← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 242

Sashe 94

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zee har ta goge ta yi kyau, sai dai ko kaÉ—an bata jin daÉ—in zama da su Aneesa, suna tsangwamanta, bare ma Sarina da in dai ta shigo sai ta ci mata mutuncin da kare ma ba zai sinsina ba, amma tana hakuri tana dannewa dan gidansu ta zo, kuma ko ba komai sun taimaka mata, ita burinta Khadijah ta samu lafita su koma Nigeria abinsu.

Da yake uncle Jahiz ɗan duniya ne girma cikin turawa, sai ya fara binta da kallo tun daga kafafunta har izuwa kirjinta, sai da ya ɗan tsai da idanunsa a kan kirjinta ma kafin ya kai kallansa a kan face ɗinta. Ta yi ƙasa da kai ta takure jikinta waje guda, tana jin kunyar motsawa daga in da take, jin sallamarsa dama yasa ta juyo, ta yi danasanin ɗaura towel bata sanya hijabi kamar yadda take yi a gida ba, kuma saboda taga babu wanda yake shigowa ɗakin ne yasa bata saka hijabin ba.

Ko kaÉ—an babu kunya a idanunsa ya sake dawo da kallansa a kan kirjinta da suke cike fam, a hankali ya kalli santala santalan cinyoyinta da yanzu suka murje suka yi kyau saboda wanka da sabulai masu rai da lafiya na Aneesa da take yi.

Ya kasa motsawa ya kuma kasa kawar da kallonsa daga kanta, sai ma ƙara kurawa kirjinta ido ya yi, ita kuma ta kasa gudu ta bar wajen, to me kuke tinani zai faru? Shi dai uncle Jahiz ba kunya ne da shi ba, ni dai na tafi shan maltina idan na dawo zan ga shi da ita waye zai ɗagawa ɗan uwa kafa, shin zai hakura ya ja da baya ya koma ne? Ko kuma ita zata danne zuciya ta gudu? Su dai suka sani, ni na yi ta nan...............🥱

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
======🔥🔥🔥===========

MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

Cigaba da karewa albarkatun jikinta kallo yayi, kwata kwata babu alamar zai ja da baya ko ya kawar da kansa, ta gaji da tsayuwa taga alamar bafa dai'na kallanta zai yi ba, dan haka sai ta daure ta fara takawa a hankali kamar wadda kwai ya fashewa a ciki ta nufi dressing room na Aneesa.

Dik wani step ɗinta ɗaya a kan idanunsa take yi har ta kurewa ganinsa, nannauyar ajiyar zuciya ya sauke tare da ɗan dukar da kansa ƙasa, shi kaɗai ya fara ayyana yadda kyanta yake a cikin ransa, saman sofa ya zauna yana kara jinjina kyan abin da ya gani, to da alama dai ransa ya biya.

Shi da bashi da fara'a ko kaɗan, sai ga shi yau ya sanya hannu saman arabs hairnsa, yana ɗan watsa gashin yana murmushi kamar wani sabon kamu......... My people's ni wai ba uncle Jahiz ba ne ya ce ba zai taɓa san mace ba sai ya kai 40 years? Sannan har da wani ce mana babu abin da zai yi da yar yarinya, shi mace daga mai 25 years ya yi sama yake so? Anyi haka ko ba'ayi ba? To inaruwansa da Zee ɗinmu? Zee dai 17 years take da shi, ko Khadijah bata kai 20 ba bare Zee bare kuma a kai ga 25 years, me uncle Jahiz yake nufi? Kada ma ya kuskura ya fara ce mana ya janye kalamansa, dan ba zamu lamunta ba, amma guy ɗin nan ya sha damu dama, to wai an faɗa mashi mata wasa ne?......…....🤔

Shiri Zee ta yi cikin abaya again, kunsan su Aneesa kaso 80 cikin ɗari na kayansu abayas ne, saura kaso 20 ɗin kuma irinsu riga da wando, riga da sket and gown ne. Abaya mai kyau da tsada launin purple color ta sanya, ta yi rolling mayafin a kanta, sai kuma ta ƙasa fitowa waje, saboda bata san haɗa idanu da shi, zuciyarta ta ja baya matuƙa da shi, dama kun san halin Zee ai, yanzu ma saboda Khadijah ta samu lafiya yasa ta yi sanyi take jure komai da ake yi mata, banda haka ai wlh ba sarauta ba, ko uban me uncle Jahiz yake ji da shi bai isa ya karewa albarkatun jikinta kallo haka ba.

A yanzu haka zuciyarta ta raya mata uncle Jahiz É—an iska ne, kada ta yarda da shi ya je ya cuceta ya yi mata ciki kamar Khadijah, wannan shi ne babban dalilin da zuciyarta ya rike yasa ta yi baya sosai da shi, ta ji bata san sake haÉ—a inuwa da shi, amma kuma tana san ganin Khadija, kuma kun san dole sai ta hannunsa zata samu damar ganinta.

Ta kai 30 mins da kammala shiri, amma ta samu waje saman É—aya daga cikin drawers dake cikin ta yi zamanta tana tinanin mafita a gareta, dan wlh bata ga abin da zai sa ta sake bari ya kalli surar jikinta har haka ba. Shi kuwa zama ya yi yana jiranta, tunanin kyan surarta da kwaÉ—aituwa da shi yasa bai ga tsawon lokacin da ta É—auka bata fito ba, sai yake ganin kamar yanzu ta shige.

Sai da suka kara wani 20 mins a kan wancan 30, nan ma sai da yaga kiran Dr sannan ya miƙe tsaye ya nufi dressing room ɗin cike da mamakin me ya hanata fitowa? Shi bai san cewa mu ƴan Nigeria muna da alkunya ba, dan shi bashi da shi sai yaga kamar kowa ma bashi da, a'a mu Nigerians muna da shi sosaima.

Ya sha madarar mamaki na ganinta zaune shiru ta buga uban tagumi, tinanin Khadijah da ta afka yasa bata ji shigowarsa bama, sai jin sautin muryarsa ta yi yana faÉ—in. "Zee lafiya kika zauna a nan?".

A É—an razane ta É—ago ta kallesa. Kallo É—aya ta yi mashi ta yi saurin kawar da kai, ta tsani maza dama idan baku manta ba, da shi kaÉ—ai ta É—an saki jiki ashe shi ma É—an iska ne, wani tsanarsa ce ta ratsa zuciyarta, sai ta ji kamar ta gudu ta bar gidan, amma ina zata je to idan ta gudu?.

Kanta a ƙasa ta amsa mashi da babu komai. Ko kaɗan bai kawo aransa da wata matsala ba, dan shi yana ganin ai normal ne kallan da ya yi mata.

"To tashi muje Dr na jiranmu". Ya faÉ—a idanunsa a kan kirjinta dik da ta sanya kaya.

Da yake bata ma san fita zasu yi ba sai ta ji zancen wani irin, a ranta ta furta yanzu haka zata jera da wannan É—an iskan? Sannan su shiga mota É—aya a gidan baya, bayan haka su je hospital? Wlh ba dan Khadijah ba bata ga abin da zai sa ta sake É—aga idanu ta kalli mutumin nan har ta jera a tare da shi ba.

Miƙewa ta yi jiki ba kwari ta nufo shi, a maimakon ya wuce gaba sai ya ce mata ta yi gaba zai rufa mata baya, aikuwa nan fa ta ce babu wannan magana, kar ta fito ta ce mashi ita a'a sai dai ya wuce gaba ko ta fasa zuwa ta hakura da ganin Khadijah ɗin. Jin hakan yasa bai yi mamaki ba ya wuce gaba, da harara ta bishi tana jin kamar ta dallah mashi mari amma babu dama, zai wani ce ta wuce gaba dan ya ji daɗin kalle mata baya tana tafiya, to wlh ba zata yiwu ba, ta faɗa a cikin ranta tana harararsa.

Sai da ma ya É—an yi nisa sannan ta rufa mashi baya. Ko da suka shiga mota taki É—agowa ta kalli in da yake, shi kuwa a da idan sun shiga mota latse latsen wayarsa yake yi baya wani kallanta, yau kuwa zura wayar a aljihunsa ya yi yana cigaba da kare mata kallo da kyau kamar wanda ya samu tv. Dannewa ta yi kamar zata yi kuka, amma haka ta hakura har suka isa hospital É—in.

Kai tsaye ɗakin da Khadijah take suka nufa, special room ne da aka ware mata ita kaɗai dan kula da ita sosai, a gaskiya ba karya ta samu kulawar da ta dace matuƙa. Tana kwance shiru idanunta biyu tana kallan sama, da yake ta yi ta shan drip sai bata wani rame ba, har wani haske ta kara yi sosai, ta kusa kamo Zee hasken fata, jikinta ya yi fresh sosai.

Tana ɗaura idanunta a kan su ta wani zabura ta miƙe zaune, idanunta a kan uncle Jahiz ba a kan Zee ba, ita kuwa Zee tana ganin ta farfaɗo ta tafi da gudu ta rungumeta tana ambatar sunanta. Tamkar ba Khadijah bace a wajen, ta kafe uncle Jahiz da kallo mai wuyar fassaruwa, lokaci guda kuma wasu zafafan hawaye suka fara wanke kata fuska.

Hankali a tsakanin tashe ta furta. "Zee a ina kika samo wannan mutumin............". Sai kuma ta dakata da yin maganar, a hanzarce ta kai hannu ta fara goge hawayenta da suka fara zubowa, a take ta shanye kukan nata.

Jin furucinta yasa Zee ta yi saurin raba jikinsu da juna, a tsananin matse da san jin kan zance Zee ta ce. "Khadijah kenan da gaske shi ne a jikin wancan hoton ko? Dama na ce maki shi ne kika ce ba shi bane, kullun sai na kalli hoton nan in kuma kallesa idan mun haɗu da shi, har yau ban taɓa ganin banbancinsa da na cikin hoton ba, amma kuma kin ki ki faɗa mun gaskiya".

Da Hausa suke maganar, hakan yasa uncle Jahiz sam bai fahimci me suke faÉ—e ba.

Murya a raunace, da alamar karyewar zuciya a tattare da ita, da kyar ta iya cewa. "Zee kada ki sake yin magana a kan wannan hoto kamar yadda na faɗa maki a baya, na faɗa maki ba shi bane ya tsaya a iya hakan!! Idan kuma ɓacin rai'na kike so to bismilla ki cigaba, and in kuma ban isa in yi maki magana bane nan ma ki cigaba kasa ki dai'na".
Chapter 94 · 0% Book details