← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 170 OF 242

Sashe 170

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsaye yake a tsakiyar ɗakin ɗaure da towel a waist ɗinsa, da alama daga wanka ya fito, dan ga dark black curly hairnsa nan yana ɗigar da ruwa, hannunsa rike da wani ɗan ƙaramin towel yana goge kyakkyawan gashin kan nasa. Da yake ta kudurta a ranta kome zai faru babu gudu babu ja da baya sai ta daure bata juya ta gudu ba, kada ku manta ta taɓa ganinsa a yanayin da ya fi haka, a farkon ganinta da shi da ɗan ƙaramin short ta gansa, gara yau towel ɗin tana da ɗan tsawo ta kai mashi har zuwa gwiwa.

Tun daga kan tafukan kafafunsa ta fara kallansa har izuwa sama, ita kanta ta shaida he's so sexy, handsome and cute, yanayin jikinsa sai yasa ka fola..... Tana sauke kallanta a kan face ɗinsa sai taga shi ma ita yake kallo, dan fa ba karya ta yi kyau cikin shigarta. Suna haɗa idanu ya yi gaggawar kawar da nasa kallan yana ɗaure fuska, ta fahimci sam sam baya san ta kama shi yana kallanta, dan haka sai ta yanke shawarar zata rinƙa dannewa ba zata bari ya san ta san yana kallanta ba.

Kai Black Tiger da Sweetie duniya, wato babu maganin Black Tiger sai Sweetie, a gana mata azaba amma kuma yana jin daÉ—in kallanta, musamman idan tana tare da Ronnie tana sakin cute smile É—in nan nata mai narkar da zuciya.

Cikin dauriya da natsuwa ta tako ta nufo in da yake, bai yi kamar yasan tana zuwa ba, ya cigaba da yin abin da yake yi. A dab gabansa ta tsaya, hannu ta kai ta karɓi ƙaramin towel dake hannunsa, zuciyarta na harbawa da sauri sauri, ta yi ƙasa da murya cikin siga mai jan hankali da salo ta ce. "Dama ni nasan kai adali ne, kai ɗin mai tausayi ne, kai ɗin jarumi ne, kai ɗin mutum ne da dik in da ake neman cikakken namiji ka kai nan har ma ka wuce, ba zan taɓa mantawa da alkhairinka na yafewa mutanen birnin nan ba, tabbaa yadda kake da balai'n kyau zuciyarka ma haka take". Ta ɗan dakata da yin maganar tare da kai kallanta a kan face ɗinsa, sannan ta fara goge mashi Lion chest ɗinsa da towel ɗin.

Mutuwar tsaye ya yi yana tinanin shi kuma a yaushe ya yi wa mutanen birnin nan afuwa da har take yi mashi irin wannan yabo? Sai dai kuma yabonta a garesa ta ratsa zuciyarsa, ya ji daÉ—in hakan sosai, sai ya ji dama ta cigaba da yi kada ta dakata...... Batu na gaskiya yabo tana karya zuciyar koma wani irin mutum ne, ki gwada ware rana guda ki yi yabo da zafafan kalamai ga wanda yake kusa dake kiga yadda zai shiga cikin farinciki a wannan lokaci, gaskiya ne abin da hankali bai bayar ba rashinsa ba zai bayar ba, abin da kwamciyar hankali bai bayar ba rashinsa ba zai bayar ba.

Haƙiƙa Sweetie ta fahimci yabon da ta yi mashi ya yi tasiri a cikin zuciyarsa, dan har da sauke ajiyar zuciya ya yi, kuma ta ji hakan, dan haka ta shiga farinciki ita ma.

"Kana da kyau sosai our big bro, haka zalika zuciyarka ma mai kyau ce tsarkakekkiya". Yadda take magana cikin salo mai É—aukar hankali yasa bai san lokacin da ya amsa mata da. "Amma kuma jiya kin ce zuciyata bata da kyau ai?"....... Kam bala'i ashe kalamanta na jiya sun shiga kunnuwansa, magana da ta yi mashi a tsawatance yasa ya ji ba zai iya ragawa kowa ba, da ace jiya ta yi mashi magana yadda ta yi mashi yau da tabbas za'a samu rangwame, sai dai kash, ta fusata ita ma, tabbas magana cikin natsuwa yana iya canza komai.

"Jiya ai ɓacin rai ne yasa na yi maka magana a haka, amma tabbas kai mutum ne mai farar zuciya". Ta kai karshen maganar tare da ɗaura mashi ɗan towel ɗin nasa a saman shoulder ɗinsa, sannan ta juya da nufin ta matsa daga gabansa, ta koma saman sofa ta zauna ta jirasa yasa kaya ya fito ta kara yi mashi godiya, bata san karya Ronnie ya sharara mata ba.

Tana juyawa ɗan ruwa ruwan da ya zuba a wajen daga gashin kansa yasa ta zame, baya baya ta yi ta faɗa jikinsa, buga kanta da kirjinsa ta yi a in da ta tsuke fuska kamar zata yi kuka. Tana ƙoƙarin yin ƙasa daga jikin nasa yasa hannu ɗaya ya tallabota tare da juyota garesa, face ɗinta ya zubawa idanu yana kallan yadda ta datse nata idanun tana jiran ta ji ta isa ƙasa. Yau yabon da ta yi mashi ne ya sanyaya mashi rai har yasa ya ceceta bai bari ta kai ƙasa ba, dama ransa tun jiya a ɓace na juya mashi baya da mutanensa suka yi.

Kurawa juna ido suka yi gabaɗaya kamar sun mance a wani duniya suke, sun shagala da kallan juna gangar jikinta ya gaza iya jurar tsawuyar da ta yi ɗin, dan kusan a iska take, bayan wuyarta ya tallabota da hannunsa. Kerma kafafunta suka fara yi a in da ta yi ƙoƙarin zubawa ƙasa, cikin zafa ya fisgota mai gabaɗaya ta tafi ta faɗa saman lion chest ɗinsa, yasa hannunsa ɗaya ya tallabi tsakiyar bayanta. Like wow, abin da bata taɓa expecting zai yi mata ba, wai ya taimaketa, bata taɓa zata ba, sai ga shi ya yi hakaɗin sanadiyyar daɗaɗan lafuzanta a kansa, abin fa ya yi mashi daɗi ne sosai, sai dai shi ba'a gane farincikinsa ko bakincinsa shiyasa bata wani gane sosai ba.

Hannunta É—aya ta É—aura a saman lion chest É—in nasa ta gefe, dan dikkanta bata gama cike rabin faÉ—in kirjinsa ba, Æ´ar karama a gabansa. So sai ta É—aura hannunta a gefen chest É—in nata, a hankali ta É—ago da kanta dan ta kalli face É—insa, ya kura mata idanu yana yi mata kallan kurillah. Habawa sarkafewa idanunsu ya yi cikin na juna kamar É—azun. Sun É—an jima a haka kafin ya yi gaggawar kawar da kallansa a kanta tare da saketa, kamar wani mara gaskiya ya juya da sauri ya nufi clothes set É—insa. Bin bayansa da kallo ta yi har ya shige cikin wajen, ajiyar zuciya ta sauke, cikin natsuwa ta taka ta isa gaban sofars É—insa, saman É—aya ta zauna, tsabar laushi har lumewa da ita ya yi, tagumi ta É—an yi tare da afkawa duniyar tinani, faÉ—i take yi a ranta ta fara yin nasara, ji take yi sun kusa canza zuciyarsa, amma ita dik a tinaninta yafewa mutanen birnin da Ronnie ya ce mata ya yi ne take ganin sun fara nasara ba. Uhm akwai sauran aiki a gabanki Sweetie, dan wannan mai black heart É—in kam bai ji komai a ransa ba.

Zaman good 10 mins ta yi a wajen kafin ya fito shirye cikin sleeping dress ɗinsa, yana fitowa ta miƙe tsaye tana kallan irin kyan da ya yi cikin wannan kaya, dai'dai lokacin kuma aka turo kofar ɗakin aka shigo..... A hanzarce ta kai kallanta wajen kofar nasa dan ganin wanene?. Wasu..................

Dama a karshen littafin nan na yi maku alkawarin baku wasu addu'oi na mallakar zuciya ko? Da na yi niyya sai a kashen littafin, amma duba da ramadan ya gabato, a cikin Ramadan ma buƙata zata fi saurin biya yasa nace bari na baku the most important ɗin, ku yi shi a cikin watar Ramadan, ki yi shi da kyakkyawar niyya, ina uwa da ɗanta yake zinace zinace, yake yawace yawacen banza bin abokan banza da shaye shaye? Ina mata masu shan wahalar namiji? To dik dai ku matso, ku yi shi da tsarkakakken niyya sosai

Da farko dai zaki yi. Astaghfirullaha Rabbi min kulli zambin wa atubu ilayh kafa É—ari dai'dai, sannan ki yi salati ga annabi kafa goma. Amma fa sai kin yi alwala, zaki iya farawa karfe sha biyu na dare, za kuma ki iya farawa karfe 2 na dare, idan kin yi alwala kika yi sallah raka'a biyu, sai ki zauna, ki gabatar da abin da na faÉ—a a farko, sannan ki yi salati, ga salatin ma a rubuce ga waÉ—an da basu iya ba. Allahumma salli ala Muhammadin wa ala ali Muhammadin, kama sallayta ala Ibrahima wa ala ali Ibrahima innaka Hamidum Majid. Bayan kin yi wannan sai ki gyara zama sosai a kan dadduma, ki É—aga hannayenki sama ki fara addu'ar kamar haka.

Allahumma aslih zawji ( sai ki ambaci sunansa, wato suna da kike yiwa ɗin kenan) waj’alhu min as salihin, waj’alhubniyyatahu nafi’atan lid duniya wa akhirati. Da kyakkyawar niya fa, ki sanya a ranki tamkar Allah ya gama biya maki buƙata, ki ji cewa bayan Allah babu wanda zai yi maki. Sai Rabbana hablana min azwajina wa dhurriyyatina qurrata aƴunin waj’alna lil-muttaqina imama. Wannan addu'a tana da mahimmanci kowace uwa ta kasance tana yi, yana cikin Suratul Furqan. Sai Allahumma inni as’aluka an tahdi zawji ila sabilika al-mustaqim, wa an tub’idahu ‘an ma yughzibuka, wa an taj’alahu min ahlil taqwa wal istiqama. Wannan addu'oi masu tsadar gaske ne, idan kika yi sho da tawali'u zaki sha mamaki, zaki gode mun kamar babu gobe. Sai Allahumma inni a’udhu bika min jahdi al bala’ wa su’il qadha’ wa shamatati al a’da’, wa min kulli sharrin dhahirihi wa batinihi. Wannan addu'a tana matuƙar kariya daga dik wata sharri na abin halitta, wannan ba dan miji ko wani zaki yi ba, kanki zaki yi wa dan Allah ya kareki, amma zaki iya yiwa kowa yaki dan ya shiga kariya, wlh wlh wlh addu'a ce mai karfin gaske. Tsarin yin wannan addu'oi dama kwanaki 40 zaki ɗauka kina yinsu cikin dare bayan kin yi sallah raka'a biyu, kinga ga Ramadan ya zo, zali samu saukin tashi ki yisu, sai ma buƙatunki sun fi biya, shiyasa na baku a yanzu dan ku yi da ramadan, saura sai mun haɗu a karshen littafin, saura wata budurwa ta je ta yi wa sarauyinta ta zo ba aurensa zata yi ba, wlh babu ruwana, ya Allah dik wanda ba da kyakkyawar niya zata yi wannan addu'oi ba Allah kada ka amsa mata, dan ba da ni za'a cutar da wata ko wani ba!!.
Chapter 170 · 0% Book details