← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 124 OF 242

Sashe 124

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dressing room na momma ta nufa da gudun gaske. Alkyabba ta ɗauko ta fito, tana fitowa shi ma yana shigowa cikin room ɗin, ya duba parlour babu kowa. Murya ƙasa ƙasa ya ce. "Zo mu tafi babu kowa a parlour".

Ai tin kan ya faɗi haka ta yi saurin wucewa. Hannunta ya riko suka fito, ina wannan hanyar sirrin nasu da Hoorain ya taɓa kawota wajen a lokacin da mayakan Queen Zarina suka kawowa kingdom ɗin hari? Kun tuna lokacin da ya ɗaukota daga gonar King ya kawota wajen su momma a wajen?.

To ta wannan hanya suka bi, underground kenan, ko da suka shiga wajen sun rufo kofar kamar ba'a taɓa buɗewa ba, da sauri ya kunna hasken wutar wayarsa, saboda babu haske a wajen. Hannunta ya ja da sauri suka bi ta wajen, sai shera hawaye take yi, shi kuma sai rarrashinta yake ta kara yi. Sun yi tafiya mai nisa kafin su tsaya a wani waje mai ɗan faɗi idan da hanyar suka rabu kashi uku, tsayawa ya yi yana tinanin wani hanya ce wadda zata sada shi da prison na kingdom ɗin nan? Dan a cikin prison ɗin ɗakin duhu yake.

Ya ɗauki a kallah 5 mins yana tinani kafin ya jata suka sake miƙewa kai tsaye suka nufi wajen. Kunsan masarauta idan ta kai masarauta akwai ire iren waɗan nan hanyoyi na sirri ta ƙarƙashin ƙasa waɗan da zasu sadaka da kowani ɓangare na cikin Kingdom ɗin ya kasa, dik salan dabarun yaki ne.

Guyson kamar bai san komai ba, amma sai ga shi yasan hanyar sirri, kai tsaye ya kaita har in da ɗakin yake, sannan ya tsaya da kyau wajen tinanin a dai'dai ina kofar take? Amfani ya yi da ƙwaƙwalwarsa da Allah ya bashi wajen gano kofar,. Duƙawa ƙasa ya yi Auta ta haye saman shoulder ɗinsa, karfinsa yasa wajen miƙewa da ita tsaye, dan shi tsawonsa ba zai kai ya iya buɗe kofar ba, sai ya ɗagata dan ta buɗe.

Hannunta tasa wajen tura kofar, ba koface kamar kowacce kofa ba, tiles ce ta yadda ba za'a taɓa gane akwai kofa a wajen ba sai wanda yasan da wajen, so dikka kofofin hanyar underground ɗin nan tiles ne ta ciki.

Tura tikes É—in ta yi ta buÉ—e ta ciki kenan, tiles É—in ya buÉ—e ta in da Hoorain yake kenan.

Ganin ya buÉ—e yasa guyson ya ce. "Ki haura ki je ki gansa, kada ki wuce 5 mins dan kada a nememu, sannan ki kula akwai masu gadinsa daga ta waje, kada ki bari su ganki".

Okey kawai ta amsa da shi kafin ta yi gaggawar haurawa ta fito ta cikin É—akin, Allah sarki guyson, saboda yana san farincikinta saman shoulders É—insa ta taka da kafafunta ta haura sama, amma ko kaÉ—an bai damu ba, shi dai taga Hoorain ta yi farinciki ya wadatar.

Tana hayewa ta ce ya mashi. "Yah Omar ɗakin akwai duhu sosai, ka miƙo mun wayarka zan haska in gansa".

Kai ya girgiza mata kafin ya ce. "A'a ki je haka kawai, idan kika saka haske a ɗakin masu gadinsa dake waje zasu san an shigo ciki, da waje haka ki laluɓi in da yake kawai a cikin duhun".
Juyawa ta yi ta kalli cikin É—akin, wani irin bakin duhu ta gani mai razanarwa, a hankali ta sake jiyowa ta kalli guyson dake kallanta.

"Ki je babu abin da zai faru In Sha Allah, ki kula sosai". Shiru ta tsaya tana jin tsoron shiga cikin ɗakin, saboda duhun. Kara mata kwarin gwiwa sosai guyson ya yi har sai da ta yarda ta miƙe tsaye, a hanzarce ta mayar da tiles ɗin ya rufe, ta fara laluɓen Hoorain a cikin duhu tana ambatar sunansa ƙasa ƙasa.

ÆŠakin tsit baka jin motsin kowa, tamkar babu halitta mai rai dake a ciki. Sai yawo take yi a cikin duhu amma sam bata ga alamar zata ga halitta a ciki ba, har ta fara karaya ta fara jin kamar zata hakura. Can wani tinani ya zo mata a kan ta yi shiru tsit in dai yana cikin É—akin tabbas zata ji sautin numfashinsa ko kuma bugawar zuciyarsa. Haka kuwa aka yi, ta tsaya shiru tare da kasa kunnuwanta dan saurara.

A hankali sautin numfashinsa haÉ—e da bugawar zuciyarsa dake fita da karfi karfi ya fara ratsa dodan kunnenta. Natsuwa ta kara yi domin sauraron ta ina sautin yake fitowa. Fahimtar daga ina ya fitowa yasa ta fara takawa ta nufi wajen a hankali hankali tana sanÉ—a.

Unexpectly ta ji ta daka tuntuɓe a in da ta buga kanta da kirjinsa, ko bata ga face ɗinsa ba tasan kirjinsa ne daka, da sauri tasa hannunta ta fara laluɓar jikinsa dan ta ji a wani hali yake ciki. Allah sarki, ɗaure yake cikin sarkoki masu girma da kauri, a tsaye yake a kan kafafunsa, a horon dama babu kwanciya, idan wata guda aka yankewa mutum haka zai kasance a tsaye tsawon wannan wata gidan, abinci ma masu gadi zasu bashi a baki, bashi ba motsawa, shiyasa dik wanda ya shiga ɗakin dubu dik ranar da aka fitar da shi kafafunsa basa iya takawa. Dan ko dare ne a tsaye zaka yi barci, kafafu da hannaye dik a ɗaure suke da sarƙa, kuma an ware maka su ba ta yadda zaka yi ka zauna, abin dai gwanin ban tausayi.

Sosai hankalin Zunaira ya tashi, bugawar da kirjinta yake yi ne ya kara tsananta, kuka ta fashe da shi tare da fara jijjiga Lion chest É—insa tana ambatar sunansa a hankali.

Shiru bai amsa mata ba, babu alamar zai amsa mata ba, kuma yana numfashi bare ace ya suma, yana jiyota, magana ne ya ƙasa yi mata tamkar an ɗaure tongue ɗinsa, Allah sarki azaba ce ta yi mashi yawa, a yadda yake ɗauren nan jini ne yake zuba daga damatsan hannunsa da ya sha horo wajen warriors da King ya wakilta dan hora shi, sun dakesa da bulalar kaca mai kifiyoyi a jiki, sannan suka zanya mashi gishiri a dik in da fatarsa ta fashe dan tsananta mashi horo, ya kara jin azaba kenan.

Da yake a cikin duhu ne ɗin Zunaira bata ga wannan ba, ita dai kuma kawai take yi tana jijjiga ɓulɓul ɗin breast ɗinsa. Ganin ba zai amsa mata ba yasa ta laluɓi saman face ɗinsa ta ɗaura hannunta a kumatunsa, a hankali ta ɗaga kafafunta ta kara tsawo, a saman kirjinsa ta kwantar da kanta tare da laluɓar ɗan bakinsa da hannunta dan ta yi shin an rufe mashi baki ne.

Yatsanta ta tura cikin bakinsa tana cigaba da ambatar sunansa, gabaɗaya kayan jikinta sun ɓaci da jininsa ba tare da ta sani ba.

Wani irin ajiyar zuciya ya sauke, can ƙasan maƙoshinsa, da kyar ya iya furta. "My Hoonaira".

Jin alamar kamar ya yi magana yasa ta yi saurin É—ago kanta daga kirjinsa tare da kara É—aga kafafunta ta haÉ—e fuskokinsu, hankalinta a tsananin tashe ta ce. "My Hero ka yi magana ne? Ka yi mun magana ne? Please kana jina? Meyasa ka yi mun shiru?". Out of control take zuba surutan nata.

Silent talk ya yi wajen cewa. "

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
======🔥🔥🔥===========

MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

Silent talk ya yi wajen cewa. "My Hoonaira dama zaki sake yin tinanina har kizo in da nike?".
Kuka mai narka zuƙatan masoya ta saka mashi, a hankali take ɗan bubbuga hannunsa a saman lion chest ɗinsa, da kyar muryarta ya samu damar fita ta fara faɗin.

"Kamanta dama na faɗa maka ko zan mutu babu gudu ba ja da baya ne? Ba zan taɓa iya rabuwa da kai ba, kai ɗin jinin jikina ne, please my Hero kada wani wuya yasa ka juya mun baya, In Sha Allah zamu yi nasara, nasan daddy yana kan fushi ne, idan ya sauko zai saurareni, please ka t............".

Wani irin tari ne ya kubce mata wanda ya sanyata dan dole ta haÉ—iye sauran maganganunta, hannunta tasa da sauri ta toshe bakinta gudun kada tarinta ya fita ya sanya masu gadin su fahimci akwai mutum a ciki.
Su fa Modarawa haka suke da zuciyar bala'i, kada ku ga laifin King, zuciya a jininsu take, basu isa su cirewa kansu ba, shiyasa kuka ga King a haka, wai baku ga dikka jikokin Akka idan sun fusata haka suke rikiÉ—ewa su zama basa ji kuma basa gani bane? To gado ne shi ma wannan tin zamanin jahiliyyah.

Allah sarki yana san rungumarta ya rarrasheta amma babu dama, saboda dikka hannayensa a ɗaure suke. Yana jin raɗaɗin kukan da take yi har cikin ransa tana ratsa shi, amma babu halin taɓuka komai, muryarsa bata fita sosai yake ta faman ce mata ta yi shiru ta daure, sam bata jin me yake faɗe, sai da ta yi kuka sosai har tasa zuciyarsa ta fara yi mashi ciwo, sannan ne ta komar da kanta saman kirjinsa ta kwantar tana shessheka mai taɓa zuciya.

A hankali ta zame hnnunta daga ɗan bakinsa, sannan ta ɗago kafafunta tare da sanya hannayenta ta saƙalo wuyarsa da shi, ta haɗe fuskokinsu waje guda, murya a sarkafe ta ce. "My Hero, promise that ko wani hali zamu shiga tabbas zaka tsaya a kan soyayyarmu babu gudu ba ja da baya".

A yadda take maganar lausasan lips ɗinta suna taɓa nashi yasa gabaɗaya ya jisa a wani sabon babin na yanayi, gabaɗaya sai ya kara jin kasala sosai, dama ba wani kwari ne da jikin nasa ba. Da kyar ya iya cewa. "Ba zan taɓa juya maki baya ba my princess, dik wahalar da za'a bani matsawar ina numfashi to tabbas zuciyata zata yi kowacce bugawarta ne da sunanki, ba zan janye ba sai dai a kasheni ko kuma ke ki juya mun baya!!".

Kai ta fara girgizawa kafin ta ce. "Ba zan taɓa juya maka baya ba ka ji?". Kai kawai ya jinjina mata yana cigaba da sauke numfashi mai ban tausayi.

••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥🔥
Chapter 124 · 0% Book details