← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 242

Sashe 21

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karfe 7 dai'dai Ronnie suka dawo daga church, yana san zuwa ya ga Sweetie amma ya fi san ya kai ga yayansa a farko, dan haka a bakin kofar room É—insa suka rabu da Floris, ita ta shiga ciki shi kuma ya wuce part na Black Tiger.

Ya ɗauki a kallah 30 mins a ciki, can ya fito sanye da hoodies masu balai'n tsada a jikinsa, ya yi matuƙar kyau, da alama a part ɗin ya yi wanka, da yake yana da hasken fata sosai sai black color tana bala'in yi mashi kyau launin kayan kenan.

Dab zai shiga room É—insa ya tsinkayo muryar Floris da Sweetie suna magana, É—an dakatawa ya yi dan ya ji me suke faÉ—a.

"Kina nufin kin san Jesus?". Cewar Floris. Ta yi maganar mamaki sosai a saman face ɗinta, dan suna dawowa daga church ta yi saurin karisawa wajen Sweetie, a shirmenta wai bari ta yi saurin fara koyawa Sweetie addininta dan ta rinjayeta, shi ne da ta fara magana a kan Annabi Isa (A.S) sai Sweetie ta ce mata ta san shi ai, abin ya bata mamaki matuƙa. Sai ta samu wajen a bakin bed ta zauna dan ta ji daga ina Sweetie ta san Jesus?!.

Jinjina kai Sweetie ta yi tare da amsa mata da. "I think mu musulmai ma mun fi ku sanin wanene shi! Kai bama i think ba, mun fi ku sanin wanene shi menene tarihinsa na hakika!".

Sanya password Ronnie ya yi a kofar ya buÉ—e, dan yana san ya ji hujjojin da Sweetie take da shi da har take magana with full confidence a kan addinin nan nata yana san kureta.

A tare suka dawo da kallonsu a kansa tin da ya shigo, zama ya yi saman egg-s chair dake fuskantarsu, ya harÉ—e hannaye a saman kirjinsa yana binsu da kallo.

"Beb ka ji Sweetie wai ta san Jesus fa!". Cewar Floris da bata yarda Sweetie ta san Annabi Isa or ta fita saninsa ba!.

Kallonsa a kan Sweetie da ita ma take kallonsa. "A ina kika san Jesus bayan ba addinin nin mu kike ba?".

Kamar baya san yin magana ya yi ta, kuma shi ma yanzu yana san kure Sweetie ne, saboda ya ga confidence É—inta ya yi yawa, gara su kureta su gani.

"A malamullah mai tsarki wato Alqur'ani, a nan nasan shi, shi ya zo mana da tarihinsa gabaÉ—aya har ta dalilin da yasa kuke ce mashi Allah, wasunku su ce mashi É—an Allah".
Ta bashi amsa cikin halin ko in kula bare har ta wani damu.

"Wanene Jesus?". Ronnie ya wurga mata tambayar dan ya kureta, su ji shin da gaske ta san shi ne ko dai cika baki ne kawai, basu yarda da ana yin karya a duniya ba, dan basa yi, amma a kan wanan magana sun fara tunanin kamar san zuciyarta kawai Sweetie take faÉ—a, sunga kamar tana san janyesu izuwa addininta ne ba tare da wani hujja ba!.

Miƙewa tsaye ta yi cike da jin daɗin tambayoyinsu a gareta, dan dama so take su bata dama ta yi masu bayani game da hujoji domin ta samu Allah ya taimaketa ta tsiratar da su daga duhun kafurci izuwa haske da rahma. Tambayar Ronnie ya yi mata matuƙar daɗi sosai, sai ta ji tamkar ice block ya manna mata a kirjinta.

Jingina da jikin wall ta yi tare da harÉ—e hannayenta a kirji, dikkansu idanunsu a kanta suna jiran bayaninta.

A nitse ta fara magana one by one with full confidence.
"Jesus wato Annabi Isa manzon Allah ne, yana ɗaya daga cikin manya manyan manzanin da Allah ya turo masu riƙe da litafi, shi ne annabin da aka turowa bani Israela wato yahudawa, shi ne ya zo da littafin injila wanda a yau kuke kiranta da Bible domin isar da saƙon Allah zuwa ga bani Isra'ila................"

Katseta Ronnie ya yi da cewa. "Ta yaya Jesus ya zo duniya? And yana da baba ko bashi da shi?".
All his though ya É—aureta a wanna tambaya, dan da wanna suke amfani a koda yaushe su danganta annabi Isa a matsayin É—an Allah, idan ta bashi amsar Annabi Isa bai da baba kunga ya samu damar kara karfafa cewa É—an Allah ne shi.

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce. "Da ga kai har Floris kada wanda ya sake katse mun maganata, zan yi maku bayani a kan wanene annabi Isa (A.S) dallah dallah, dan da alama ku baku san ainahin wanene shi bama, so yakamata ku san shi da kyau ku kuma san in da kuka dosa!!"......... Tashin sense.

Ko tsoronsu bata ji ba ta gaya masu hakan, idanunta a kan Ronnie da yanayin face ɗinsa ta fara canzawa izuwa na ɓacin rai, ita kam Floris tuni dama ranta ya gama ɓaci, ta ya Sweetie zata ce masu basu san Jesus ba? Wannan ma ai rainin wayo ne!.

Ko kaɗan bata damu da ganin sun ɓata rai ba, ko a gefen takalmarta, cike da kwarin gwiwa da yakinin in ta yi masu bayani zasu fahimta ta fara magana kamar haka.

"Annabi Isa (A.S.), wanda ake kira Yesu Almasihu a Kiristanci, yana daga cikin manyan annabawan Allah da Musulmai da Kiristoci ke girmamawa, kowane yana da fahimtarsa kan tarihinsa da matsayinsa".

"Tarihin Annabi Isa (A.S.) a Musulunci". Idanunta a kan Ronnie take wannan magana ko shakkarsa babu bare tsoronsa.

"An haifi Annabi Isa ta mu’ujizar Allah ba tare da uba ba, mahaifiyarsa Nana Maryam tana cikin tsarkaka. Wannan lamari ya faru ne saboda umarnin Allah don ya zama alama ga duniya a cikin Suratul Maryam shafi na 19 aya ta 16 zuwa 34 a nan wannan bayani yake!"

"Annabi Isa ya zo da sakon tauhidi, yana kira mutane su bauta wa Allah shi kaɗai, ya kuma tabbatar da shari'ar Annabi Musa (A.S.). Ya kuma kawo mu’ujizai da suka haɗa da warkar da kurma da makafi da maido da matattu bisa iznin Allah".

"Matsayinsa a Musulunci. Musulmai ba su dauki Isa (A.S.) a matsayin Allah ba, sai dai matsayin annabi kuma manzon Allah. A Musulunci annabi Isa ba kasheshi aka yi kamar yadda kiristoci suke tunani ba! Allah ya É—aukaka shi zuwa gareshi wato sama, cikin Suratul An-Nisa shafi na 4 aya ta 157-158 Allah ya yi magana akan hakan!"

____________________🪐💘

"Dalilin Da Yasa Wasu Suke Bauta Masa a Kiristanci. A cikin Kiristanci, Yesu ana É—aukarsa ÆŠan Allah, kuma Kiristoci suna ganin shi a matsayin cikar alkawarin Allah ga Æ´an Adam don cetonsu daga zunubi ya kaisu ga rahma!. Kiristoci suna ganin nassoshi da aka rubuta a Littafinsu suna nuna cewa Yesu shi ne ÆŠan Allah wanda aka aiko domin ya mutu don zunuban duniya, sannan ya tashi daga matattu, malamansu sun gaya masu irin mu'ujizozinsa hakan yasa suke ganin ya kai ya zama É—an Allah, saboda ya tada matattu ya kuma warkar da marasa lafiya bisa umarnin Allah. Wannan shine tushen imaninsu kiristoci".

"Wasu Kiristoci suna daukar Yesu a matsayin wani bangare na Ubangiji. Wannan akidar ta samo asali daga fahimtar su game da littattafan Injila ko in ce Bible É—insu na yanzu!".

"Nasan zaku yi mamaki idan nace maku Bible da kuke karantawa a yanzu ba shi ne wanda Annabi Isa ya zo maku da shi ba, and canza maku shi tsawon dubbanin shekaru, amma bari in yi maku bayani yadda zasu fi fahimta da kyau, bari in banbance maku Alqur'ani mai girma da kuma injila haÉ—e da Bible É—inku na yanzu, bari ku ga banbancin sai ku fidda na gaskiya".

Ta kai karshen maganar tana sauke ajiyar zuciya. Daga Ronnie har Floris babu wanda ya sake tofa ko uppan, sun tsareta da idanu, sai dai dikkansu ransu ya sosu na yadda take ƙoƙarin karyata malamansu da kuma littafinsu, amma sun kasa kunne dan su ji hujojinta.

Cigaba da yin maganar ta yi cikin tsanaki yadda komai doɗewar kwakwalwar mutum sai ya fahimci zancenta tsaɓ!.

"Bambanci Tsakanin Injila da Al-Qur'ani Mai Girma, and Bible".

"Injila wanda Annabi Isa (A.S.) ya kawo shi ne wahayi daga Allah, wanda aka yi niyya ga bani Isra'ila a lokacin. A Musulunci, an san wannan da Injil, amma ba wannan ba ne Littafin Bible da Kiristoci ke amfani da shi a yau. Littafin da Kiristoci ke kira Bible an haɗa shi ne daga rubuce-rubuce daban-daban, ciki har da Tsohon Alkawali da Sabon Alkawali, wanda yawanci ya ƙunshi tarihin Annabi Isa da wasikun manzanni, ba asalin Injila da Allah ya saukar ba, tarihin mu'ujizar Annabi Isa ne suka cika cikin Bible na yanzu, shiyasa kiristoci suka zage a kan lallai Annabi Isa Allah ne tun da zai iya raya matattu, ina da yakinin da anbawa kiristoci ainahin littafin da Annabi Isa ya kawo masu domin su san girman Allah to da tabbas yau za'a wayi gari babu Christians ko ɗaya a duniya, da zasu san girman Allah su san kuma dik abin da Annabi Isa ya aikata dan gane da mu'ujizarsa to Allah ne ya umarcesa ya kuma yassare mashi yin hakan, amma an ɓoye masu gaskiya an barsu cikin ɓata!".

Ɗan dakatawa ta yi da maganar tana jan numfashi, tabbas ta lura ran Ronnie ya kara ɓaci. Amma ko kaɗan bata damu ba!.

Kasa jurewa Ronnie ya yi har sai da ya ce. "Menene hujjarki na cewa an canza mana littafi ne ba wanda Jesus ya zo da shi muke amfani da shi ba?!". Da É—an daga murya ya yi maganar.

"Amma ai nace kada ku saka mun baki a magana ko ku katseni ko?".

Mamakin jin furusinta suka yi, yadda ta yi masu magana kamar tana basu umarni, kallon mamaki Ronnie ya bita da shi ita kuma Floris kallan takaici! Sai dai basu furta uppan ba, ita kuma ko a jikinta.

"Idan na gama bayanai da nike son yi sai ku tambayeni in kuna da tambaya, amma yanzu ku yi shiru ku saurareni tukun nan, zan gaya maku komai game da hujoji!".

Kasa yin magana Ronnie ya yi, amma ba karya ransa ya sosu, ta wani ajisu kamar wasu Æ´aÆ´anta tana kora masu kashedi, wlh Sweetie akwai balai'n karfin hali yarinyar nan!.

Sai a lokacin Ronnie ya kula da kamar wani abin ya faru a room É—insa bayan tafiyarsu church, amma bai yi magana ba, ya yi shiru bisa umarnin hajiya Sweetie!.
Chapter 21 · 0% Book details