← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 242

Sashe 74

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

SHIKENAN KIN HAƊA SABULUNKI, IN SHA ALLAH ZAKU RINƘA SAMUN SANA'O'IN DA ZASU RINƘA YI A CIKIN GIDA DAN TSIRA DA MUTUNCINKU WANDA KUMA JAMA'A ZASU SAYA, DAN DIK KAYAN AMFANI WAƊAN DA AKE AMFANI DA SU YAU DA GOBE ZAN KOYA MAKU, WAƊAN DA DOLE ZA'A SAYESU DA AMFANI.

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
=========🔥🔥🔥===========

MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

19

••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

KINGDOM OF POWER.

Zaune Momma, Mama Haulat and aunty MieMie suke a parlourn momma, mama Haulat tana zaune a ƙasa, Aunty MieMie da momma a saman sofa, babyn Khadija yana rike hannun momma, ya sha kwalliya cikin wasu irin kayan sanyi masu bala'in kyau wanda momma da kanta tasa uncle Taheer ya je shopping ya saya mata su, kayan baby dayawa ya sayo mata, yaro sai sakawa yake yana kara canzawa abinsa, har ya murmure, amma matsalar ɗaya shi ne bai samu nonon uwa ba, ko sau ɗaya bai ɗanɗana ba, Allah sarki.

Cikin sanyin murya momma ta fara magana tana kallan Aunty MieMie. "Raeesa kamar yadda na faɗa maki cewar wannan yarinya matar Jaish ce to hakan take, yau da safe na same shi a bedroom ɗinsa domin muyi maganar da shi, sai ya nuna mun shi wlh baya santa, hasali ma ba zai taɓa zama da yar kauye wadda bata yi karatu ba, ya nuna baya santa kuma ba zai taɓa santa ba, har da ce mun shi bashi da lokacin mace a yanzu, shi ma daddynku ya kafe a kan bayan santa, wai sai dai a warware wannan aure".

ÆŠan zaro idanu Aunty MieMie ta yi, cike da mamaki ta ce. "Amma kuma momma menene laifin yarinyar nan da zasu ce basa sonta?". Allah sarki, ita Aunty MieMie ko kaÉ—an bata ji kyamarsu Mahreen ba, wato mufa Nigerians dik in da muke mun fita daban, jinin É—an Nigeria musamman É—an arewa ci wlh baya kyamar kowacce yare da kabila, zama muke da kowa da zuciya É—aya, sai dai a nuna mana kabilanci da wariya, amma mu bana nunawa, kowa É—aya muka É—aukesa, lallai ya tabbata jinin Nigerians na gudu a jikin Aunty MieMie, jama'a ku tafa mata, bata bar gida ba baiwar Allah.

"Hmmm shi dai Jaish kin ji dalilinsa, wai saboda yar kauye, yar datti, ba karatu ce yasa baya santa". Cewar Momma kenan.

ÆŠan siririn tsaki Aunty MieMie ta je. "To shi kuma daddy menene dalilansa na kinta?". Cewar Aunty MieMie.

Shiru momma ta É—an yi, can kuma sai ta ce. "Saboda kin san halinsa ai, wai akwai qualities da yake sanwa Æ´aÆ´ansa a matan da zasu aura".

"To yaga ita Mahnoor É—in ne da zai ce bata yi ba?".
Kai momma ta girgiza mata kafin ta amsa da. "A'a bai ganta ba tukun nan, na dai ce ya bani sati guda zan kawota ya ganta, in ya ganta sai ya yanke hukunci".

Shiru suka yi Aunty MieMie tana tinanin mafita.

Katsesu momma ta yi da cewa. "To shi ne yanzu nike san mu yi shawarat ta yadda zamu haɗa mata dik wasu qualities ɗin da suka dace ta yadda idan ya ganta zai bada goyan bayan Jaish ya zauna da ita, ni bani da matsala ta ɓangaren Jaish, dan nasan ba zai saɓa umarnina ba, matsalar daddynku ya aminta da ita ne kawai, kunga idan aka raba auren nan magana ta domin Allah an cutar da yarinyar nan da iyayenta, bana jin kamar ko shekaru 15 ta cika, sannan dik bama wannan ba, Mahnoor ta dace a matsayin matar Jaish wlh, iyayenta sun yi mana halacci na wuce misali, bai kamata mu saka masu da sharri ba".

Jinjina kai Aunty MieMie ta yi, tabbas dik abin da momma ta faɗa gaskiya ne, bai kamata a yi wa Mahnoor wani abin da ba dai'dai ba, domin yarinyar ta kai dik wani matsayin da ake buƙata matar Prince ta kasance, ta cike dik wasu qualities, ilimin bokon ne dai kawai ya rage mata wanda shi dama ai ba dashi ake zuwa lahira ba, bai zama wajibi ba, rashinsa ba zai hanata zaman aure da kyautatawa mijinta ba, ta samu babban wato ilimin addini, dik wasu abin da ake koyarwa a bokon tushensu daga inane? Dik daga litattafan addini ne, dan haka Mahnoor bata da wata gazawa. Iya shege ne kawai irin na Jaish.

"Ranki ya daÉ—e zan iya yin magana?". Cewar mama Haulat dake binsu da kallo....... Jinjina mata kai alamar e Momma ta yi ba tare da ta yi magana ba.

"Ni a ganina tin da haka ne ai matsala ce mai sauki, sai mu gyarata, ta sha gyara sosai, a samu wanda zai fara koya mata karatu Kafin wani ɗan lokaci, ta goge ta canza, In Sha Allah zai sota, kuma shi ma mai martaba zai kaunaceta ya karɓeta a matsayin sirika".

Jinjina kai Aunty MieMie ta yi tare da cewa. "Wannan shawara ce mai kyau, sai dai kuma ina da kari a kan shawarar".

Zuba mata idanu momma ta yi alamar tana sauraronta kenan.

Cigaba ta yi da cewa. "Momma kada ki sake yi wa Jaish maganarta, tun da kin bawa daddy sati É—aya, to a cikin wannan sati É—ayan kada a yi magana da kowa, mama Haulat ki gyara mana ita, sai ki fara koya mata wasu abubuwan da suka dace dan kauyancin nan da rayuwa kamar na dabobi ya fita a kanta, kun san idan nan da sati É—aya aka kaita gaban daddy ya aminta da ita to a bisa doka daga ranar zata koma part É—in Jaish, sannan zata zamana ita kaÉ—ai alhakin kula da cinsa da shansa zai rataya a wuyarta, kun san yadda doka yake babu wadda zata sake kusantar abin da ya danganci cinsa, shansa da wasu privacy nasa ko?".

Jinjina kai mama Haulat ta yi, ita kuma momma still dai tana binta da ido bata furta word ba.

Cigaba ta yi da cewa. "Dole za'a haÉ—ata da mama Haulat a part É—in nasa dan ta tayata yakarsa, kun san halin Jaish da shegiyar murÉ—iya, mama Haulat ai É—an É—akinki ne shi kin san halinsa, dan haka ke zaki É—aurata a hanyar da ta dace domin ta tabbata a matsayin matarsa ya kuma sota, dan haka wannan ragama mun rataya maki shi a wuyarki ko ya kika ce momma?". Ta kai karshen maganar tana tsayar da idanunta a kan momma.

Jinjina momma ta yi, sannan ta ce. "Tabbas wannan shawara ta yi, yanzu Haulat ki dage kafin nan da sati guda ki canza mun ita, ta yi kyau sosai, idan Allah ya É—oramu a kan daddynsu muka yi nasara sai ki bita part É—in Jaish É—in kina cigaba da koya mata abubuwa da yi mata gyara, ban yarda da wata kuyanga da ta shiga lamarinsu ba face ke, da ke kaÉ—ai na yarda a gidan nan, nasan zaki kula da su dikkansu biyu, kin san abin da yake so da wanda baya so, dan haka sai ki É—aurata a kan hanyar da ta dace, wlh ina san Jaish da wannan yarinya, ban san dalili ba".

Cikin girmamawa mama Haulat ta karɓi wannan ragama da suka bata tare da tambayar ko akwai wani abin da za'a ƙara sanar da ita?. Aunty MieMie ce ta amsa mata da babu komai zata iya tafiya ta je ta fara aikinta daga yanzu, wato ta je ta ɗaukesu izuwa wajen gyara yanzu kenan, tare da Mahreen za'ayi masu komai dan a ragewa Mahreen ɗin ma wannan hauka da yake a kanta.

Miƙewa mama Haulat ta yi ya nufi waje tana yi masu addu'oi masu tasiri da ratsa zuciya.
Tana fita uncle Jahiz ya shigo bakinsa ɗauke da sallama. Zeezee tana biye da shi a baya, dama Aunty MieMie tana ƙoƙarin ɗaukowa momma zanjen babyn nan dake kama da shi ne sai ga shi ya shigo.

Dan haka cikin girmamawa suka gaisa. Saman sofa mai zaman mutun biyu ya zauna tare da umartan Zee da ta zauna a kusa da Aunty MieMie.

Kin yarda ta yi, ta zauna a ƙasa tana sunkuyar da kai, ta ji sauki sosai jiki ya yi kyau Masha Allah, ita dai ta samu sallama, saura Khadija da mai keken napep ɗinsu da shi ma ya farfaɗo yana ta fama da nashi jinyar bawan Allah.

Zee na ƙoƙarin zama a ƙasa idanunta suka hango mata babyn Khadija dake hannun Momma, ai kuwa zubur ta miƙe, ita da bata san a ina take ba, bata san ba a gidan wargi take ba, bata san a gidan sarauta masu izza da ji da kansu take ba, sai ta miƙe a zabure tare da nufar momma da nufin ta kwace babyn.

Tsawa Aunty MieMie ta daka mata tana faÉ—in basa san shirmen banza, ita bata san a gaban wa take bane? Gaban princess Rahilarh take, dole ta nitsu ta jira komai sai an bata izini, su sarauta ba'ayi masu irin wannan wautar.

Shi ma uncle Jahiz dama ya buÉ—e baki zai dakatar da ita daga tinkarar momma É—in ne sai Aunty MieMie ta rigasa, dan haka sai ya ja bakinsa ta datseta cif.

Allah sarki Zee, jikinta sai rawa yake yi, burinta ta karɓi ɗanta ɗan ƴar uwarta, yau sama da sari biyu kenan tana rokon da abata shi ta ga jininta, amma bata samu dama ba, ta tsumu da san ganinsa har ta gaji, kullun idan uncle Jahiz ya je dubasu sai ta yi mashi kukan ina yaronta, yau dai da aka basu sallama sai ya ce ta zo su je ta ga ɗanta, shiysa yanzu da ta gansa ɗauki yasa ta rasa nitsuwarta, ta rasa control ɗinta, kuma ya haɗu da bata san a gaban wa take ba, shiysa ta yi saurin miƙewa zata je ta karɓesa, shi kawai idanunta yake hango mata, sam bata ga su momma ba baiwar Allah.
Chapter 74 · 0% Book details