← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 242

Sashe 86

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Matsawa kusa da Jaish Jawad ɗin ya yi, wani irin tausayin ɗan uwan nasa ya ji, ɗan rungumosa ya yi yana ƙoƙarin kwantar mashi da hankali. King kuwa, waje ya buƙaci da su samu su zauna zasu tattauna. Da kyar Jaish ya yarda ya zauna a bakin bed ɗin daddyn nasa, sai huci yake yi shi ransa a ɓace ancuce shi da aka dangantasa da ita, an zubar mashi da kima.

Zama King ya yi a gefensu, sai da ya fara da rarrashin É—an nasa, suka haÉ—u shi da Jawad suka taushi wannan zazzafar zuciyar, dan idan zuciyar bata sanyayya ba babu wata magana da zata iya shiga kunnensa har ya iya amfana da ita, hakan yasa suka fara da tausan shi.

Sai da suka tabbatar da ya É—an huce, sannan ne King ya fara bashi labarin yadda Momma ta faÉ—a mashi komai dallah dallah da yadda aurensa da ita ya kasance, zaman da suka yi da komai da komai.

Tin da King ya fara magana basu ce ko uppan ba, suna binsa da kallo suna sauraro har ya dasa aya.

Da É—an É—aga murya Jaish ya furta. "That's not me dad! Not me! Gaskiya wannan ai sai dai a film ne kawai zai faru, me I can't do that, kawai dai they told momma what the want ne kawai, but isn't true, kuma ni i can't believe that, and i can't accept this nonsense, dik zan yi maganinsu ne". Cike da gaskiyarsa yake wannan magana.

Cigaba da tausan shi suka yi, King ne ya ce. "Sorry son, ba mommarka ta ce we should give her one week zata gabatar mana da yarinyar ba? So calm down, after one week sai mu ce we can't agree with her idan muka ganta, that's all".

Girgiza kai ya yi tare da miƙewa tsaye. "No dad, ba zai yiwu ba, babu wani one week da zata yi, yanzu zata bar gidan nan, for what reason zata ce matata ce? Ni nace ina san in yi aure ne? Did I say so?". Ya kai karshen maganar tare da nufar waje.

King bai dakatar da shi ba, dan ya fahimci lallai yau ran ɗan nasa a matuƙar ɓace yake, saboda Jaish bai taɓa yi mashi magana a irin wannan sigar ba, bai taɓa ɗaga murya fiye da nasa haka ba, kuma ga dikkan alamu Jaish ya manta a gaban King yake ma, dan har da ficewa tin basu gama magana ba, a bisa dokansu Jaish ya cancanci hukunci a kan abin da ya yi yanzu na suna magana da King ya tafi, dik da yake matsayin daddynsa sarki fa sarki ne mai cike da isa da izza a ko ina yake.

Ni kuwa na ce ba a ko'ina yake ba, ina da ja a kan wannan magana, domin kuwa a gaban momma dai baby yake zama, babu wani sarauta a wannan waje idan yana............. To dai saboda sirirkina ne na yi shiru, amma da kwance mashi zani a kasuwa zan yi....😅

🔥🔥🔥

Amma sanin halin ɗan nasa yasa bai ce komai dangane da hakan ba, sai ma ya ce Jawad ya bishi ya rarrashesa kada ransa ta cigaba da ɓaci. Da sauri Jawad ya miƙe ya bi bayansa. Shi kuma King parlournsa ya fito dan ya yi breakfast ya tafi fada, yau sarkin hatsi zai fitar da zakka daga runbum kayan hatsi na King izuwa ga talakawan dake cikin kingdom da kawaye.

•••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

A yau momma ta tsara Ibrahim kawun Mahnoor zai koma Nigeria, sai dai zai koma ba tare da ya sanya Mahnoor ko Mahreen a idanunsa ba, dan kowa yasan yadda dokan kingdom of power yake, dik da yake kawun Mahnoor yanzu matsayin matar Prince take, bashi da damar ganinta a saukake haka, idan ba ita ta buƙaci ganinsa ba to ko ya so ganinta ba za'a bashi dama ba har sai ta buƙata, kuma sun shiga ɗakin gyara ma abinsu. Ko momma ɗin ma bai samu damar gani ba, ta dai turo a faɗa mashi nan da sati ɗaya (wato idan King ya aminta da Mahnoor kenan) nan da sati ɗaya ya sanar da bappa zasu zo da tawagarsu su kawo masu kayan lefen Mahnoor da sadaki da komai da ake yi a biki, shi ne sarinta.

Sannan ta haÉ—a mashi uban tsaraba, yadika, shaddoji, atamfa, lace da arab abayas and jallabiyas, kayan abinci da makuÉ—an kuÉ—aÉ—e a kan ya kaiwa bappa a rabawa Æ´an uwan Mahnoor sai sun zo nan da sati guda In Allah ya É—orasu a kan King.

Tawagar mota guda ta É—aga a kan a kaisa airport, ya samu gata albarkacin Mahnoor, dan kuwa private jet aka É—aga ta É—aukesa zuwa har birnin Jimeta Yola.

Yana san ganawa da ƴaƴan nasa, amma babu dama, haka ya hakura dan bai ga fuskar tambayar ina suke bama, saboda warriors da suka kai saƙon Momma garesa bai ga fuskar ya masu magana ba, tsoro ma suma bashi, da wuri dole ya amshi komai suka wuce airport.

Yana zuwa baifi da minti 10 ba jirginsa ya É—aga sai Nigeria.

••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

UNCLE JAHIZ🔥

Sai da ya tsaya Zee ta ci abincin nan sosai ta ƙoshi, sannan ya ce ta tashi su je ya kaita wajen ƴaƴansa ta yi wanka ta shirya anjuma su je kallan Khadijah.

Ajiyar zuciya ta sauke, haƙiƙa ta yi farinciki na jin cewa zata je kallan ƴar uwarta, sai satar kallansa take yi, idan ya kalli face ɗinta kuma sai ta yi saurin kawar da kallanta.

Ɗakin Aneesa ya nufa da ita, a lokacin ita kuma tana ƙoƙarin fitowa hannunta rike da wayarta tana kallan hoton Yah Rizwan, Allah ya gani tana san bawan Allahn nan. Sanye take da sleeping dress, yanzu ta tashi daga barci, kamar wata aljana ta samu labarin Yah Jaish ya yi aure ne ta nufo waje, ko wanka bata tsaya yi ba zata je kaiwa Fanan gulmar.

Kai Aneesa duniya, da alama ƴaƴan mama ma ba baya ba a kaifin ƙwaƙwalwa, ga Ramish ga Aneesa, ko daga ina ta samo labarin Jaish ya yi aure kuma?. Maganar da iya King and Momma ne kawai suka sani, sai kuma Yah Jawad da aka faɗawa da safen nan, ko uncle Abbas and uncle Jahiz da suke matsayin uba a garesu ma basu sani ba, kai gaskiya Aneesa ta fara bani tsoro.

Zata fita shi kuma zai shigo, É—an karo suka yi, baya ta É—an koma tana ce mashi sorry haÉ—e da cewa. "Good morning my lovely second dad".

Kanta ya É—an shafa yana amsa gaisuwar tata cike da kauna, Allah sarki koma dai me Aneesa macece mai fara'a ga iya Æ´an uwanta kawai banda bare, a waje kana ganinta zaka san jinin sarauta ya ratsa jinin modarawa dake gudana a jikinta, kuma suna shiri da uncle Jahiz sosai.

"Daughter ga friend na kawo maki, ki tayata ta yi wanka ki bata kayanki ta sanya". Ya faÉ—a yana satar kallan Zee ta witsiyar idanunsa.

Da wani irin kallo mai kama da na ƙaskanci ta ɗan bi Zee da shi, ba dan uncle Jahiz ne ya kawota ba da bata ga dalilin da zai sa wannan ƙazamiya ta shigo mata room ba, sai wari ma take yi, ta faɗi hakan a cikin ranta, a fili kuma sai ta ɗan kwaɓe fuska, cike da izza ta ce. "Second dad wacece ita ɗin?".

Ya fahimci kyamar Zee take ji duba da yadda ta kwaɓe fuska, amma bai ga laifinta ba, dan haka suke, suna da tsabta basa san datti komai ƙanƙantarsa.

"Daughter tana da mahimmanci sosai ga rayuwata, ba kamar yadda kike tinani ba, ta wuce nan, ki kula mun da ita sosai, kada ki ji kamar ba Æ´ar uwarki bace, ki kalleta a matsayina kin ji?".

Ya yi mata hakan ne dan kada Zee ta fiskanci kyara da kyama a wajensu, yasansu sarai, idan ba haka ya bi da su ba wlh Zee zata yi kuka kasancewarta da su.

"Second dad ka ganta fa, a hakan ne take da mahimmanci a wajenka?". Cike da mamaki ta yi maganar. Tana yi tana É—an hararar Zee da wannan idanun nasu na gado.................................... Jinjina kansa ya yi alamar tabbas tana da mahimmanci a wajensa.

"To amma second dad meyasa bata yin wanka, ka ji fa wari take yi". Ta sake jefa mashi tambaya.

Da yake da larabci suke yin magana, kuma sun zurfafa sosai sai yazamana Zee bata ji sosai, dama sama sama take ji, shi ma dan islamiyyar da suka yi kafin babanta ya rasu ne yasa take É—an ji. So bata ji irin cin mutuncin da Aneesa take yi mata ba.

Satar kallan Zee ya yi kafin ya dawo da kallansa a kan Aneesa da ta turɓune fuska sosai.
"Daughter bata da lafiya ne fa, daga hospital ta tawo yanzu, please take good care of her, ni zaki yi wa kin ji my lovely daughter?".

Kai ta gyaɗa mashi amma rai bai so ba, dan yadda ta ɓata ran nan babu alamar zata yi na'am da Zee, ta yi mugu mugun rai'na class ɗin Zee, a cewarta ma ko a ƴar aiki ba zata ɗauki Zee ba, gaskiya kuma dik kuyangunsu mata ne masu tsabtar gaske.

"Allah ya yi maki albarka Daughter, anjima da yamma zan zo in ɗauketa kin ji?". Sake jinjina kanta ta yi tana cigaba da ɓata fuska.

Juyowa ga Zee ya yi, cikin harshen turanci ya ce. "Zee zan dawo da yamma in É—aukeki, ki zauna tare da Daughter kin ji?".

Kanta a ƙasa tana ɗan satar kallansa ta amsa da okey sai ya dawo. Kamar ba zai tafi ba, alamar baya san rabuwa da ita, amma sai ya daure ya juya ya fita. Yana juyawa ta bi bayansa da kallo.

Kura mata idanu Aneesa ta yi tana kallan yadda take binsa da kallo har ya kurewa ganinta, sannan ta katseta da cewa. "Kyakkyawa ne uncle É—ina ko?".

Aneesa akwai iya shege wlh, cikin harshen turanci ta yi maganar ganin uncle Jahiz ya yi wa Zee É—in magana da turanci, sai ta yi tinanin ko bata jin larabci ne yasa, kuma ta ganta bakar fata sai ta kara rai'na class É—inta.
Chapter 86 · 0% Book details