← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 242

Sashe 48

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aunty MieMie dake zaune a gefen King ne ta amsa da. "Gaskiya kam ba'ayi masu adalci ba, bai kamata ayi masu haka ba".

Miƙewa Jaish ya yi ya nufi hanyar fita daga parlon. Aunty MieMie ce ta tambaye shi ina zai je.

Ba tare da ya dakata daga tafiyar ba ya amsa mata da nitsuwa yake so, baya san hayaniya, zai je ne ya kwanta. Miƙewa ta yi ta bi bayansa dan tana san yi magana da shi. A wannan lokacin ne suna fita ya wuce hospital wajen Jawad dan yau tun da rana da ya je asibitin suka gaisa bai sake zuwa ba, Jawad kuma baya fita ko nan da can sai masallaci, so a tare suka je da Aunty MieMie.

Sosai momma ta nuna rashin dacewan abin da suka yi, ita ma mummyn Chuchu ta nuna hakan, mama dai bata ce ko uppan ba, ta dake a kan kujera tare da É—aura kafa É—aya bisa É—aya.

Momma ce ta nemi King da ya yarje mata zata je ta ga mutanen nan da suka rike mata yaro, har ta ji kaunarsu ya ka mata, uwa kenan, ko yaya ka yi wa É—anta abu bata mantawa da kai.

King yasan condition da take ciki na rashin nitsuwa a kan ɓatar Auta, a yanzu farincikinta suke nema ba ɓata mata ba, dan haka sai ya ce to za'a shirya mata tafiya nan da gobe ta je ta gansu ɗin, wannan shi ne dalilin zuwanta Jimeta, bata ma san Jaish yana da mata ba, bata san irin rayuwan da ya yi a can ba, ita dai ta zo da kanta ne ta yi godiya na riƙe mata yaro da suka yi, to kun ji yadda aka yi, taso su zo a tare da Jaish, amma yaki yarda, ya ce shi gaskiya babu a gajiye yake, kuma baya san zuwa ne kawai. Yauwa ku kara tafawa mata jama'a.......

••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

Da gudu Mahreen ta tafi ta rungumi guyson, dan a tunaninta Jaish ne, securitys É—insu sun so hana Mahreen isa gare shi, amma kafin su tareta tuni ta isa gare shi, kun santa da iya gudu.

Ita dai Mahnoor ta san ba Jaish bane, dan suna da banbanci da guyson dik da cewa guyson É—in ke binsa a wajen haihuwa, amma suna da banbanci.

Momma bata yi mamakin ganin Mahreen ta rungume mata yaro ba, saboda tana ganin Mahreen yarinya ce, sannan kuma hakan da ta yi yasa momma ta kara jin daÉ—i a ranta, dan alamu sun nuna sun yi sabo da Jaish sosai shiyasa ta rungumi guyson matsayin Jaish.

Uncle Jahiz ne ya wuce gaba wajen isa gaban ArÉ—o dake tsaye a kofar gida yana kallansu, sun ga shi ne dattijo a wajen sai suka nufesa.

Sarautar nan dai tana nan, badan momma bama da su uncle Jahiz ba zasu zo nan ba, dan haka cikin isa ya ce da ArÉ—o suna neman gidan da É—an uwansu ya yi rayuwa a ciki kafin suka zo suka É—aukesa kwanaki shidda zuwa bakwai da suka wuce!

ArÉ—o ya É—an yi mamakin jin yadda Uncle Jahiz ya yi mashi magana kamar wani É—ansa, yana mashi magana ba girmamawa, bai san haka suke magana cike da izza ba su kam.

Da hannu ya nuna masu gidansu Mahnoor dake bayansa, dan yasan a kan bakonsu Jaish suke magana.

Momma da guyson kuwa, sun yi tsaye suna kallan Mahreen da ta rungume guyson tana zuba mashi surutai haÉ—e da É—auki game da sambatun ta san zai dawo garesu dama, har da cewa ta yi kewarsa, ta fara bashi labarin irin kukan da Adda Mahnoor É—inta ta yi a lokacin da baya nan.

Guyson da momma dik babu mai jin yarenta, dan haka basu san me take faÉ—e ba, sun dai yi shiru suna sauraranta ne.

Jin basu yi mata magana bane yasa ta raba jikinta da guyson É—in ta riko hannunsa ta fara jansa wai ya zo su je su ga bappa, bappa ma yana can yana kewarsa. Ita dai Mahnoor idanunta a kansu ko kyaftawa ta kasa yi, tana kuma tsaye, fuskar mijinta kawai take gani a face É—in guyson.

Sam bashi da kuzari a jikinsa ya dawo da kallonsa a kan Momma, Mahreen sai faman jan mashi hannu take yi.

"Bita muje ka ji, dik yadda aka yi a gidansu yayanka ya zauna shiyasa take janka, ga dikkan alamu kallan matsayin yayanka suke yi maka".......... Cewar Momma kenan.

Kamar zai yi kuka ya ce. "Momma jikinta dik datti fa! Kalli yadda ta zo ta taɓani ta ɓata mun jiki".

Kunsan guyson É—an wanka ne, ga kayan jikinsa farare kal kal, irin Pakistan na maza riga da wandon nan ne, ya sha rawani a kansa, kyau iya kyau, so baya shiri da datti ko kaÉ—an, Allah sarki dan ma yana da saukin kai ne yasa bai yi mata faÉ—a ko ya mareta ba, da su Omaid ne ai da yanzu zancen sun sumar da ita ake yi.

"Yi hakuri, É—aukin ganin yayanka yasa ta yi maka haka, idan mun koma gida sai ka cire kayan ka ji?"................ Cewar Momma.

"Momma ni Allah bana san dattin, kice kawai ta sakeni".

Momma da ta fahimci zai iya saka masu kuka a wajen, dan wlh ko da wasa baya san datti, sai ta riko hannun Mahreen da take rike da shi, cikin harshen larabci ta ce da Mahreen.

"Zo wajena kin ji?......"

Bata idasa maganar ba Mahreen ta kwace hannunta, cikin tsiwa ta ce. "Wacece ke da zaki rikeni? Ni ki barni a wajen hamma na". Tana kai karshen maganar ta sake rike hannun guyson.

Kasancewar da fillanci ta yi maganar sai momma bata gane me ta faÉ—a ba. Shi kuma guyson tana rikesa ya fisge hannunsa da karfi haÉ—e da cewa........... "Kada ki sake rikeni da hannunki dik datti".
Da larabci ya yi maganar. In baku manta ba a baya Mahreen ta fara koyar larabci kaÉ—an kaÉ—an, dan haka ta ji wannan kalmar da guyson ya ce ta sake shi.

Sai kuma a lokacin ta lura voice É—insa ba iri É—aya da Jaish ba, muryarsa na yara ne, kuma É—an siriri ne sosai. Fahimtar hakan yasa ta yi saurin ja da baya daga kusa da shi.

A tinanin momma tsawar da ya daka mata na ta sake shi ne yasa ta ja bayan, dan haka sai ta yi ƙoƙari matsawa kusa da ita ta rikota. Ai ina, a miliyan Mahreen ta juya ta bar wajen tana rushewa da kuka mai ban tausayi, Allah sarki ta gane ba Jaish bane yanzu.

Uncle Jahiz da ya tsaya yana turɓune fuska yana binsu da kallo ne ya matso kusa da momma............ "Ga gidan nan, ku shiga ku yi abin da zasu yi kin dai ji yaya ya ce kada mu kwana, yau zamu juya". ....... Ya faɗa ransa a ɗan ɓace, da alama bai so batun zuwansun nan ba sam.

Momma ta lura da baya san zuwa, dan ma saboda ita ce, wlh da mummyn Chuchu ko mama ne ba zai zo ba, dan haka sai ta wuce gaba saboda su yi sauri su je su fito.

Cikin mutunci ta gaida Arɗo, sannan ta buƙaci da ya yi mata jagoranci izuwa ciki, bodyguards zasu shige cikin su duba babu wani abin cutarwa kafin ta shiga, ta yi saurin dakatar da su, ta ce su bari zata shiga kawai.

Mairo ArÉ—o yasa ta tarbesu hannu bibbiyu, a lokacin da suka shigo bappa baya É—akin, ya samu kaikayin ta sakesa saboda ArÉ—o ya labta mashi kashin sosai a jikinsa.

Nenne kuma ta gudu gidan Arɗo, so Mairo ce kawai a cikin ɗakin tana ƙoƙarin gyara komai, ta fitar da tabarman da aka kwantar da bappa, ta juye mashi wani ruwan wankar ya shiga wanke jikinsa, da yake isaka na kaɗawa sosai ma har kashin shanun ta bushe a jikinsa.

Tabbas momma ta ji kyamar shiga cikin gidan, amma duba irin alkhari da suka yi mata, É—anta sukutum, first born É—inta suka kula mata da shi, sai ta danne kyamar ta shiga cikin gidan.

Guyson kam ya gudu wajen uncle Jahiz sun koma cikin mota sun zauna. Time da Mairo ta yi masu iso cikin É—akin, Momma ta so ta ki shiga, amma kuma da ta tuna Jaish sai ta daure ta shiga ciki.

Mahnoor kuwa ganin babu Jaish a cikin tafiyar sai ta dawo cikin gida ta wuce É—akinta ta kwanta, ita kuwa Mahreen bin momma ta yi har cikin É—akin bappa dan taga me ya kawosu gidansu?.

ArÉ—o ma ya shigo cikin É—akin dan ya ji me ya kawo su Momma?. Cikin girmamawa Mairo ta tsugunna ta É—agawa Momma gaisuwa.

Sai dai kash babu fillanci, momma bata gane komai da suka faÉ—a ba, da yake ArÉ—o babban malami ne yana jin larabci sai ya sanar da momma gaisuwa Mairo take yi mata.

Jinjina kai kawai momma ta yi, ta ku ma É—an ji daÉ—in ansamu mai jin irin larabcinta, dan haka sai ta faÉ—a mashi ita mahaifiyar bakon da suka rike ne, ta zo ne ta yi masu godiya bisa rike mata yaro da suka yi.

Sosai Arɗo ya yi mamaki, a wani ɓangaren kuma ya ji matuƙar daɗin hakan, ko ba komai sun nuna sun san anyi masu halarci.

"Bani na rike ɗanki ba, ɗana ne ya riƙesa, ya shiga wanka bari ya fito sai ku gaisa".......... Cewar Arɗo.

Jinjina kai momma ta yi ba tare da ta yi magana ba, dik zama a cikin ɗakin ya isheta, ji take yi kamar zata yi amai, amma haka ta daure har bappa ya fito daga wanka, yana sanye da jampa blue, ta koɗe kam sosai, jikinsa fa dik ya ji ciwo bawan Allah, bayansa ta ɗaye, kai Nenne muguwa ce, ta gana mashi azaba, wannan ma fa wai yanzu aka fara zaman kishin, anya nan gaba Nenne ba zata saka masu wuta ba kuwa.................🤔

Lokacin da su Momma suka zo bai gama dawowa cikin hayyacinsa ba, so bai san da batun zuwan nasu ba. Da ya fito yaga jirage a saman suna shawagi kuma sai ya ce bari ya je ya wanke jikinsa da sauri ya fito yaga menene yake faru? Shi ma dai da kallo jiragen sau É—aya ya raya a ransa Jaish É—insa ne ya dawo garesu.
Chapter 48 · 0% Book details