← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 242

Sashe 11

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bappa ya rasa me zai ce mata, ya rasa da wasu kalamai zai yi amfani wajen shawo kanta, ya rasa me zai yi, ya zauna shiru ba zai iya jure kukanta ba, ya yi rarrashi kuma bashi da kalaman faÉ—e.

Sallamar da suka ji a tsakar gidan ne ya ja suka kai kallonsa bakin kofa shi da Mahreen.

"Kawu Ibrahim ka shi go mana". Cewar Mahreen.

Allah sarki, shi bappa da farko ma bai É—ago muryan mai sallamar ba, tsabar yana cikin damuwa, sai da ya ji Mahreen ta ce kawu Ibrahim ne ya gane.

Hannun Mahnoor ya riƙo tare da ce mata. "Zo muje".

Ba musu ta tashi ta bisa. Waje suka fito, Ibrahim kanin mamanta yana tsaye rike da wata sanda a hannunsa, ya yi shiru kamar mai tunanin wani abin. Idanunsa jajir kamar wuta.

"Jaɓɓama lale Ibrahim". Cewar bappa.

Da yauwa ya amsa idanunsa na a kan Mahnoor da dik fuskarta ya yi jajir kamar jan kosai saboda kuka, kun san farar fata idan tana kuka, har wani ja na musamman face É—in yake yi, bare ma wajen dogon hancin nan nata ya yi jajir sosai.

Matsowa ya yi ya karɓeta daga hannun bappa yana faɗin ta yi hakuri. Ɗan kwanciya ta yi a jikinsa tana ɓoye fuska, soyayyar Jaish ya ja ta manta da batun kunya har ta bari kukanta na rashinsa ya fito fili kowa ya gani, sai a yanzu dik ta ji kunya ya mamayeta. Sai ta wani ɓoye fuska a jikin kawu Ibrahim.

"Ibrahima lafiya kuwa?". Cewar bappa, ya yi tambayar ne bisa ganin kamar ran Ibrahim É—in a bace, ga idanunsa sun yi jajir sosai.

"Babu komai babbo, dama na zo kara tabbatar da abin da na ji kuma nasan dama zai iya faruwa ne, amma kukan Mahnoor ya riga da ya bani amsa".

Shiru bappa ya É—an yi dan bashi da abin sake cewa, Jaish ya jefa shi cikin matsala, ga yanayin al'adarsu yanzu zasu É—auki laifin dik su É—aura a kansa, bare dama ya hana Faisal ita, ai shikenan kuma ya kara shiga uku da dangi, sai kuma abin da Allah ya yi.

"Bobbo zan tafi da Mahnoor zuwa gida". Ya yi maganar ne rai a dakile, dan idan ransa ya kai miliyan wlh a yau ya ɓaci sosai, tin ainahi yana balain tausayawa Mahnoor baiwar Allah.

Bappa bai iya ce mashi ko uppan ba, dan bai san me zai ce mashi ba, kuma at this point bai isa ya ce zai hana shi tafiya da ita ba, shi kansa zai so a tafi da ita, su je Inna ta rarrasheta ko za'a samu ta yi shiru.

Ibrahim ya lura da cewa ɓacin ran da yake ciki sam ko rabin na bappa bai kai ba, dan ya lura bacin rai ya hana bappan yin magana. Dan haka sai ya ɗan sassauta ya danne nasa ɓacin ran ya ce. "Bobbo bari muje ko?".

Kai kawai bappa ya iya gyaÉ—a mashi ba tare da yin wani yunkuri ba. Jiki ba kwari Ibrahim ya ja hannunta suka nufi waje, sai binsu da kallo bappa yake yi. Da sauri Mahreen ta bi bayansu, dan kun san tana kaunar Æ´ar uwarta.

Suna tafiya bappa ya shige cikin É—akinsa, saman Æ´ar gadonsa ya hau ya kwanta, ya yi iya yinsa ya rufe idanunsa ko zai ji saukin abin da yake ji har barci ta yi awon gaba da shi, amma ina ya kasa, idanun ma sun ki rufuwa.

Kamar a mafarki ya hango suit ɗin Jaish da suka tsinto shi da shi makalle a jikin kusa ta bayan kofar shigowa, tun ranar da bappa ya cire mashi suit ɗin ya makala a wajen babu wanda ya taɓa taɓa shi.

A hanzarce ya miƙe zaune a saman gadon, tunani ya fara yi a kan watakila zai iya samun wani abin mai muhimmanci a cikin aljihun kayan, hakan yasa ya yi saurin miƙewa tsaye, da sauri ya diro kasa.

Kai tsaye kayan ya je ya ciro, a bakin gadon ya koma ya zauna, dik jikinsa a mace bawan Allah. Aljun kayan ya fara laluɓewa. Cikin sa'a ya fito da wallet a aljihun wandon.

ÆŠan kurawa wallet É—in ido ya yi kafin ya ajiye a gefe ya sake mayar da kallonsa a kan kayan.

A aljihun rigar ya ciro dalleliyar wayar Jaish, ya sha mamakin ganin wayar sosai, gata kamar sabuwa, bata ci screen ko ta lalace ba, sai dai bata kawo wuta, a kashe take.

A gefensu ya ajiye kusa da wallet ɗin ya cigaba da binciken aljihun, a nan ya samu passport, dama kun san da niyar yin tafiya Jaish ya bar gida, so ga passport ɗinsa da komai, amma ruwa ya jiƙasu har sun ɗan yayyege, sun kuma manne da juna babu halin bappa ya buɗe ya karanta.

Hakan yasa ya ajiye a gefe, cigaba da laluɓar aljihun ya yi har sai da ya tabbatar da babu wani abin da ya bari a ciki. Sannan ya ajiye kayan a gefe ya kai hannunsa ya ɗauko wallet da ya fitar da farko.

Da kyar ya iya ɓalle wallet ɗin ya buɗeta, sannan ya fara fito da abubuwan dake ciki, akwai takardarsa na ɗan kasa, ID cards da sauran muhimman cards.

Dik babu wanda bappa ya iya karantawa ya gane, saboda rubutun turanci ne a jikinsu, dibasu ya fara yi one by one yana binsu da kallo ba tare da yasan amfaninsu ko me zai yi da su ba.

Da yake yasan waya sai ya ɗauko na Jaish ɗin yana ta kallo, ya rasa ta ya zai yi ya kunnata, dan ya danna wajen kunnawa da ya sani na wayoyi amma taki kunnuwa, hakan yasa ya ji jikinsa ta kara sanyaya matuƙa, ya ga rashin amfanin bincikar aljihun tun da bai samu wani abin da zata taimaka mashi ba.

Daga karshe ya kwashi komai ya mayar in da ya fitar, ya É—auki kayan ya mayar ya makalesu, ya dawo ya kwanta yana tunanin yadda zai yi da wannan al'amari, ya saba da Jaish sosai wanda rabuwarsu lokaci guda haka babu ko sallama zai iya haifar mashi da babbar matsala, and ya zai yi da Mahnoor?. Ya jefawa kansa tambaya.

A ɓangaren Nenne kuwa, murna kamar zai kasheta, tuni ta je ta kyankyasawa gwaggo ga abin da yake faruwa, sun yi matuƙar jin daɗin hakan, gwaggo har da wani bata shawara da ta ɗaura ɗamarar zaman gidan bappa a yanzu dan ta dawo da ƴancinta da ta rasa a baya, sannan ta tabbatar ta gallazawa Mahnoor har sai Inna ta ji ɗaci a ranta tamkar ta haɗiyi zuciya ta mutu.

Ba ƙaramin daɗi Nenne ta ji ba jin abubuwan da gwaggonta ta ce, dan haka ranta fes ta janyo doggin kafafunta ta nufo gidan bappa da su.

A hanya ta haÉ—u da Ibrahim da su Mahreen. Ko tsoron Allah babu bare kunya ta wani dakatar da zu har da cewa.

"Kai Ibrahim ina kuma zaka kai su?".

Bai tankata ba, ga dikkan alamu basa zaman lafiya da ita, ko kallon in da take ma bai yi ba ya sanya kai zai wuce ya cigaba da tafiya.

"Ba da kai nike magana bane Ibrahim? Nace ina zaka je da su?"
A harzuƙe ta yi maganar, irin ranta ya ɓaci ɗin nan, ya za'ayi ace tana mashi magana zai bawa banza ajiyarta yasa kai zai wuce?.

Still dai bai tanka ba, bai yi kamar yasan da halittar bil'adama a wajen bama, ya cigaba da tafiya hannunsa sarkafe dana Mahnoor.

"Ke Mahreen zo nan ki wuce mu tafi tun da ke kam nike da iko da ke!!".

Cike da isa da gadara ta yi maganar, irin Mahreen ƴarta ai dole ta bi umarninta. To kun san halin Mahreen ba sai na sake faɗa ba, yarinya ce da bata bin bayan rashin gaskiya komai ƙanƙantarta, dan haka sai ta ce.

"Nenne ni kam kawu Ibrahim zan bi, ina gidan ArÉ—o yau".

"Ban yarda da haka ba! Zo maza ki wuce mu koma gida". Cikin gadara ta yi maganar.

"Nenne wai idan mun je gidan me zan yi maki? Kawai in je in zauna?".

Kai ta gyaÉ—a mata alamar e, sannan ta É—aura da cewa.
"Kwarai kuwa, ko ban isa in ce ki yi abu bane?".

Shiru ta É—an yi tare da juyawa ta kalli Ibrahim da Mahnoor da suka É—an yi nisa a tafiyar da suke yi, sun barta tsaye tana biyewa Nenne.

"Ni gaskiya Nenne ba zan koma gida ba, wajen Æ´ar uwata zan je, ke bakiga kuka take yi bane? Zan je ne mu rarrasheta, yau a gidan ArÉ—o zamu wuni!".
Tana magana tana turo baki na rashin kunya da kuma shagwaɓa

"Eyee ke da in nace ki je wajen gwaggo sai ki ce mun baki son zuwa ke ba zaki je gidan ArÉ—o ba, amma yanzu saboda munafurci ne har da cewa a can zaki wuni ko?".

Kai ta gyaɗa haɗe da cewa. "Yanzu ma saboda Adda Mahnoor zan je, ba dan ita ba ni Allah ya sawwaƙa in je gidan Arɗo".

Salati Nenne ta saka ta sanar da Ubangiji, sannan ta ce. "Kema yanzu kin koyi munafurci koh Mahreen? Wato Mahnoor ta koya maki munafurci da rashin kunya ko?".

ÆŠan zaro idanu waje ta yi, cike da mamaki ta ce. "Adda Mahnoor da munafurci kuma?".

Kai Nenne ta gyaÉ—a alamar e haÉ—e da cewa. "Ko karya nayi ne?".

Kai tsaye Mahreen ta amsa da. "Wlh karya ne! Adda Mahnoor bata munafurcin kowa, nice ma nan kullum nike kawo mata gulmar Inna Rabi, kuma har faɗa take mun a kan in dai'na gulmar mutane idan basa nan, in ya zama dole na yi maganarsu to ya zamana maganar da zan iya maimaitawa a gaban idanunsu su ji ransu bai ɓaci ba zan faɗa, kullum sai ta yi mun nasiha, ai Nenne ke da wancan gwaggo mai ido kamar na aljanun ne ma kuke yin gulmar mutane, ba har zagin Inna kuke yi ba? Ai ina jinku dik abin da kuke............."

Bata kai karshen maganar ba ta yanka a miliyan ta bi bayansu Mahnoor sakamakon cabka da Nenne ta kai hannu zata yi mata.
Chapter 11 · 0% Book details