← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 232 OF 242

Sashe 232

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɗakin Diddi Mairo ya wuce ya je ya kwanta a zuwan anjuma zai koma wajen kiwonsa. Yana cikin kwanciyar ne ya ji mutum a kansa, ɗago kai da zai yi sai ganin Nenne a tsaye da zabgegen wuƙa tana kaɗa ƙugu kamar sandar snooker a kan lallai ya fitar mata da Mahreen, cikin sauri ya miƙe zaune yana kallonta, kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce. "Amma baki da hankali ko? Ko dai wani abin ne kika sha a yau?".

Wata uwar harara ta dalla mashi kafin ta ce. "Gaka babban mahaukaci kuma azzalumi! Ka sayar da ƴarka ga masu kuɗi, wlh sai ka fitar mun da Mahreen ko kuma in kasheka a cikin ɗakin nan, bakin shaiɗani kawai"....... Ransa ne ya yi mummunar ɓaci jin kalaman da take dangantasa da su, wai baƙin shaiɗani, cikin fushi ya miƙe tsaye suna fuskantar juna. Yau ya koma ainahin kalarsa, wani irin gigitaccen mari ya ɗauketa da shi wanda sai da yasa ta yi baya baya kamar zata faɗi ƙasa.

Ranta ne ya yi mummunar ɓaci da yasa ta ɗaga wukar da gaske zata buga mashi a ciki, sai dai ina, kafa yasa ya taketa ta yi baya ta bugu da jikin bango ta faɗi kasa wukar ma ya faɗi ƙasa, sandar kiwonsa ya ɗauka ya hau jibgarta tamkar an saukar mashi da wahayi. Jin ihunta yasa Diddi Mairo shigowa ciki da gudu, hankalinta ne ya yi mummunar tashi ganin abin da yake faruwa, dama ita tasan shi da iya duka tun da ya yi ta jibgar mahaifiyar Mahnoor, so ta ɗauka ya dai'na ne, ganin hakan yasa ta kara shiga taitayinta, tsoron zuwa bashi hakuri ma ta yi, sai ta ja baya tana ruwan hawaye.

Shi kuwa sai da ya tabbatar ya jiwa Nenne ciwo, sannan cikin fushi ya ce. "Ki tashi ki tafi gidan ArÉ—o na sakeki, kada in kara ganin kafarki a gidan nan!!". Ya kai karshen maganar tare da jefar da sandar ya nufi waje cikin fushin da tun bayan mutuwar maman Mahnoor bai sake shiga fushi irin wannan ba!.

Rushewa Diddi Mairo ta yi da wani irin kuka mai tsuma zuciya, bata taɓa tinanin zai iya sakin Nenne ba, saboda auren gida ce, sannan kuma kanwa ce ga mahaifiyar Mahnoor, ai ko ba komai sirirkinsa Arɗo ya yi mashi halaccin da ba kowa zai iya yi ba.

Amma kuma idan aka dubi tsawon shekarun da Nenne ta kwashe tana gana mashi azaba kowa yasan ya yi hakuri, kwata kwata bashi da kwanciyar hankali da ita, masifar yau daban na gobe daban, ga rashin zaman gida, bini bini tana yawon makota, ko girki bata zama ta yi mashi bare sauran abubuwan da yazamana hakki a kan mata ta yi wa miji, kai ya yi namijin ƙoƙari sosai da halinta dik da cewa shi kansa yasan alhakin maman Mahnoor ce yake bibiyarsa shiyasa ya haɗu da ukubar second wife, amma dai ya yi nadama ai!.

Kasa miƙewa da kafafunta Nenne ta yi, da ta yunkura zata miƙe sai ta faɗi, hakan yasa Diddi Mairo ta matso ta taimaka mata, yau dai babu bakin masifa, bata hana Diddi Mairo taɓata ba, ita ta taimaka mata suka fita waje, zata kaita ɗakinta Nenne ta ce a'a ita gidan Arɗo zata wuce, dan tasan halinsa idan ya dawo ya sameta ba zasu wanye lafiya ba, kara mata wani azaban zai yi, dan haka gara ta tafi kamar yadda ya ce ya saketa ta tafi ɗin.

Ba yadda Diddi Mairo bata yi da ita a kan ta zauna ba, amma ta ce ina babu wannan magana, haka ta lallaɓa ta yi ta bin jikin bango har ta isa gidan Arɗo da kyar. Allah ya taimaketa Arɗo na cikin gida baya waje a tare da jama'a, hakan yasa ta wuce ciki kawai. A tsakar gida ta isko iyayen nata goggonta na ta faman raba bala'in da ta saba, sai zage Inna take yi kamar an aikota. Ai tana ganinta ta nufeta tana tambayar lafiya kuwa?.

Faɗawa jikin goggonta ta yi tana faɗin ai Kwairaga ne ya saketa bayan ya yi mata wannan ɗan iskan dukan. Salatin da Goggon tasa ne yasa Arɗo fitowa daga bukkarsa da azama. Yana ganin Nenne ya ja dogon tsaki tare da cewa. "To yau kuma wace bala'i kika je kika taɓo yar bala'i?".

Take ta sha jinin jikinta ta natsu tsit, kukan ma haÉ—iye shi ta yi, cikin kamalarta with full respect ta ce. "Bappa ne ya sake ni kuma ya dakeni.........." Wani irin harara da ya dalla mata ne yasa ta yin gaggawar shanye sauran maganar game da haÉ—e malaman jikinta waje guda ta kara natsuwa. "Wato sai da kika tunzura shi ya sakeki ko? To ai ga gidan nan, sai ki zauna ki ci abin da uwarki take ci! Ke kuma tin da ba zaki É—aura yarinyar nan kan hanyar gaskiya ba, sai ku cigaba da zama ki tasata gaba kina kallo!!". Ya kai karshen maganar tare da juyawa ya koma cikin É—akinsa.

Cikin bala'i Goggo ta ce. "Lallai ma kam, ya dakar mun ɗiya ya kuma saketa shi ne baka ga laifinsa ba bare ka yi zancen ɗauka mata fansa kake wani cewa ita ce da laifi? To wlh ba zata saƙuba, idan kai baka san darajarta ba ni na sani, yau Kwairaga ba zai kwana da lafiyarsa ba, ke ɗauko mun mayafi in tafi in faɗawa su kawunki Iro da Ilu su zo su tafi su ɗauka maki fansa, ai ba daga saman bishi kika faɗoba, kuma ba kwaranyoki aka yi daga ruwan makwarara ba da wani matsiyaci can ɗan haure wanda bai gaji arjiki ba zai taɓa lafiyarki ya zauna lafiya, wane mutum, jini da tsoka ce ke gudana a jikinki kema, kuma rai ne dake, sannan iyayene suka haifeki!!". Ta kai karshen jajjagen bala'in tata tare da jan Nenne suka wuce ɗaki.

Inna dai bata ce masu ko uppan ba, dan tasan ko ta faÉ—a ma ba ji zasu yi ba! Sai dai ma su hauta da balbalin bala'i, su sauke haushi a kanta! Shi ma ArÉ—o yana jiyosu, amma ko a kasar sillpers É—insa bugun China bai damu ba.

Inna na tsaye a wajen goggo ta fito da mayafi fuuuuuu kamar wata haske ta wuce ta nufi waje, salati kawai Inna ta rinƙa nanatawa a ranta tana addu'ar Allah ya shiryi su goggo ta kuma shiga tsakaninsu da Bappa, dan tasan su Ilu mahaukata ne, tsab zasu illata bappa, shaye shaye suke yi, can cikin birni suka gano wani gidan giya, tun da suka san wajen a nan suke zuwa su sha su yi nakil har su yi guzuri, su dawo suna tangal tangal suna ashariya, ga shi giyar da suke sha ma irin na gero ne, uban aiki da caji kenan, haka suke hauka, Inna tasan ba hankali suke da shi ba, tsab zasu iya kashe bappa ba, hankalinta ne ya yi mummunar tashi sosai.

A daidai wannan lokacin kawun Mahnoor Ibrahim ya shigo cikin gidan bakinsa a É—auke da sallama. A buÉ—e kuma a gaggauce Inna ta yi kansa tana faÉ—a mashi ya je ya sanar da bappa ga abin da yake faruwa tun wuri yasan in da dare ta yi mashi kafin su Ilu su tattara zugarsu su je su yi masu illah. Sosai shi ma Ibrahim hankalinsa ya tashi, cikin gaggawa ya juya ya fita, sai addu'a Inna take yi na Allah ya kawo sauki a kan wannan al'amari, ita kuma Nenne tana É—aki tana murzan kuka. TO KUN JI ABIN DA YA FARU A JIMETA BAYAN TAFIYAR SU MAHNOOR KENAN, SHIN A YANZU YA BAPPA YAKE? YANA RAYE KO SU ILU SUN KASHE SHI? NENNE TANA GIDAN ARÆŠO KO YA MAYAR DA ITA GIDANSA? INA DIDDI MAIRO? UHM TO MU JE ZUWA

🔥🔥🔥🔥BLACK WORLD🔥🔥🔥🔥

Tsaye take a sama mai gabaɗaya tana kallon yadda duniya take, birnin ba dai wutar lantarki ba, 24 hours ba'a ɗaukewa, ko'ina tankar kamar rana ce, duniya dik ta yi shiru saboda dare da ya tsaya, iska mai matuƙar ni'ima ce take ta faman kaɗawa a wajen, shi kansa Ronnie ya jima da yin barci, ita kuwa barcin ne ya gaggareta ta hauro sama ta tsaya ko tsoro babu, kamar wata aljana, ba komai ya hanata yin barci ba face fargaba da tinanin zuwanta church gobe, abin ya tsaya mata a rai, ta duba Bibles ya fi sau goma, dik da ta tara hujojin tinkararsu, amma gabanta yana faɗuwa matuƙa, tana fargabar lamarinsu.

Sanye take da sleeping dress wando zuwa gwiwa da riga nai ɗan madaidaicin hannu launin milk color, ta sanya headband a kanta mai shegen kyau, birnin yana da matuƙar kyau da ɗaukar hankali idan ka kallesa daga sama da daddare, gabaɗaya jikinta ta yi weak, tinaninta ɗaya shi ne ya zamanta da su zai kaya?. A hankali hankali iska yake kaɗa kyakkyawan golden hair ɗinta yana wani rito har yana dawowa ta gaba yana rufe mata idanu, da yake headband ɗin nata ɗan siriri ne wanda ya tsaya mata a iya forehead ɗinta.

Ta luluƙa duniyar tinani sosai, sam bata ji alamar motsin mutum ba sai ji ta yi ya zuro hannunsa a daga ta bayanta izuwa saman shafaffen cikinta. Wani irin azabbabben tsoro ne ta ji ya kamata, ga shi dim light ne a wajen ba iya gane fuskar wanenen sosai zata yi ba. Da farko ta zaci Ronnie ne daga yanayin hannunsa a saman cikinta, amma da ta juyo sai ta ji wannan faɗin kirjin ya fi na Ronnie gaskiya.
Chapter 232 · 0% Book details