Sashe 13
Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Idan Sweetie ta kurma ihu sai ya ji hakan a cikin ransa, amma sam bai kawowa ransa ita ce take cikin damuwa ba. Pastor na jawabi babu abin da kunnuwansa suke iya É—auko mashi, idanunsa dai yana a kan pastor, amma baya sauraronsa.
Da wani irin karfi na ban mamaki wannan chandelier ya nufeta tsaye a jikin bango tana ihun neman taimako. Lokacin guda da chandelier ya kusa isa gareta ya riƙiɗe ya zama wani irin kaifaffen wuƙa mai dafin bala'in, hasken dake fita daga jikin wannan wuka sai da ya sanyata kanƙantar da idanunta.
Kan wukar ta zanen bakar damusa ce, hasken light blue ne yake fita daga dik wata kusurwa na jikin wukar.
Kai tsaye wuyar Sweetie wukar ya nufa, da karfi kuma. Wani irin razanannen ihun ta saki mai doÉ—e kunnuwa, bata da madogara, ba hanyar gudu, tana ji tana gani zata mutu.
Ganin cewa wuyarta wanna wuƙa ya nufa yasa ta kai hannayenta ta tare wuyar tata tana ihu, sai dai a wannan karon bata datse idanunta ba.
Tana tare wuyarta da hannunta unexpect taga wani haske ya fito daga cikin hannunta ya nufi wanna wuƙa, nan take wanna haske ya dakatar da wukar a dab kusa da ita.
Ya ilahi ya lilliahi, ai sumar tsaye ta yi tana kallon hannunta, her first time seeing that she has a unknowing magic, she was so surprised!.
Kamar wata wadda aka zarewa ruhi, ido ta kara zarowa tana ganin yadda hasken hannun nata yake tamkar light aka kunna, abin ya yi mugun É—aure mata kai, tana son ta motsa hannun nata ko wani sassa daga jikinta amma ta kasa, dik sai ta ji jikinta ya yi mata nauyi sosai.
Kafafunta ne suka fara gaza iya ɗaukar gangar jikinta, hakan yasa ta ɗan yi tangal tangal kamar zata faɗi. Wannan tangal tangal da ta yi yasa hannunta ya ɗan motsa, hakan ya haifar da motsawar wannan wuƙa da a yanzu yake ƙarƙashin sarrafawar hasken hannunta.
Kara zaro idanu sosai ta yi tana kallon wanna abin al'ajabi. Da kyar da suɗin goshi ta iya kama kanta bata zube ƙasa ba. Har lokacin iska mai karfin nan dai yana cigaba da kaɗawa a cikin ɗakin, Black Tiger yana cikin wannan iskar, ya zuba mata idanu ne yana kallon gudun ruwanta, amma kuma ya yi matuƙar mamakin karfin irin na magic ɗinta da har ya iya tare wannan wuka da ya turo mata bai huda fatar wuyarta ba.
Idanunta a kan wukar, cikin karyewa da sanyin gaɓɓan jikinta ta yi iya ƙoƙarinta wajen motsa ɗan hannun.
Tana motsa shi ma wanna wuƙa ya motsa, dik in da hasken hannun nata ya bi wanna wuƙa ma yana bi, a hankali ta fara matsar da hannunta daga wuyarta, hakan yasa shi ma wukar ya matsa daga saitin wuyar tata da ya yi.
Abin al'ajabi ya bata matuƙa, sai kuma kamar wata zararriya ta saki murmushi wanda sai da yasa dimple ɗinta bayyana, ko me abin murmushi a wajen?.
Ajiyar zuciya ta sauke ganin tana da hanyar cetan kanta, fara ƙoƙarin tabbatarwa da kanta hakan ta yi ta hanyar juya hannunta ta in da takeso.
Dik yadda ta juya wukarma sai ya juya ta nan, wani irin dariya ta fashe da shi kamar wata zararriya.
Yi take yi babu kakkautawa idanunta a kan wukar.
========================💔
Lokacin guda kuma ta tsayar da dariyar tata cak, kome ta tuna? Sai kuma idanunta suka ciko da kwallah, a hankali ta furta.
"Innalillahi wa Inna ilahir rajiun, Hasbunallahu wani'imal wakil, ya Allah.........."
Bata kai karshen maganar da take son amayarwa ba kenan taga wanna wuƙa ya faɗi a ƙasa, faɗuwarsa ke da wuya ya haifar da wani irin sauti mai ban tsoro, a take guguwar dake ɗakin ta kara karfafa kamar an watsawa aljanu ruwan addu'a yana konasu.
Ba ƙaramin kara razana ta yi ba, da karfi ta furta. "Wayyo Allahna ka kawo mun ɗauki......"
Ai bata gama rufe bakinta ba kofar ɗakin ya ɓalle ya buɗe kansa da kansa. A miliyan ɗari ta kwasa ta nufi waje, ta kasa gane cewa sunan Allah da ta ambata a wajen ya rikita dik wani tsafi dake waje, shiyasa take jin wanna guguwa ta kara karfafa wai dan su kare kansu daga kalamanta shi ne suka kara karfin iko.
Kai tsaye parlourn ƙasa ta nufo tana ihu, bata tsaya electric stair case ɗin ya yi kasa da ita ba ma, da kanta ta tattake shi ta yi ƙasa.
A wanna lokaci ta kasa iya sake ambatar sunan Allah, abin ku da shaiÉ—an da kuma shirka.
Bayanta Black Tiger ya biyo cikin wanna iska, dan ransa ta kara bakanta na sunan Allah da ta kira ta jijjiga mashi hankulan ruhohin tsafinsa. Ya sha alwashin yau zata gane kurenta.
Wanna iska ne yasa gabaɗaya kofofi da windows ɗin parlourn kasa suka rufe kansu, fara ƙoƙarin kamata Black Tiger ya yi, ihu take kurmawa tana neman hanyar tsira.
A wannan lokacin ne ya riƙiɗa ya zama mutum, da ainahin face ɗinsa ya bayyana, yana sanye da pj a jikinsa.
Like wow, kamar wani kafani, kaman ba mutum ba, ga shi ya juya idanunsa izuwa na magic, sai ya kara riƙiɗewa kamar ba mutum ba, zallar madarar kyau.
Cak ta dakata da neman hanya da take yi, bata yi zaton shi bane da ba zata gudu ba a cewarta, ita da take son ganin face É—insa daman! Ai da tsayawa zata yi kome zai faru ya faru.
His first time kasakcewarsa a cikin wanna parlon, bayan ɗakin Ronnie da yake kai ziyara ta hanyar magic bai taɓa fita ko ina ba, yau karo na farko Sweetie ta sanya shi fitowa.
Ita ce mutun ta farko da ta fara ganin face ɗinsa bayan babansa, and ita ce mutun ta farko da ta fara sanya shi fitowa har parlon ƙasa, lallai ya tabbata idan bai tsaya ya bada himma ba zata iya cin nasara fa a kansada gaske.
Zuba mashi idanu ta yi tana kallonsa, face É—insa babu alamar mutumci ko kaÉ—an, zallar mugunta ce a samanta, in ka gansa sai ka razana, amma yarinyar nan Sweetie ko a jikinta, bata ji tsoron ganin cikin idonsa ba.
Wani irin ihu mai sauti na ruhohin tsafinsa ne ya fara karaÉ—e ko'ina a cikin parlon, hakan ya ja dikkansu biyu suka É—an yi shock, abin ya bashi mamaki jin wanna ihu.
Cigaba da kura mashi kallo Sweetie ta yi tana mamakin hali irin nasa, ga shi kyakkyawa amma kyan ɗan maciji ne, ɗan kunama!. Shi kuma gabaɗaya hankalinsa ya koma a kan sautikan da yake ji wanda ita Sweetie bata iya jiyo hakan, da yake ta ɓangaren tsafinsa ne, shi kaɗai yake ji.
Can kamar saukar aradu haka ya tsinkayo wata iriyar murya mai tashin kai, mai kuma karfin gaske cikin guguwa da kuwa, tamkar muryan kartin maza ya ce.
"Autan duniyoyi ya bayyana, Autan ruhohi ya bayyana".
Shi ne abin da yake fita daga wanna sauti.
Jin haka yasa ya tuna wasiyar babansa na karshe a idan yake ce mashi.
"Wasiyata a gareka shi ne, kada ka yarda ya fita waje dik rintsi dik kuma wuya, kai ba kamar kowani mutum kake ba, kai ruhin ruhohine, autan duniyoyi ne, jagoran rundunoni ne, gatan manya manya ruhohi ne, nemanka suke yi kamar hauka, kai ɗan baiwa ne, da baiwa aka haifa mun kai, wanna dalilin yasa suka mayar da kai autansu, ni kuma ban yarda da hakan ba, saboda nasan me hakan yake nufi, wanna dalilin yasa na baro duniyar shaiɗanu da kai tin kana karami baka wuci 5 years ba, wannan dalilin yasa ban taɓa barinka kaje wani waje ba, saboda fitarka zai sa DUNIYAR SHAIƊANU su shaida in da kake, bana son su rabani da kai! Kada ka fita daga Black world har sai ka tara karfi sosai wanda zaka iya sanya barazana da tsoro a cikin zuƙatan DUNIYAR SHAIƊANU, wanda karfin ikonka zai iya sanyawa ka kwaci kanka daga ɗaukarka da zasu zo yi...............".
"Ka tara karfin iko mai karfin gaske ɗana, na jima ina karɓar yaya maza daga hannun matan garin nan ina sanyawa ana basu horo dik dan na yi maka tanadi ɗana, ka cigaba da horar da su dan su zame maka bayi masu bada rayukansu a kanka!!".
A lokacin da babansa yake yi mashi wanna bayanai hankalinsa baya'a jikinsa, a lokacin yana tunanin rashin lafiyar baban ne kawai, bai ɗauki zancen da wani muhimmanci ba, and bayar ɓacewar baban daga fuskar duniya bai sake tunawa da zancen ba sai yanzu.
============💘🔥===========
FOREST NE. Wajen yana cikin tsakiyar dokar daji mai cike da bishiyoyi masu girma, wadanda ganyensu suna rufe hasken rana. Akwai hayaniya mai ban tsoro kamar kuka na tsuntsaye da dabbar da ba a iya ganinta.
Duwatsu da Tsaunika. Duwatsu sun kewaye wajen, suna ɗauke da layuka masu kama da alamomin tsafi, suna haskawa da ɗan wuta mai launin kore. Tsaunukan suna da tsayi, kuma akwai tsallake-tsallake na ruwa mai fitowa daga saman tsauni yana ƙara tsoratarwa.
Babban kogon dutse shi ne cibiyar wajen matsafan. An yi ƙofofinsa da baƙin duwatsu mai siffar fuskokin aljannu. Jikin kogon yana ɗauke da rubutun tsafi a harshe da ba a fahimta. A ƙofar akwai fitila masu kunne da harshen wuta mai ruwan zuma da jajaye.
======CIKIN KOGON DUTSE=======
Ɗakuna Tsafi. Babban ɗaki ne da ke tsakiyar kogon, yana da stage mai ɗauke da kayan tsafi, kayan al'ajabi, kwalabe masu kunshe da ruwa mai launi, ƙananan gumaka, da wukake masu ban tsoro.
Ɗakin Hada Magani. A cikin babban ɗakin yake shi ma ta gefe guda. Cike yake da tukwane masu hayaƙi, ganye iri-iri, da fararen ƙasusuwa. Akwai ƙanshi mai kaɗaici da hayaki mai ɗan duhu yana tashi daga cikin tukwanen.
Ɗakin Ajiya. Wannan ɗaki yana da duwatsu masu haske kamar gold, manyan littattafai na tsafi da aka ɗaure da sarƙoƙi, da wasu abubuwan al'ajabi kamar ƙwayoyin ido da ƙananan gumaka.
Ɗakin Ƙulle-ƙulle. Wannan ɗakin yana da tagwayen layukan duhu a kasa, fitilu masu koren wuta, da gumaka masu kama da halittun ban tsoro suna kewaye.
Tsarin Haske. Hasken daga fitila ko wutar tsafi shi kadai yake cike kogon, kuma wutar tana ja da baya idan mutum ya matso kusa.