Sashe 37
Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kaiconku! Kun bani kunya kuma na raina kwarewarku! Commander kana da shekaru sama da talatin kana matsayin mai jan ragamar warriors da suke cikin kingdom ɗin nan, amma yau har a samu wani mai karan kwana da zai iya keta tsaronka ya shigo har cikin kingdom ɗin nan ya ɗauki Zunaira ya fita da ita! A gaskiya ka gaza dayawa Zafar!"............ Shi ne abin da King ya faɗa a kan kunnen Hoorain da ya dakata da yunƙurin shiga fadar ya kasa kunne yana sauraronsu.
Kasa da kai commander ya yi, bashi da bakin yin magana tun da ba'a bashi izini ba, sai kawai ya yi ƙasa da kai yana sauraron faɗar King.
Cigaba da faÉ—a cikin zafa King ya yi.
"Dole hukunci zata hau kan Hoorain! Saboda shi na ɗaurawa alhakin kula da Zunaira! Shi na ɗaurawa alhakin kada ya bari ko guda ya taɓa mun ita, dan haka idan wani abin ya samu Zunaira dole in hukunta shi!!"..........
A dai'dai wannan gaɓa sai da commander Zafar ya yi hanzarin ɗago kansa da kallonsa izuwa kan King, ya ji zazzafar magana da baya jin zai iya jure hakan, wato hukunta Hoorain, yasan hukuncin King bata da sauki, bare kuma a kan Auta, ai ina abin ba zata yi kyau ba.
Sai da ya ji tsikar jikinsa ya tashi, gaban maza sai da ta bada dukan uku uku, Hoorain shi ne farincikinsa, sannan ace za'a hukunta shi da laifin da bai sani ba? Gaskiya a wannan gaɓar baya jin zai iya ɗaukar wannan hukunci na King, to amma ya zai yi? Ya jefawa kansa tambaya. Sai sake sake yake yi a cikin zuciyarsa ya daina sauraron abin da King yake faɗa.
Kamar daga sama ya ji warriors dake tsaye a kusa da shi ya kai hannu ya taɓa shi yana faɗin. "Master King yana magana".
A ɗan zabure ya miƙe tsaye, bawan Allah ya afka duniyar tunani ne bai ji King yana tambayarsa ina Hoorain ɗin yake ba?.
Ran King ne ya kara ɓaci na ya yi magana commander bai jisa ba, kun san idan mutum yana cikin ɓacin rai da zarar an mashi abu kaɗan zai tashi ya hau bala'i, to haka abin take.
Ɗan risinar da kai ƙasa commander ya yi alamar girmamawa.
"Kayi hakuri ranka ya dade, tun É—azun da kace in kira Hoorain É—in na faÉ—a mashi kana kiransa, ban yi tsammanin zai kai har iyanzu bai iso ba!".
Sosai ran King ya kara bakanta, a É—an fusace ya umarci É—aya daga cikin warriors dake cikin wajen a kan su kira mashi Hoorain yanzun nan, sannan kuma dole ya fuskanci wani hukuncin a kan jinkirin da ya yi bai amsa kira ba.
Dik maganganun da suke faÉ—a a kan kunnunsa suka yi ta, ya ji komai! A maimakon ya shiga cikin fadar ko hakurine ya bawa King ko zai samu sassaucin hukunta shi da za'ayi, sai ya juya ya fasa shiga, cikin sassarfa ya bar wajen. Masu gadi kuwa basu ce da shi ko uppan ba!.
Kai tsaye bedroom É—insa ya koma. After 5 mins da shigansa cikin É—akin ya fito ya nufi katafaren wajen dawakansu, dik da yana sanye cikin kayan yaki ya É—aura jacket mai girma a jikinsa, ya kuma sanya hular jacket É—in a kansa, hakan ba zai hana ka gane yana cikin tashin hankali na kin karawa ba!.
Saman wannan ƙosasshen jibgegen dokin nasa ya hau. Da karfi ya bawa dokin wuta, kai tsaye babbar gate na Kingdom ɗin ya nufa.
Tun daga kan gate na farko har izuwa babba na karshe babu wani warriors da ya dakatar da shi ko ya ce zai hana shi fita ko dai ya tsaya a bincikesa, saboda dik wanda ya kwana ya tashi a cikin kingdom É—in yasan wanenen Hoorain kuma me matsayinsa, dan haka basu yi gigin dakatar da shi ba, sai ma hanya da suka bashi cikin girmamawa ya danna waje a miliyan.
Ina kuke tunanin zai je? Meyasa yaki amsa kiran King? Meyake shirin faruwa ne? Guduwa ya yi ne ko menene?....................
=======================🔥
Dai'dai lokacin da wannan warriors da King ya aika da ya kira Hoorain ya dawo cikin fada dan ya isar da sakon Hoorain baya nan bai gansa ba, a dai'dai wannan lokacin uncle Jahiz ya danno kai cikin fada, ta kofar da zata sadaka da cikin gida kenan.
Sun jero a tare shi da Jaish, tin É—azun suka shigo cikin kingdom of power, yanzu haka basu fara isa ga kowa ba sai da suka iso ga King.
A karo na farko a tarihin kingdom of power yau King bai san lokacin da ya miƙe tsaye daga kan kujerar mulkinsa a zabure ba lokacin da ya ɗaura idanunsa a kan Jaish.
Tun da King yake bai taɓa jin wani abin na tashi hankali ko na farinciki or al'ajabi da zai sanya shi ya zabura ya miƙe tsaye daga saman kujerarsa ba sai dawowar Jaish unexpext, Ramish ya iya bazata kam gaskiya.
Sun jima suna dakon wannan rana shi da Momma, kullun addu'arsu Allah ya bayyana masu É—ansu farincikinsu, sai ga shi Allah ya bayyana shi a lokacin da basu tsammata ba, lokacin da suka fidda rai suka yanke kauna, suna cikin wani tashin hankalin kawai ya dawo garesu unexpext, kai Allah abin godiyane matuka, ya baka wani lokaci, wani lokaci kuma ya hanaka, dik cikin ikonsa da kyautatawansa ne!!.
Dik da commander yana cikin tashin hankali da damuwar furucin King a kan Hoorain zai karɓi hukunci hakan bai hana shi ya zaro idanu yana kallan Jaish ba.
GabaÉ—aya su salama sun zuba mashi idanu, suna san yi mashi sannu da dawowa, amma babu hali, dan King bai bada damar ayi magana ba.
King É—in kuwa, ya tsaya ne tamkar wanda aka dasa. Idanunsa sun zaro waje sosai, kallonsa a kan fuskar jaish É—insa da ya ke kallan abin tamkar a mafarki ko kuma zuciyarsa ce take yi mashi gizo.
Karisowa gabansa Jaish da uncle Jahiz suka yi, shi Jaish mamakin irin kallansa da King yake yi mashi ya yi, saboda in baku manta ba a baya ya yi loosing memorunsa ne, yanzu ne ya dawo dai'dai, so shi bai san da cewa ya jima baya gida ba, ya mance da rayuwarsa ta baya wato na gidan bappa kaf.
Har sai da Jaish ya tsugunna a gabansa domin kwasan gaisuwar ban girma wanda kun san yin hakan dole ce a sarauta matuƙar masu gudanar da mulkin irin King Zuhair ne masu ƙarfin izza.
Jin bugun numfashin É—an nasa a kurkusa da shi ne yasa ya gasgata abin da idanun nasa suke gane mashi, amma dik da haka sai da ya ce.
"My Jaish kai ne? Hakika kai ne É—ana, tabbas kai ne!"............. Ya yi maganar cikin murya mai sanyi, amma cike da rawar jiki.
Bai jira amsar Jaish ba, ya yi sauri duƙawa ya ɗagosa ya jawo shi jikinsa ya rungume.
Rungumar tasa tana da ƙarfi, cike da kewar watanni da suka wuce. Ya rike jaish gam kamar kar ya sake barinsa ya motsa ko nan da can, kamar kada ya raba jikinsu tsantsar so da kauna.
"Na jima ina jiran wannan rana, mun jima muna neman ka........... ba zan sake rabuwa da kai ba!".
Ya furta cikin farinciki wanda ke haÉ—e da murmushi mai bayyana farincikin sosai.
Jaish da bai gane me King yake magana a kai ba sai ya ce. "Dad ba zamu rabu ba ai dama".
Kara kankamesa sosai King ya yi tamkar zai mayar da shi cikin cikinsa. Sai murmushi uncle Jahiz yake yi. GabaÉ—aya fada sai da suka É—an murmusa ban da commander wanda dama shi baya yin murmushi, sannan kuma ya kara haÉ—uwa da yana cikin damuwa King zai hukunta mashi É—an gold É—insa.
Dawowar Jaish ya sanya su farinciki ya kuma sanyaya masu zuƙatansu akan raɗaɗin da suke ciki na rashin gimbiya Zunaira.
Yanayin ya cika da farinciki mara misaltuwa, kamar duniya ta tsaya domin wannan lokaci na musamman. Kowannensu yana jin tamkar zuciyarsa tana kara kaunar juna. Wannan haɗuwa ta koma alamar soyayya da ƙarfin alaƙar uba da ɗa, wanda baki ba zai iya misiltawa ba.
Uncle Jahiz ne da ya ga abin nasu ba mai karewa bane sai ya matso ya ɓanɓanre Jaish daga jikin King yana faɗin.
"Is okey yaya, Jaish lest go to ur mom room, I want to see her reaction a lokacin da zata É—aura idanunta a kanka".
Ɗan ɗaure fuska kaɗan Jaish ya yi. "Uncle sai ka ce wanda ya ɓata tsawon lokaci sai yanzu aka ganesa? Tafiya fa nayi na je na dawo, kaga dad ma sai wani ƙanƙameni yake yi".
Tun da ya fara magana idanun King a kansa, sai yanzu suka fahimci Jaish fa bai san komai dangane da ɓacewansa na tsawon watanni ba, dan haka sai King ya ce Jaish ya je wajen mommarsa da wuri, ya ce mashi hakan ne kuma dan yana da yakinin zata rage damuwar da take ciki a halin yanzu idan ta gansa.
Aikuwa hakan ce ta faru. Lokacin da suka haÉ—u da momma a bedroom na King, hawaye masu É—umin gaske ne suka fara kwaranya daga idanunta, tamkar ruwan sama mai É—auke da albarka. A hanzarce ta sauko kasa daga saman bed É—in King, da sauri ta kariso ta rungume shi da karfi, numfashinta yana cike da farinciki mara misaltuwa.
Ganin abin take yi tamkar a mafarki, shi kuma mamakin hakan yake yi, dik da yasan cewa Momma tana yi mashi fiye da haka idan ya yi tafiya ya dawo, to amma bata ruwan hawaye a kan tafiyarsa da dawowansa, yau sai ga shi tana hawaye, sai ƙwaƙwalwarsa ta fara bashi lallai akwai wani dalili mai karfi da yasa iyayen nasa suka yi mamakin dawowarsa, ƙwaƙwalwarsa ce ta tariyo mashi yadda King ya tarbesa, abin sai ya yi mashi some how haka.
Raba jikinta da nasa momma ta yi ta fara binsa da kallo, tana duba shi daga sama har ƙasa, kamar tana tabbatarwa idanunta shi ne ko ba shi ba.
"Kai ne Jaish, da gaske kai ne ka dawo gare ni, Allah mai iko, Allah mai kyauta mai kari!". Ta furta cikin muryar da ta ƙunshi da dukan ƙauna ta duniya.
"Momma nine mana, akwai wani abin ne?".