← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 234 OF 242

Sashe 234

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gadan gadan guguwar ya nufota yana dunkule waje guda yana fitar da kalar wuta daga cikinsa ga hayaki. Hannunta ta sanya ta kare fuskarta tare da furta lailaiha illah anta subhanaka inni kuntu minaz-zalimin, hasbunallah wani'imal wakil. Lokaci guda ta ji an taɓa jikinta, a gaggauce ta zame hannunta daga saman face ɗinta tare da waro idanunta waje.

Nan ta yi arba da kyakkyawan face É—in Ronnie yana tsaye, idanunsa dik barci, gashin kansa a watse kamar wani mahaukaci sabon kamu! "Sis lafiya kike ihu haka?". Ya jefa mata tambayar cikin muryar barci. A miliyan ta kai kallonta bayansa dan ta duba guguwar. Juyawa ya yi shi ma ya kai kallansa wajen, wayam babu kowa, INA GUGUWAR?. Windows É—inma a datse suke gam. A tare suka dawo da kallonsu a kan juna.

Ɗan girgiza kai ya yi. "Akwai wani abin ne". Ya yi maganar idanunsa suna washewa daga barcin da yake yi. Haka kawai ta tsinci kanta da ƙasa faɗa mashi abin da ta gani da irin mafarkin da ta yi, sai ta ce mashi babu komai. Ɗan zubawa face ɗinta idanu ya yi yana kallon irin razanar dake a kan fuskar tata, sai kuma ya ɗan juyar da kallonsa izuwa in da ta kurawa idanu, a cikin zuciyarsa ya fahimci akwai wani abin, dole wannan ihun da ta rinƙa zundumawa wani abin ta gani, amma sai ya ce mata. "Muje ki kwanta in tayaki ki yi addu'a babu abin da zai faru In Sha Allah". Shi da yake bai san da batun Duniyar Shaiɗanu ba, sai ya zaci ko dai yayansa ne ya razanata ta hanyar magic, so yasan ba zai cutar da ita ba shiyasa ya ce su je ta kwanta.

Ba musu ta bisa ya rakata wajen bed, kwanciya ta yi tare da fara karanto addu'oi, shi ma addu'oin ya tayata karantawa waɗan da ya iya, ya shafa mata sannan ya ja mata bargo tare da miƙewa ya nufi bedroom ɗinsa dake manne da nata. Tana kallonsa bata iya ce mashi ko uppan ba, tamkar an ɗaure tongue ɗinta har ya fice. Ajiyar zuciya ta sauke tare da juyar da kallonta tana kallon windown, tamkar ba windown da ɗazun ya ruguje ba, to me yake faruwa da ita ne?. Ta jefawa kanta tambaya, ni kuma na amsa mata da kin fara shiga sabgar Duniyar shaiɗanu ne ta hanyar ƙoƙarin sauya masu Auta, dole su yi tattaki dan daka maki zazzafar warning, ai ke yanzu rayuwarki tana cikin gagarumin haɗari mai karfin gaske, dole ki dage da addu'a tare da fatan Allah ya raba Black Tiger da duniyar shaiɗanu, dan kuwa shi kaɗai ne zai iya tsaya maki ya kwaceki daga hannunsu, gara ki yi addu'ar ya fita daga makircinsu, idan ya fita, zai fitar dake kema!!.

My people's dik yadda aka yi Sweetie and Ronnie suna da alaƙa ta jini mai karfi gaske, saboda irin tsananin kaunar da suke yi wa junansu, sannan idan kuka yi duba da yadda Ronnie zai rungumi Sweetie, ya bata hot sumbata, ita ma zata rungumesa, amma ko kaɗan basa jin feeling ɗin juna, hakan ya nuna akwai jini mai karfi a tsakaninsu, Sweetie ta fi Floris kyau da komai da komai, amma meyasa Ronnie baya feeling soyayya a kanta sai a kan Floris? Blood is thicker than water gaskiya, dik yadda aka yi suna da alaƙar jini mai karfi, za dai muga ta ina wannan alaƙa zata fito gaskiya, ko da yanayin yadda na faɗi Ronnie zaku san yana kama da Sweetie sosai.

Da kyar barci ya É—auketa, shi ma sai can wuraren asuba haka. Shi dai Black Tiger dik wannan bidiri da ake yi bai da labari, yana can hankalinsa a kwance yana barci, Sweetie na can tana mafarkin ya shanye mata baki!.

🔥🔥KINGDOM OF POWER🔥🔥

Fitowa ta yi daga cikin toilet É—insa É—aure da towel a chest É—inta, yanzu kwata kwata ta dai'na fita waje, kusan a cikin bedroom É—insa take wuni, saboda takunkumin da ya sanya mata, yana tsoratar da ita.

A maimakon ta sanya kaya anjikinta, sai ta faɗa saman bed ɗinsa haka nan tare da minginawa ta ƙudundune jikinta a cikin bargo, lokaci guda ta saki siririn murmushi tana kallon sama, yau wani irin nishaɗi na musamman take ji! Kamar ba Pretty tamu ta zamani ba!. Ta yi nisa a cikin halin da take sai ganin mutum ta yi a saman bed ɗin yasa hannun yana ƙoƙarin janyo bargon da ta rufe jikin nata da shi, ƙoƙarin hana shi ta yi ta hanyar juyawa, sai shi kuma ya matsa ya yi mata rumfa da faffaɗar kirjinsa.

Turo baki ta yi kafin ta ce. "Ni banaso, dan Allah kada ka taɓa mun bakina". Harara ya dalla mata kafin ya sanya hannu ya janye bargon kasa gabaɗaya, ya rage daga ita sai towel ɗin da ya haura sama gabaɗaya santala-santalan cinyoyinta a waje!.

Jan dogon numfashi ya yi tare da saukewa a hankali, hannunsa ya É—aura a saman cinyar tata ya É—an shafa tare da lumshe idanu alamar abin ta kai mashi karo!.

Me kuke kallah my people's? Na ce me kuke kallah a nan? Maza ku ware! Matarsa yake latsawa ba kowa ba, dan haka bamu san sa ido. Kwarai kun jini da kyau matarsa na ce!! Ya aka yi tazama matarsa, na san tambayar dake ranku kenan, ku bari idan lokaci ya yi zaku san yadda aka yi, babu wanda yasan matarsa ce sai ni, shiyasa nima na sanar da ku, ko momma fa bata sani ba wlh, ita kanta Prettyn bata sani ba, amma tabbas matarsa ce ta sunnah ma kuwa, ɗan rainin wayo shiyasa yake abin da yaga dama da ita, momma ta tambaya kuma ya ce wai ba haka ba, wai my people's a ina kuke har Smart ya mallaki Pretty baku sani ba? Gaskiya ba zan sake bari a yi maku rufa rufa ba, zan rinƙa buɗe maku kun ji ai!. Uhm King yana can yana nema mashi auren Sareena, shi kuma ya yi son ransa da ƴar babyn matarsa mai sakalci da shirirta, ga Mom ta tsaya nema mashi auren Heleena, dik ashe ya manna masu hauka ne, zaɓin Mommarsa ya ɗauka ya rabu da King and Mom, Smart ya cika ɗan halak mai son farincikin mahaifiyarsa mai kuma bin umarninta, ta umarcesa a kan Pretty kuma ya bi, surprise yake san yi mata mai zafi shiyasa yaki faɗa mata cewa matarsa ce, amma ya kuke tinanin King zai karɓi wannan al'amari? Shin zai yarda kuwa? Kada ku manta ya rigada ya karɓa mashi auren Sareena fa!.... QUEEN OF SURPRISE NIKE, yau ma na tashi kanku da batun auren Smart and Pretty, ko ya hakan ya kasance, amsar zaizo maku daga bakinsa a time da yake sanar da Mommarsa, uhm akwai kallo fa! Bala'i Pretty bata san cewa ita ɗin mallakinsa bace!!!.

Yunƙurawa ta yi zata miƙe ta bar wajen, hannu ɗaya yasa ya mayar da ita ya kwanta tare da kai hannu zai warware towel ɗin, dik iskanci da rashin jinta ashe tasan suturta tsiraici, a miliyan ta sanya hannu ta damki towel ɗin nata tana ƙoƙarin zunduma mashi ihu. Cikin sanyin murya ya ce. "Kina buɗe baki zan kira Tiger, kuma ki cire mun hannunki daga wajen".

Shiru ta yi tana girgiza kai ta fasa yin ihun, saboda tsoron Tiger yasa ta zame hannunta daga rikon da ta yi wa towel É—in, take idanunta suka ciko da hawaye. Banza ya yi da ita tamkar bai ga hawayen ba, cikin natsuwa ya sanya hannu ya warware towel É—in gabaÉ—aya ya yi mata zindir.

Tsabar tabbatar duniyanci irin na Smart sai yasa hannunsa yana kewaye Æ´an matasan tula tulanta yana kallon face É—inta. "You toooooooooo small for me! Shekarunki nawa?". Ya yi maganar yana mai da hannunsa saman lipa É—inta. Hawaye ne suka fara gangarowa a idanunta, kun san dik yadda mace take da san bayyana tsiraicinta wlh a lokacin da tula tulanta suke tasowan girma ta tsani a kallan mata su, amma saboda iskanci irin nasa, ya san da hakan sarai, kawai dan ya bakanta mata rai ne ya buÉ—e mata su.

"Mena yi maki da kike kuka?". Ya faɗa a ɗan kausashe. Wai a cewarsa yanzu zai reneta ne sai ta girma, amma kunga ɗan rainin wayo yana shanye mata baki, daga reno kuma ana ta...............🤫

Kai ta girgiza mashi alamar babu abin da ya yi mata.
"Baki da bakin yin magana ne?". Da kyar ta iya ce mashi tana da shi. "To idan na sake yi maki magana kika amsa mun da kai ba ki buÉ—i baki kin yi magana ba sai na yi maki irin ta jiya". Tana ruwan hawaye ta ce to.

Munahiki har cikin ransa yake jin sugar kallan surar jikinta, amma saboda iskanci wai renonta zai yi, gabaÉ—aya hankalinsa a tashe fa yake, dik abar ta motsa, har idanunsa sun kaÉ—a sun yi jajir kamar wuta, yana wani ciccijewa. Uhm to malam Smart mun dai san komai! A dai'na wani shassha mana kamshi ana wani É—aÉ—É—aure mana fuska.

(Kambalai kun san me na tina? Yadda haÉ—uwar Pretty and Heleena zai kasance, ga Sareena a gefe, yadda Heleena ke mutuwar son Smart anya akwai zaman lafiya kuwa? Ga shi su turawa mata É—aya suke yi, idan Heleena ta san ya yi aure shikenan tasan ba zai kara wata mata ba sai dai idan kashe Pretty zata yi sai ya aureta, akwai badakala! Pretty dake son Kamran kuma shi aka bata ya kuke ganin wannan bidir zai faru idan tasan ita matar wani ba Kamran bane?!)
Chapter 234 · 0% Book details