← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 154 OF 242

Sashe 154

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A gefe guda kuwa Sharifat tana can tana neman Leesharh, dan ta je É—akin da take jinya bata sameta ba. Har É—akin Ramish É—in Sharifat ta zo ko Leesharh na a ciki nan ma ta ga wayam, cike da damuwa ta koma bedroom É—insu. Wayarta ta É—auka ta hau kiran number Ramish dan ta tambayesa ina Leesharh? Sai dai bai É—auka ba, É—aura wayar a saman phone set ta yi tare da kwanciya tana tinanin ina Leesharh ta tafi.

Can wani ɓangare na zuciyarta ya ayyana mata ai Leesharh tana tare da Ramish ɗinki. Wani irin zabura Sharifat ta yi ta miƙe zaune tana furta auzubillahi minashshaiɗanirrajim, dan zuciyarta ba zai iya ɗaukar wannan bala'i ba, kishi ne da ita nasu na gado, zata iya kashe Leesharh a kan Ramish, dan nata ne ita kaɗai.

(To nima zan iya kashe maltina roba goma a kan guyson, dan nawa ne ni kaɗai🥱😅)

Sai da ta ɗauki almost 5 mins tana ta nanata sunan Allah a ranta dik dan koran tunanin Leesharh na tare da Ramish, da kyar ta samu ta rabu da tinanin, sannan ta koma ta kwanta tana fatan Allah ya mallaka mata Yah Ramish ɗinta, haƙiƙa idan Sharifat bata mallaki Ramish ba za'a sami gagarumin matsala.

To my people's me kuke tunanin zai faru a gidan Abbie? Uhm muje dai zuwa.

••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥🔥

🔥🔥🔥PARIS🔥🔥🔥

Cikin bedroom ɗinsa ya wuce rike da hannunta, a gefen bed ya zaunar da ita tare da ɗauko tissue paper, hawayenta ya share mata tare da yin shiru yana mamakin karfin hali irin na daddyn nasu, ace mutum kamar Hoorain ai bai cancanci ace King ya hana shi wani abin idan ya nema ba, wannan sam ba halacci bane, mutum tun tasowarsa yana yi maku hidima, ya sadaukar da ransa saboda kare rayuka, dukiya, martaba da kimar masarautarku, sannan shi ne zai zama abin walaƙantawa a gareku dan kawai ya fita a matsayin bawanku mai yi maku hidima?. Har King yana da bakin cewa Hoorain ya tara makiya ba zai bashi ɗiyarsa ya aura ba? To saboda su waye ya tara makiyan? Ba dik dan saboda kare rayukanku ya tara makiyan ba?.

Kuma shi King da yake wannan magana a gabaɗaya kingdom ɗin suna da biyun Hoorain da mahaifinsa ne? Yau da za'a kawowa kingdom ɗin hari ace babu tawagar Hoorain da mahaifinsa kuna tinanin kingdom of power zata kai labari ne? Wlh ko zata kai labari sai da taimakon su Ramish, amma dik da haka yau Hoorain da mahaifinsa sune abin walaƙantawa da ƙasƙantar a gaban al'umma dan kawai Hoorain ya kamu da son Auta wanda ba shi ya ɗaurawa kansa ba, gaskiya yana da kyau ya gyarawa kingdom of power ɗin nan zama su san cewa babu wata aya ko hadisi da ta banbanta matsayin talaka da mai kuɗi, sai dai ayar da ta banbanta tsakanin mai tsoron Allah da mara tsoron Allah.

Ganin ya yi shiru yasa ta yi tinanin shi ma zai ji kyamar talakawa ne, bata san shi É—in cikakken mai amfani da iliminsa bane.

"Yah Omerish kai ma baka san my Hero ko?". Ta faɗa tana shessheka. Dawo da kallonsa a kanta ya yi, cikin sigar rarrashi ya ce. "Meyasa ba zan so abin da shalelena take so ba? Matikar bai saɓawa faɗar Allah ba tabbas zan zama mai goya maki baya my sweetheart". Ya kai karshen maganar yana janyota jikinsa. Zaro wayarsa daga cikin aljihunsa ya yi da nufin ya yi call sai ga kiran momma ya shigo.

Katse kiran ya yi ya sake kiranta, bugu ɗaya ta ɗauka, cikin natsuwa da girmamawa ya ɗaga mata gaisuwa. A maimakon ya ji ta amsa sai ya ji muryan King yana amsa gaisuwar tasa. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Dama yanzu zan nemeka Dad"......... Daga ɗayan ɓangaren King ya ce. "A ina kake tun jiya muke nemanka a waya a kashe?".

Raba jikinsa da Auta ya yi, sannan ya miƙe tsaye ya nufi balconynsa dan ma kada Auta ta ji hiransa da King, dan ya sha alwashin ba zai ragawa kowa ba muddin suka kawo mashi tsaiko a kan abin da ba Allah bane ya haramta, su sun zaɓi kenan su yi wa yarinya auren dole su tabbatar da rayuwarta a cikin kunci da bakinciki? To shi bai zaɓi hakan ba kuma ba zai zaɓa ba, infact bai ga wanda ya isa ya hana Zunaira abin da take so ba matuƙar bai saɓawa shari'a ba.

Saman É—aya daga cikin kujerunsa dake wajen ya zauna yana faÉ—in. "Ina Paris"...... Ta karfi King ya maimaita kalmar Paris kafin ya sake cewa. "To ka yi maza ka dawo in san ganinka". Jinjina kansa ya yi kamar yana a gaban dad É—in nasa, sannan ya ce. "Dad menene batu a kan Zunaira and Hoorain?".

King daga in da yake tsaye ya wani haɗe rai tare da komawa bakin bed ya zauna, momma dake zaune a bakin bed already ne mamaki ya kamata na ganin ya haɗe rai, da kallo ta bisa tana san fahimtar me yasa ya ɓata rai haka? Kada dai ace Smart yana yi mashi wannan iko da ya saba, dik sai hankalinta ya tashi.

"Wannan magana ai na gamata, na bawa Abdussalam aurenta, kuma this coming Friday za'a ɗaura shi, dan haka bana da buƙatar sake tada wannan magana, dalilin ma da yasa na ce ka yi gaggawar dawowa kenan, saboda bikin"........ Shiru ya natsu yana sauraron dad ɗin nasa har ya kai aya a magana, sannan ya ɗan gyara zamansa tare da jan dogon numfashi, cikin sanyin murya ya ce. "Amma ita Zunaira ta ce Hoorain take so ba Abdussalam ba!......"..

Katse shi King ya yi da cewa. "Ni kuma Abdussalam nike so ba Hoorain ba". Shiru Smart ya É—an yi, kamar ba zai sake tankawa ba, sai kuma ya ce. "Menene yasa baka san Hoorain dad?"...... A fusace King ya ce. "Saboda rayuwarsa bata da tabbas! Daga yanzu zuwa kowani lokaci zai iya mutuwa, ban shirya ganin rayuwar Zunaira a gantale ba! Dan haka na yi rantsuwa da girman Allah na kara yi ba zan bashi Zunaira ba, kada kuma ka sake mun maganarsu, dan na gama yanke hukunci, wlh a kan wannan magana sai dai Zunaira ta nemi wani uban!!!". Tashin hankali.

Haƙiƙa Smart ya fahimci dad ɗinsa ya ɗauki zafi dayawa, kuma a yadda ya yi wannan rantsuwa yake magana a fusace haka ya tabbata iya gaskiyarsa yake faɗe, and kome zasu yi ba zasu taɓa canza mashi ra'ayi, dan haka sai ya ce. "Okey dad, na yarda da maganarka, na yarda Zunaira ba zata auri Hoorain ba, but ina san ka saki Hoorain ya koma yadda yake rayuwa kamar da". Ya kai karshen maganar tare da ɗago idanunsa, unexpect ya yi arba da fuskar Auta tsaye a bakin kofar balconyn tana kallansa tana hawaye, bai yi zatan tana kusa ba, yanzu ta ji dik abin da suka faɗa da King.

Daga cikin wayar King ya ce. "Already ni na saki Hoorain, yanzu haka yana hospital yana jinya, idan ya samu sauki zai koma bakin aikinsa, dan mun yi yarjejeniyar hakan da mahaifinsa, ya mun alkawari Hoorain zai rabu da Zunaira har abada, shiyasa ma na sakesa".

Jinjina kai Smart ya yi zuciyarsa na ƙoƙarin pushing na fushinsa ya bayyana, shi kuwa yana ƙoƙarin danne zuciyar tasa saboda kada ya yi jayayya da mahaifin nasa, yana da ilmin addini sosai, so yasan rabo tana kisa, idan ya tsaya ya ce zai ja da dad ɗin nasu in Allah ya ƙaddara za'ayi wannan aure to suna iya rasa King ɗin, hakan ne kuma baya so, shiyasa ya sassauta zuciyarsa ya aminta da haka, gara mashi su bi wata hanya su saka King ɗin kaffara kawai a kan su yi ja in ja da shi su rasa shi na har abada, a kan batun aure da batun yara ba'a jayayya, idan ma'aurata sun rabu ba'a gardama a kan ƴaƴa, misali ace uwa ta ce ita zata rike uba ya ce abasa kayansa, irin haka ma Allah yana ɗauke ƴaƴan kowa ya raba faɗa, so a kan aure da yara ba'a ja in ja.

"Dad zamu yi magana anjuma". Yana kai karshen maganar ya katse kiran diff ba tare da ya jira amsarsu ba. Alama ya yi wa Auta da hannu a kan ta zo. Da Æ´ar gudunta ta tafi ta faÉ—a jikinsa tana sakin kuka mai tsuma zuciya. Rarrashinta ya fara yi cike da so da kauna. Cikin kuka ta fara faÉ—in. "Shikenan Yah Omerish kai ma yanzu baka goyan bayana? Yanzu ka koma bayan dad? Kai ma baka san my Hero?".

Hannu yasa ya ɗago haɓarta suna fuskantar juna, cikin sanyin murya ya ce. "Kin yarda da ni?"....... Kai ta gyaɗa mashi alamar e ta yarda da shi. "To i promised you that In Sha Allah zaki zama mallakin muradin ranki, burinki zai cika wannan alkawarina ne, alkawari kuma kaya ne". Cike da gaskiyarsa ya yi maganar, babu wasa ko golaya dan ta yi shiru yasa ya faɗa mata haka.

A ruÉ—e ta ce. "Yah Omerish how? Ta yaya zan mallaki Hoorain bayan daddy baya sansa, kuma ya yi rantsuwa da girman Allah ba zai bashi ni ba, sannan kowa a gida baya sansa, har Akka bata sansa, and nan da one week dad ya ce zai aura mun Yah Abdussalam". Tana magana zafafan hawaye suna bin kuncinta.
Ɗan jinjina kai ya ɗan yi kafin ya ce. "Haka ne dik abin da kika faɗa, and nasan abu ne mai wahala yiwuwar aurenku, amma In Sha Allah daddy da kansa zai sanya maku albarka a ranar aurenku, darasi zan bawa gabaɗaya familynmu ta yadda gobe ko da kuɗi aka basu ba zasu taɓa sake kyamar talaka ko na kasa da su ba".
Chapter 154 · 0% Book details