta dake mata barazanar tarwatsewa........... King kuwa, ya zaro idanu ya kalli Auta ya sake kallan Smart, saboda kaman dake a tsakaninsu, shi dai Auta kawai ya sani, to wanenne wannan mai kama da ita ɗin? Ya jefawa kansa tambayar cike da mamaki game da ƙaguwa da san jin wanene?.

Cikin wani irin murya a mai kama da marairacen murya momma ta furta. "Omerish meya kawoka nan? Meyasa ka zo? Meyasa baka sanar da ni zaka zo ba?".

A miliyan King ya dawo da kallonsa a kan Momma, ita ma Akka ta dawo da kallanta a kan momma, nan ta dikka family suka dawo da kallonsu a kan momma.

"Dama ni nasan tabbas a shekarun baya karya Rahilarh ta yi mana, a lokacin da wancan matsala ta faru tabbas nasan Rahilarh munafurtarmu ta yi". Cewar Mammie da ta gaza iya haÉ—iye abin da yake ranta.

Sarina kuwa, miƙewa tsaye ta yi kallanta a kan Smart da ya rungume Auta yana cigaba da goge mata hawaye yana kallan momma, shi bai bi ta kan King bama, dan bai ma san wanene King ba, iya momma da yaranta kawai ya sani, bayansu shi bai san kowa a cikin kingdom of power ba.

My people's me kuke tinanin ya kawo Smart kingdom of power? Me alaƙarsa da momma? Ya aka yi yasan su Jaish bai san su Ramish ba? Me ya faru a shekarun baya da suke ikirarin momma ta munafurcesu?. To dama na faɗa maku a week ɗin nan zaku sha surprises, taku dai har kullum Princess Teema queen of surprise!!.

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
======🔥🔥🔥===========

MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

34

"Omerish". King ya maimaita sunan kallansa a kan momma da ta miƙe tsaye tana zaro idanu. Lokacin guda ta fara kame kame alamar rashin gaskiya.

"Wani isasshe ya sanya Zunaira kuka a cikin gidan nan? Dama abin da kike ɓoye mun kenan momma? Yau tsawon 2 month kenan tin kafin na yi tafiya (duniyar wata) har na yi na dawo kullum idan na kiraki na ce ina Zunaira sai ki yi ta kauce mun, ashe zalintarta ake yi kika ɓoye mun? Shiyasa hankalina ya gasa kwanciya mana! Me ta yi maku kuma waye ya mareta a face ɗinta?!!" Cewar Smart, ya kai karshen maganar cikin kakkausar murya.

Gabaɗaya parlourn tsit suka yi an rasa mai bashi amsa, dan dik sai da suka sha jinin jikinsu ganin kwarjin dake face ɗinsa, an rasa mai tanka mashi, shi kansa Jaish shakkarsa yake yi dik da sun yi sabo matuƙa, amma yana shakkar wani ɗan abin da ya saɓa ya haɗasu.

Akwai wanda ya taɓa tina lokacin da Jaish yake yi wa su Omaid nasiha time da zasu koma school? Kun tina a cikin nasihar da yake yi masu ya ce in basu natsu sun mai da hankali a kan karatu ba zai mayar da su ƙasar Faransa! Kun tina wannan lokaci? To wajen Smart yake nufi kenan, baku ji su Omaid ɗin sun ce ya yi hakuri gara masu Yah Ramish a kan Faransa ba? Basa san zuwa wajen Smart dan ubansu zasu ci, sau biyu suka taɓa kai mashi ziraya kafin su dawo sai da suka haddace rabin Alqur'ani mai girma, suka natsu kaman wasu malaman da'awa, da suka koma Dubai sai suka watse...........😅

King dai kusan suman tsaye ya yi, saboda ganin abin yake yi tamkar a mafarki, ya aka yi Smart yake kama da Zunaira over haka?.

"Okey ba zaku iya faɗa mun wanda ya mari Zunaira ba sai ran kowa ya ɓaci ne?". Smart ya yi maganar cikin kakkausar murya again.

Tsit suka yi har lokacin an rasa mai iya tanka mashi, Sarina tini ta sha jinin jikinta, a tinaninta yadda Smart yake a hotonsa da ta sato daga É—akin momma haka yake a zahiri, sai taga ina, wannan da zafi sosai yake.

•••••••••••••••••••🔥

Uncle Abbas ne ya yi ta mazan miƙewa tsaye, cikin sanyin murya ya ce. "Mahaifinta ya hukuntata". Wani irin kallo ya jefi uncle Abbas da shi wanda yasa su Dr Raj zaro idanu waje, dan kallo ne mai kama da mugun kallo.

"Saboda shi mahaifinta ne sai aka ce ya zalinceta? Meta yi mashi? Shi yaga face É—in Zunaira ya yi kalar wanda za'a É—aura hannu da sunan duka a kai ne?". Yana magana yana bin uncle Abbas da mugun kallo.

Tashin hankali, zaro idanu gabaÉ—aya parlourn suka yi, barema ita momma da ta fi kowa shiga damuwa, dan kana ganinta zaka san tana cikin tashin hankali.

A karo na biyu uncle Abbas ya sake yin karfin halin cewa. "Mahaifinta fa nace maka ba wani ba, and wanenen ma kai da ka shigo mana cikin family without our permission?".

Shiru Smart ya yi na Æ´an sakanni kafin ya ce. "Then so what idan mahaifinta ne shi? Akwai in da aka bashi damar ya zalinceta ne?". Shiru gabaÉ—aya parlourn suka yi suna kallansa da mamaki, hankalin kowa a tashs, wai King yau ake cewa meyasa zai hukunta Zunaira? Tashin hankali lallai Smart ya zo da sabon alamari.

Uncle Abbas ne ya sake yunkurawa zai yi magana Smart ya É—aga mashi hannu cikin zafa alamar ya ja bakinsa ya yi mashi shiru a wajen. Cike da isa ya ce. "Bana san na sake jin ka bani amsa, babu wasu mutane a cikin parlourn ne sai kai?". Ya yi maganar yana mai da kallansa a kan King da ya rasa bakin magana kawai yana kallan momma.

Jaish ne ya ce. "Yah Omerish uncle Abbas ne fa, he's our second dad, why kake yi mashi magana haka?". .............. "So what idan kanin dad ne? Da shi na yi magana ne da zai rinƙa amsa mun?".

Zaro idanu Akka ta yi tana kallan Smart. (Akka taga wanda ya fita iya hau😅)

Shiru Jaish ya yi bai sake yin magana ba, dan shi yasan waye Smart. Akka ce ta katsesu da cewa. "Wanenen kai wai da ka shigo cikin family na kake neman tayar mana da hankali ka canza mana alkibla?". Ta faÉ—a tana É—aure fuska sosai. Dan ita ma Akka ta sha jinin jikinta ne yadda taga yake mugun kama da Auta, sai ta sha jinin jikinta.

Wani irin kallo ya bi Akka É—in da shi, shiru bai amsa mata ba, bashi ma da niyar amsa mata.

Mummyn Chuchu ce ta miƙe tsaye, cikin sanyin murya da magana cike da dattaku da sanyin word irin na uwa ta ce. "Ai kamannin dake face ɗinsa kawai ya isa ya baku amsar wanenen shi ba sai kun nemi ji daga bakinsa ba, babban yayanku ne mana, ku baku ga kamanninsa da Zunaira ba ne? Baku ga kamanin Rahilarh a face ɗinsu bane?".

Ai a miliyan su Dr Raj suka zaro idanu, a zabure mama ta miƙe tsaye, hankalinta a tashe sosai ta ce. "No........ Impossible!!, ta ya aka yi ya zama yayansu? Kin dai san bayan Ramish babu wani babba a gidan nan ai!".

Uncle Jahiz ne ya miƙe tsaye shi ma, a kan momma ya tsayar da kallonsa, a nitse ya ce. "Momma ki warware mana wanene shi, dan nasan ke kaɗai zaki bada wannan amsa mu fita cikin duhun ruɗani".
Chapter 127 · 0% Book details