Sashe 211
Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Wallahi billahi ni na haifeka Ramish, meyasa kake tantama?!!". Daga yadda ta yi maganar ya fahimci da iya gaskiyarta ta yi, dan haka ita ta haifesa, sai dai idan Dr Raj ne ba ɗanta ba, dole akwai wata a ƙasa. "To mama Raj..........." Ƙasa ƙarisa tambayar ya yi, dama zai tambayeta ita ta haifi Dr Raj ne, sai kuma ya tina yanzu zata iya zargan wani abu, shi kuma bayan Smart baya san kowa yasan abin da yake faruwa bare har su ɗaga hankalinsu haka, ta haka ne kawai zai iya cin nasara a aikinsa, rufe sirrinka shi ke kaika ga nasara, and kuma ya tina yana da jinin Dr Raj a bedroom ɗinsa a gidan Abu Abdussalam, yana nan a ma'adanarsu na gwaje-gwajen lafiya, ya taɓa gwada shi a lokacin da ya yi wani ciwo, a lokacin sun tsorata sosai, sai suke ga kamar yana shan miyagun kwayoyi shiyasa suka yi mashi gwaje-gwaje sosai shi da Bilal.
Tina yana da jinin yasa ya fasa yi mata tambayar tare da kawar da zancen zuwa zancen gidan da abubuwan da suke faruwa, a zuwan zai je gobe ya ɗauko jinin ya zo ya gwada ya gwada nasa sai ya tabbatar, ya so ma da ya samu jinin mamar tasu, dan ya kara samun tabbaci, lallai da wuya ne idan Dr Raj ɗanta ne, akwai dai wata a ƙasa.
Zama a gefen bed Leesharh ta yi tana ta kallansa yadda yake waya da mamarsa a natse. Bayan ya kammala ya katse kiran, zubawa kansa ido ya yi yana tinanin kalaman yayansu, wato Smart, a kullum yana faɗa mashi kada ya yi saurin yanke hukunci a aiki, ya koyi hakuri da danne abubuwa game da zurfafa bincike, ya zamana mai tsananta bincike da rufe sirrin dik abin da yake yi, shiru ita ce babban makaminsu a matsayinsu na jami'ai, idan yana zargin na kusa da shi, kada ya kuskura ya bari su iya gane yana zarginsu, ya yi masu sillent walk wajen kamasu, ya barsu su cigaba da rayuwa da shi kamar yadda suke a baya, amma shi yasan irin takunsa a kansu, yana lallaɓawa wajen bincike a natse ta yadda zai haɗa hujjojin da idan ya yi masu kamu ɗaya ba zasu sake dawowa ba!!.
Tuna waÉ—an nan kalamai na Smart yasa shi sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da furta alhamdulillah. Yana furta hakan ya ji sanyi ta ratsa zuciyarsa, a hankali ya É—ago da kallansa a kanta ta cikin mirror, while ita ma shi take kallah, zubawa juna idanu na Æ´an mintuna suka yi, ta shagala da kallan kyansa sai jin sexy voice É—insa ta yi ya ce. "Zaki iya bani haÉ—in kai a yanzu dan mu iya kamasu?".
Kai ta gyaɗa mashi alamar e, dan yanzu ta fara tsorata da al'amarin mutanen nan, kuma ita suke hari sosai, dan sun san ta iya ganesu, idan basu gaggauta kawar da ita ba zata tona asirinsu, ai kun san da suna ganin kamar bata da hujjar nunasu ko da an kamata ne, shiyasa suka saki jiki, amma sai suka ga ba haka bane, kuma ita ma Leesharh ta yi babban kuskure! Domin ba'a nunawa mutane irin wannan cewa ansan wani abu a kansu ko kuma za'a iya fito na fito da su, kun tuna lokacin da suka kirata tana gidan Abbie?. Ba ta ce masu tana da hujoji a kansu har da recoding ba? To wannan shi ne babban kuskuren da ta tabka, da ta yi shiru bata sanar da su cewa tasan wani abin ba, da wlh ba zasu nemi rayuwarta har haka ba....... Ku ɗauki darasi a nan, kuskure ne faɗawa wani abokin faɗa naka cewa kasan wani abin a tattare da shi wai dan ka yi mashi barazana, idan har baya san wannan abin ya fita a duniya to tabbas zai iya cutar da kai koma ya yi ƙoƙarin kawar da kai wa duniya, ba a iya labari ba, a gaske ma ya fi faruwa! Kowa ya iya harshensa, sai dai a ga komai a aikace kamar yadda Smart ya bawa Ramish shawara! Kuma kamar yadda Smart ɗin yake yi! Kun taɓa jin ya faɗi shirinsa wa wani ne? Ai sai dai ku gansa a aikace kawai!!.
"Bari in yi wanka in zo sai mu fara aiki ko?". Ya faɗa yana kallanta. Jinjina mashi kai ta yi. Toilet ya nufa, har zai shiga kuma sai ya tina da dattijuwar dake gidan, wani zuciya ce ya ce mashi ya je ya dubata, wani kuma ya ce to ya bari sai ya yi wanka, hakan kuwa aka yi, ya ce bari ya yi wanka ya fito. Yana shiga toilet Leesharh ta miƙe ita ma, dik da a tsananin tsorace da gidan take hakan bai hana ta daure ta nufi toilet ɗinta ba, dan ita ma ta yi wanka.
After some minutes ta fito shirye cikin kayan barci riga da wando masu covering jiki yadda yakamata, ta ɗaura Arabian hijab a saman kanta, kwata kwata hijabin bai wuci zuwa kirjinta ba. Kitchen ta nufa ta ɗauko cappuccino cup ɗaya da plate na small chop, sai tashin kamshi take yi ta nufi stair case ɗin, tana tafiya tana waige waige, tsabar tsoro sai ji take yi mamar ana bin bayanta. Dai'dai zata wuce bedroom na wannan dattijuwa ta nufi nasa sai ta ji kamar motsi a ciki. Dakatawa da tafiyar ta yi, a hankali ta lallaɓa ta matsa jikin kofar. Ajiye cup and plate ɗin hannunta a kasa ta yi, kamar wata ɓarauniya ta sanya hannu ta ɗan tura kofar bedroom ɗin kaɗan ta buɗe!!.
Ai bata san lokacin da ta zaro ido saura kaɗan ta zunduma ihu ba. Matashiyar mace da bata haura 23 years ba ta gani tsaye a tsakiyar ɗakin, tana sanye da irin fighter wears ɗin nan a jikinta, rike take da waya tana magana ƙasa ƙasa alamar munafurci take kullawa. A hanzarce Leesharh ta juya kallanta izuwa kan gado, nan ta hango kayan dattijuwan, wato kenan matashiyar yarinya ce ta yi shigar dattijai ta shigo cikin rayuwarsu ita da Ramish? Sai a yanzu Leesharh ta tina wannan dattijuwa ai sun jima tare da ita a gidan Abu Abdussalam, kenan dama ashe ba dattijuwa bace?. No wonder take iya aiki lafiya lou ba tare da ta nuna gajiya na tsufa ba, babbar magana, yarinya ce kenan ashe, kam bala'i lallai masu nikaf basu fitowa ba sai da suka shirya, ashe suna da gaskiya da suka ce suna da mutane dayawa a gidan Abbie. Shi Ramish ya kalli dattijuwa ce shiyasa ya ɗaukota ta kula da Leesharh, a tinaninsa tin da tsohuwa ce ba zata yi wani mugunta ba, bai san ya tabka babban kuskure ba!!.
Zuba mata idanu Leesharh ta yi tana karantar bakinta abin da take faɗe....... "Dikkansu suna cikin koshin lafiya fa, babu abin da ya samesu, sai kun kara zazzafar shiri a kansu!!". Shi ne abin da Leesharh ta iya karanta daga bakinta na abin da take faɗe. Saura kaɗan ta zunduma ihu saboda tashin hankali, mamakinta ma ɗaya shi ne yadda wannan matashiya ta yi shigar tsofaffi, ba zaka taɓa cewa ba tsohuwa bace, har da wani ɗan duƙawa idan tana tafiya, wato idan mutane suna san abinka sun fika dabara, ji zukekiyar budurwan nan fa, amma suka mai da ita tsohuwa, har da tamu tamun fata suka saka mata, kai mutum abin tsoro ne, babu mai iyawa ɗan adam sai ALLAHN da ya haliccesa.
Ta shagala da tinane-tinanen da take yi sai gani ta yi dattijuwa zamu ce ko matashiya yanzu kuma?. To oho dai, sai ganinta ta yi ta katse kiran ta nufi wajen bed ɗin, nan ta ɗauki kayanta na dattijuwan ta fara maidawa jikinta, da alama wanka ta yi, shiyasa ta cire kayan. Wani irin zaro idanu Leesharh ta yi tana ganin yadda budurwa take rikiɗewa izuwa tsohuwa cikin ƙanƙanin lokaci, amma sun iya shiri, harta fatarta mai tamu tamun ma ashe ba fatar gaske bace, ashe sakawa aka yi, yanzu ga shi ta ɗauko shi tana mayarwa, har farin gashin kanta ashe attachment ne, shi ma ta mayar. Take ta koma ainahin tsohuwa. Tsabar tashin hankali Leesharh bata san lokacin da ta saki kofar ta dafe kirjinta ba, da karfi yake buga mata ne. Baya baya ta fara komawa har ta isa wajen stair case ba tare da ta sani ba.
Ta jima a tsaye a wajen tana tinanin meyakamata ta yi kafin nan ta dawo ta ɗauki cup and plate ɗinta ta nufi bedroom ɗinsa, wani ɓangare na zuciyarta tana faɗa mata da ta sanar da shi, wani ɓangare kuma yana faɗa mata a'a ta bar abin zuwa gaba su ga me zai faru!. Zuciyarta cike da zulumi da wannan tinani ta ƙarisa bedroom ɗinsa. Bakinta a ɗauke da sallama ta tura kofar ta shigo. Yana zaune gaban bed yana duba wasu hotuna na Bilal da masu nikaf, ganinta yasa ya ɓoye hoton da Bilal yake a ciki a karkashin latop ɗin dake gabansa, da alama baya san ta fahimci Bilal yana cin amanarsa.
Saman table ta É—aura cup É—in cappuccinon, cikin sanyin murya ta ce. "Good evening Yah Ramish". Ta yi maganar tana satar kallansa, wai good evening kamar ba yanzu suka rabu ba, dik fa ta shiga ruÉ—ani da tashin hankalin abin da ta gani ne yasa sam ta mance da yanzu suka rabu.
"How was your day?". Ya faÉ—a ba tare da ya juyo da kallonsa kai tsaye a kanta ba, amma yana satar kallanta ta witsiyar ido, shi ma ya biye mata ya bata amsa ba tare da yasan a ruÉ—e take ba.
Alhamdulillah ta amsa mashi da shi kafin ta juya ta nufi waje tana faÉ—a mashi ga cappuccinon nan ta kawo mashi, sam fa ta mance da zasu yi aiki, da alama wannan dattijuwa ta rikitar mata da tinani sosai.