← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 242

Sashe 8

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Janyota jikinsa ya yi kawai yana sauke ajiyar zuciya, har ga Allah a tsorace yake, baya burin ta sake haɗuwa da yayansa, dan shi yasan wanene Black Tiger, mutumin da bai taɓa yafiya ba a tsawon rayuwarsa, bai ma santa ba, baya ɗaga kafa koda kuwa ga tsinke ne, kana mashi ɗaya zai yi maka ɗari, dole ya ji tsoro!.

Jinta a jikinsa yasa ta farga babu riga a jikin nasa, cikin sauri ta É—ago ta kalli face É—insa, while shi ma ita yake kallo. Watsewar da gashin kanta ya yi har fuskarta yasa bata samu damar ganin face É—insa da kyau ba.

Hannu ya kai ya tattare mata gashin waje guda, dan su samu damar ganin juna da kyau. Dikkansu sun ji daÉ—in hakan, barema shi da har wani cool ajiyar zuciya ya sauke.

"Ronnie why are you looking at me like that?"
Ta yi maganar tana ƙoƙarin barin jikinsa, dan ta ɗan tsorata na ganin kirar halittarsa.

Girgiza mata kai ya yi ba tare da ya yi magana ba, a hankali hankali yake sauke numfashi, hannunsa dikka biyu ya É—aura a saman bayanta ya hanata barin jikin nasa.

Da sauri ta É—ago kallonta a kansa. Kurawa juna idanu suka yi kamar waÉ—an da suka afka duniyar tunani.

An rasa mai kawar da kallonsa daga kan É—an uwa, da alama sun mace a kallon junansu ne.

--------- KNOCKING DOOR-----------------

Knocking door da aka fara yi daga waje ne yasa suka farga tare da dawowa cikin hanyacinsu, a nutse ya sauke ajiyar zuciya tare da saketa, ya É—an raba jikinsa da jikin door É—in ya kuma saketa.

Idanunta na'a a kan kofar, ta wani zarosu irin like tana mamakin wanene?.

Fingerprint É—insa ya sanya a kofar ba password ba, sannan ya wuce ya nufi wajen bed É—insa. Kamar ba shi ya wani rungumi Sweetie a yanzu ba.

Shigowa ciki Floris ta yi tana ɗan tsuke fuska alamar shagwaɓa. Sanye take da irin wannan shiga tasu ta riga da kuma sket har ƙasa, kayan yana da bala'in kyau, ta ɗaure gashin kanta a tsakiya, hannunta riƙe da Bibel, da alama shirin zuwa church ta yi.

Kallo É—aya Ronnie ya yi mata bai furta uppan ba ya nufi toilet dan ya yi wanka. Da ido ta bishi tana mamakin ganinsa babu riga, sai kuma ta kara yin wani mamakin ganin Sweetie a tsaye a bakin kofa.

Kasa haÉ—iye mamakin nata ta yi har sai da ta ce. "Sweetie me kike yi a nan?".

"Babu komai". Ta bata amsa kai tsaye tare da wucewa ta nufi wajen bed É—insa.

Bayanta Floris ta bi tana faÉ—in. "Ya ke baki yi shirin zuwa church ba?".

Tana ƙoƙarin zama a bakin bed ɗinsa ta answer da. "Na faɗa maki mu bama zuwa church, masallaci muke zuwa, idan kuna da musque zan je can on Friday".

Tin da ta fara magana idanun Floris yake a kan É—an bakinta har ta dire aya.

"Sweetie kin mun kama da wata mata da na taɓa gani cikin birnin nan! Sai dai ba sosai kuke kama ba, idan an ganki a fisge ne dai sai a ga kamar ita ce". Cewar Floris.

Ba tare da kawo wani dogon tunani ko wani nazari ba ta amsa da. "Kinsan halittun Allah dayawa, dama dai yarinya kika ce ina kama da ita to da sai in ce Pretty ce kila, amma ba yadda Ubangijinmu baya halitta".

Karisowa wajenta Floris ta yi, tana mamakin hali irin nata, yarinya sam bata taɓa ɗaukar abubuwa da mahimmanci, akwaita da careless, bata sanya damuwa a ranta, hasalima ba zaka taɓa gane ina alkiblarta a zamantakewa ya dosa ba, ji yadda ta bada amsar cewa da aka yi anga mai kama da ita, tamkar bata da uwa ko wasu ƴan uwan, a yanayin yadda suka taso su biyu cikin maraici ai zasu so ace ga mai kama da su ko dan su ji sanyi a ransu, ko da ba ɗan uwansu bane zasu ji matuƙar daɗin hakan suma yau sun ga mai kama da su, amma ta nuna halin ko in kula, dik yadda aka yi ba iya baiwa kawai gareta ba, ta san tarihin iyayenta, tasan in da za'a iya samunsu, dole akwai abin da take ɓoyewa, yarinya ƴar karama da ko 13 years bata cika ba sai shegen wayo........

Wannan cikin nata ba shakka ya fi tara sirri a cikinsa fiye da yadda yake É—aukar abinci, dole a jinjinawa Sweetie yarinya mai wayo kuma Æ´ar baiwa.

"Sweetie wai ke baki mamakin abubuwa ne?".
Floris da abin yake damunta a rai ta gaza haɗiyewa ce ta jefa mata wanna tambayar, dan ita dai gaskiya tana mamakin rashin bayyana farinciki ko bakincinkin da Sweetie bata yi, baka taɓa gane a wani irin yanayi take!.

ÆŠan motsa gefen bakinta sweetie ta yi kamar zata É—an yi tsaki haka, alama ce ta amsa magana ba tare da ta buÉ—i baki ba, alama ta yi mata da ita bata wani jin mamakin komai a rayuwarta, dan ta ga abubuwa daban daban da suka girmi shekarunta kuma kwakwalwarta ya É—auka, taga kaddarori da jarabawa daban daban, so yanzu ta daina nuna damuwa.

"Kina burgeni sosai Sweetie, and kyanki yana tafiya da ni, Please can we be a friends?". Cewar Floris.
Ta yi maganar tana miƙa mata hannu kamar mai shirin yin musabaha.

Babu wani ɗaukin hakan a tattare da Sweetie, babu wani shauki, ta jinjina mata kai tare da miƙo mata nata hannun tana faɗin. "Yeah we can".

Sam Floris bata ji daÉ—in ganin yadda Sweetie bata nuna shaukin hakan ba, amma bata nuna rashin jin daÉ—in nata a fili ba, ta danne ta kama hannunta suka gaisa, daga yau sun zama abokai kuma Æ´an uwa.

"Amatsayina na abokiyarki kuma Æ´ar uwarki na É—auki alawarin koya maki dik abubuwan da na sani a duniyar nan". Cewar Floris.

Kanta a kasa tana kallon ƴan yatsun kafafunta da suke ɗan yi mata zafi saboda karon da suka yi da Ronnie a lokacin da take ƙoƙarin shiga room na Black Tiger, so a lokacin ya taka mata ƴan yatsun kafafunta, ƴar ƙaniya tun ɗazun da take tare da shi bata ji zafin ƴatsun nata ba sai yanzu da ya shiga toilet ne ta gane ashe suna yi mata zogi, ɗazun ganinsa ya kwashe zogin.

So kanta a ƙasa ta amsawa Floris da. "For sure nima zan koya maki dik abin da na sani a rayuwata, ciki kuma harda addinina".

A hanzarce Floris ta amsa da. "Nima zan koya maki nawa addinin".

Jinjina kai Sweetie ta yi. "Na yarda ki koya mun dik abin da kika sani dangane da addininki, na kuma yi maki alkawari a dik lokacin da muka yi zurfi cikin koyan addinan guda biyu, idan har baki ji addinina ya burgeki ko kuma ya kwanta maki a rai ba, ko kin gane addinin gaskiya daga ciki ba to ni zan koma naki addinin!". Babbar magana!!

A É—an ruÉ—e Floris ta zaro idanu waje, mamaki fal a ranta ta ce. "Zaki dawo addinina? Da gaske kike yi please?".

Girgiza kai Sweetie ta yi tare da dawo da kallonta a kan Floris, ya tabbata Floris yarinya ce, ai shi addinin gaskiya baya ɓuya yarinya, wuyarta ki fara koyan ilimi daga cikinta, kina farawa ko ance ki bari ba bari zaki yi ba, yo Allah wasa ne?!.

"Tabbas in dai kika nutsu kika sami ishasshen ilimi a kan addinina, kika zurfafa tunani, kika yi dik abin da na gaya maki to ba shakka in baki gamsu da addinina ita ce ta gaskiya ba zan bi taki". Cewar Sweetie.

Sosai Floris ta ji daɗin wannan furuci na Sweetie, kuruci dangin hauka, ita yanzu a ganinta zata yi wa Sweetie wayo ne ta shigo addininsu, bata san Sweetie kam da wayonta aka haifo ta ba, ko mai shekara 20 ba ya gwada mata dabara ba, yarinya kamar renon tsafaffi, Floris sai dai mu ce welcome to Islam, dan na tabbata dabarar Sweetie ba zai barki ki iya tsallake wanna challenge ɗin ba, bari ma mu zo mu fara shirin tarbar sabuwar baƙuwa a cikin addininmu..............🤸🕊️

Fitowa Ronnie ya yi É—aure da bathrobe a jikinsa, launin milk color, white hairnsa yana É—igar da ruwa.

Kallonsu dikkansu suka kai a kansa, yana da sexy gorgeous body shi ma, kamar yayansa, ga yanayin koreans skin É—insa sai dai muce masha Allah.

"Beb kai fa nike jira tun É—azun, ka zo mu tafi". Cewar Floris.

Idanunsa a kan Sweetie ya amsa da. "Ten minutes".
Daga haka ya wuce dressing room É—insa.

A gaggauce ya shirya cikin ƙananan kaya crazy, ya fito fes abinsa, ya tsaya gaban mirror ya canza ɗankunnen dake kunnensa, dama suna dayawa har da wani ta saman kunne, dik ya canzasu, ya ɗauki wani haɗaɗen gold pil ya sanya a kusa da lips ɗinsa ta ƙasa, sai ya so ya yi kama da mace, sai ma da ya busar da gashin kansa ya tara ya ɗaure, idan baka ga kirar sexy badynsa ba kaga iya face ɗinsa zaka yi zaton mace ce ba namiji ba, kyau iya kyau.

Time da ya fito kasa hakuri Sweetie ta yi har sai da ta ce. "Ni Ronnie na rasa gane da kai da yayanka waye ya fi wani kyau? Kuma sam baku kama da shi fa, shi kamanninsa ma daban yake".

Tabbas basa kama, dan Black Tiger dai ba koreans bane, Black Tiger ya fi kama da turawa gaskiya.

ÆŠan lumshe idanu ya yi yana sakar mata murmushi.
"Na fi yaya kyau mana". Cikin zolaya ya yi maganar.

A hanzarce ta ce. "Tun da ka amsa ka fi shi to tabbas baka fishi ba, shi ya fika, dan dik wanda yake da abu baya fitowa ya ce yana da shi, sai dai a gaya mashi yana da shi, dan haka baka da kyau".

Floris da mamaki ya gama kasheta ne ta tsoma baki kamar wata mara lafiya a in da ta ce.
"A ina kika taɓa ganin yayansa har kika san yana da kyau haka?".

Ta ji abin da bata taɓa ji bane, dan tasan ko Ronnie bai san kamaninsa ba, mamaki kamar ta sume a zaune.
Chapter 8 · 0% Book details