Sashe 61
Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana rike da hannunta suka nufi master room na Black Tiger. Ko tsoro bata ji ba, dan ta kuduri niyar ba gudu ba ja da baya.
Ronnie ne ya sanya password a jikin kofar. Nan take ta wangale. Ciki suka shiga, tin da ta sako kafarta ciki take ta faman rarraba idanu tana neman ta ina zata gansa. Da yake ɗakin yana girma sosai, shi kaɗai ya kai girman gidan wani, tsakanin in da King bed ɗinsa da mirror yake ba ƙaramar tazara bace ba.
Kai tsaye bakin bed suka nufa, suna isa Ronnie ya sake hannunta ya haye saman bed É—in ya kwanta, a hankali ya janyo pillow ya rungume yana jin wani irin nishaÉ—i da bai iya tantace na menene?.
Ita kuwa cigaba da rarraba idanu ta yi tana neman ta ina zata ga Black Tiger a cikin É—akin. Can har ta cire tsammani da ganinsa kamar daga sama taga mutun a bagan mirror yana gyara gashin kansa.
S-p dress ce a jikinsa launin up white, rigar tana da dogon hannu kazalika wandan ma doguwa ce har ƙasa, yana tsaye kan kafafunsa ya basu baya.
Ajiyar zuciya ya sauke with her full confidence, with a cool voice ta ce. "Big bro good evening".
Zaro idanu Ronnie dake kwance a saman bed ya yi, bai yi expecting hakan ba, shi da ya ce su bi komai a hankali tana neman jawo masu bala'i.
Kamar bai san da su a cikin É—akin ba, cigaba da abin da yake yi ya yi....... Hannunta dikka biyu ta riko waist É—inta da shi, like she didn't care a kan shareta da ya yi, cike da tsiya da neman tsokana ta ce. "Big bro sam kayan nan basu yi maka kyau ba, ka canza wasu dan bana sansu a jijinka".
Ai a miliyan Ronnie ya tashi zaune a tsakiyar bed É—in tamkar wanda aljanu suka fasa jikunsa suka shigesa a lokaci, a razane ya zaro ido yana kallonta, lallai Sweetie ta cika yar neman bala'i, ko ina ruwanta da kayansa? Ronnie ya jefawa kansa tambayar.
Ita kuwa, É—an tawa one step ta yi gaba kaÉ—an, sannan ta É—an É—aga kanta sama kallonta a kansa, cikin salon jan magana da neman tsokana ta sake cewa. "Ni fa ko baka amsa mun ba ban wani damu ba, nasan kana jina, handsome guy kawai, amma ba wai kana da............."
HaÉ—iye sauran maganar ta yi sakamakon wani haske da ya fito daga cikin idanunsa ya daki mirror dake gabansa sai ya juya ya nufota, tafin hannunta tasa cikin zafa ta tari hasken, hakan yasa ya tsaya bai tarwatsata ba.
Yadda kuka san wani walkiya haka Ronnie ya diro ƙasa daga saman bed ɗinsa, da gudu ya iso gabanta, cikin zafa ya fisgo hannunta, da gudu ya jata domin su nufi waje.
Sai dai kash, suna isa kofar É—akin sai suka kasa iya buÉ—eta, ta datse gam.. babbar magana, dama shi Ronnie yasan tin da Sweetie ta ji Black Tiger ba zai kasheta ba ya shiga uku, ba ita kaÉ—ai zata sha azaba har da shi, wayyo Allahnsa.
Me kuke tinanin Black Tiger zai yi masu?.
••••••••••••••••FOREST•••••••••••••••🔥
A hankali ta fara yunƙurin buɗe idanuna da suka yi mata balai'n nauyin gaske. Jikinta dik ji take yi kamar ba nata ba, da kyar ta iya buɗe idanun nata, kyakkyawan ganye kore shar ta fara cin karo da shi a ganinta, hasken rana ne yake haskowa ta tsakanin ganyayyakin, sai hakan ya bada wani kala na musamman.
Mamaki ne ya kamata ganin an yi mata rumfa da ganyayyaki. A hankali ta yunkura ta miƙe zaune, jujjuya idanunta ta fara yi tana neman ta ina zata hango mutane. Sai dai bata ga alamar kowa a wajen ba.
Hannu ta ɗaura a kan cikinta domin ta taɓa ciwonta ta ji, sai ta ji kaya mai kauri a jikinta. Da sauri ta kai kallonta jikin nata. A wani irin zabure ta miƙe tsaye lokacin da ta ga irin rigar dake jikinta.
Zaro idanu waje ta yi, nan take ta haɗiyi wani irin yawu mai sauti, fitowa ta yi daga cikin rumfar, hannunta ne ya fara kerma alamar tsorata, kafafunta ne suka fara raunata suna ƙoƙarin kasa iya ɗaukarta, amma haka ta dake ta fara taka ƙasa tana waige waige, tamkar mai neman wani abin.
Jacket mai bala'in kyau launin black color ne a jikin nata, jacket ɗin yana da hula, da ta miƙe tsaye tsawonsa ya kai mata har gwiwanta, to jacket ɗin wanenen kenan?. Harda hular aka sanya mata a kanta.
Tafiya take kamar zata kifa kasa, tana yi tana waige waige kamar wata maras gaskiya. Cak ta tsaya lokacin da idanunta suka sauka a kan wasu irin furanni farare da yellows masu bala'in kyau da ɗaukar hankali, sai a lokacin ta mayar da hankalinta a yanayin wajen, fillin ya yi matukar ƙawatuwa sosai, korayen gayyayakin dake wajen sun kara haska ko'ina, ga furannin sai tashin wani irin kamshi mai kwantar da hankula suke yi, furannin suna da yawa sosai, sun kewaye arear wajen. Ga tsuntsaye masu launika daban daban.
Wani irin kara ta ji a gaba kaÉ—an kamar karar zubar ruwa kamar kuma na sahun mutane. Take ta ji jikinta ya mutu na ganin wajen, ga yanayin weather wajen iska mai ni'ima da ratsa jiki.
A hankali ta ja kafafunta ta nufi wajen da take jiyo wannan kara. Like wow, tin daga nesa ta hango wasu irin koramu dake aman ruwa mai hasken gaske, wasu irin flowers manya manyan launin white kewaye da kusa da koramar, ga duwatsu masu kyau da ɗaukar hankali, wajen ya kawatu matuƙa.
Ai Auta bata san time da ta wani irin sauke sayayyar ajiyar zuciya ba, tin ainahinta tana san irin wannan waje, kun manta nace maku ita da Chuchu suna yawan kallan films masu irin wannan dajin a nan suka sakawa soyayyarsu sunan shuka flowers É—in kauna?.
Wani irin nishaÉ—i na musamman ne ta ji yana ratsa zuciyarta, har ta saki cool murmushi ba tare da ta sani ba, ji ta yi tamkar ta je ta shiga cikin wannan koramar ruwa ya yi ta zuba a kanta, ciwonta ne kawai ya hanata zuwa, da ba abin zai hanata shiga.
A hankali ta ƙarisa tinkarar wajen koramar. Can ta hango kamar an kunna wuta ta gefen koramar ɗan baya kaɗan yana ci, hayaki ta fara hangowa. Ɗan kara ɗaga kafafunta ta yi ta nufi wajen.
Wani irin birki ta ja lokacin da ta matsa kusa da hayaki, ta hango Pretty zaune a kusa da wutar tana kara jefa wasu kananan itace dake hannunta a cikin wutar yana kara kamawa, zaro idanunta waje sosai ta yi tamkar kwayar idanunta zasu faɗi ƙasa.
A zahiri zakuga kamar Pretty take kallo, amma sam ba ita take kallah ba, namijin gaske take kallah, yana tsaye a saman wata dutse dake kusa da koramar, ya sanya takobinsa a cikin ruwan dake kwarara yana wankewa, ita kuma Pretty tana jin É—umi kusa da wuta.
A fili da karfi Auta ta furta. "HOORAIN!!!!".
A tare shi da Pretty suka dawo da kallonsu a kanta. Kafin dikkansu su yi wani motsi cikin É—aga murya ta sake cewa. "Pretty ki gudu daga kusa da shi, mugu ne! Kasheki zai yi!".
Miƙewa tsaye Pretty ta yi, cike da yarinta a muryarta ta ce. "A'a Zunaira ba mugu bane, shi ne ya taimakemu ya kuma saka maki magani a ciwonki, ya canza........."
Tsawar da Auta ta daka mata a kan ta tashi daga kusa da shi a karo na biyu ne yasa ta yi saurin haÉ—iye sauran maganar, tsawa Auta ta sake daka mata. "Kizo mu gudu Pretty, kasheni ya zo sake yi".
Hoorain dake tsaye kamar an dasashe mamakin Auta ya gama kashe shi ne ya juyo da jikinsa gareta gabaÉ—aya ya fuskanceta.
Da yar gudunta Pretty ta baro wajen wutar ta nufo Auta, rike hannun juna suka yi da sauri suka juya da nufin su bar wajen, Pretty tana ta faÉ—in. "Zunaira kin san shi ne? Zunaira kin san shi ne?".
Shiru Auta bata amsa mata ba. Cikin Zafa Hoorain ya diro cikin ruwa daga saman dutsen, a gaggauce ya mayar da takobinsa mazauninsa, yaga da gaske zasu tafi, with his full power ya bi bayansu.
Gaban Zunaira ya tare, cikin sanyin murya ya ce. "Ranki ya daÉ—e lafiya kuwa?".
A tsawace ta ce. "Ka bani hanya na wuce, idan kuma ka biyoni nan ɗin ka ƙarisa kasheni tun da Allah ya kuɓutar dani a farko ne kuma sai in ji?".
Shiru ya ɗan yi kamar mai tinanin wani abin, sai can kuma ya ce. "Ban gane me kike nufi ba ranki ya daɗe"........... Ranta ne ya kara ɓaci, ko kaɗan babu tsoronsa a ranta, dan su ba jinin tsoro bane, a fusace ta ce. "Ba zaka gane ba ai dama, ka bani hanya!!"..
Pretty ce ta katsesu da cewa. "Zunaira wai me yake faruwa ne? Kin san shi ne?".
Rai a matuƙar ɓace, zafafan hawaye har sun fara tsere a saman face ɗinta, da kyar voice ɗinta yake fita ta kalli Pretty kafin ta bata amsa da.
"Ya wuce sani na yi mashi Pretty, kuma shi ne sanadiyar zuwana wannan dajin, shi ya ji mun wannan ciwo dake cikina! Kasheni ya so yi Allah ya yi ina da rabon cigaba da rayuwa, yanzu nasan ya jefa mun ƴan uwana cikin tashin hankali, ya cutar da zuƙata dayawa, ya zaluncemu, daddyna ya yarda da shi sosai amma ya ci amanar yarda, ba zan taɓa yafe mashi ba, na tsanesa fiye da tinanin mai tinani".
Tin da ta fara magana ya shiga ruÉ—ani da tantanmar anya Zunairarsa ce kuwa? Dan dai shi yasan Zunairarsa ba haka take ba, bata da faÉ—a ko kaÉ—an.
Yana can yana tunani ta figi hannun Pretty suka raɓa gefensa zasu wuce. Cikin zafa ya sake tare gabanta, a dai'dai lokacin ta dafe saitin cikinta, saboda figar hannun Pretty da karfi da ta yi ɗin nan ya ja cikinta ya amsa.
Tana dafe cikin bai san lokacin da ya matsa kusa da ita ya tallapota a jikinsa ba, shi dai komai zai faru voice nasa a sanyaye cikin nitsuwa, sam baya da hayaniya komai tashin hankalin da zai shiga.