← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 209 OF 242

Sashe 209

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Ke zonan!". Ya faÉ—a with harsh voice, wai irin ta san ba da wasa yake yi ba, ta tsorata ta zo. Banza da shi ta yi tana cigaba da tafiyarta zata fita. Dab zata fita sai ji ta yi an damko gashin kanta ta baya. Wani irin kara ta saka mashi saboda zafi tare da juyowa da sauri. Angry face É—insa a É—aure tamau, in a harsh voice ya ce. "Ina kiranki kina tafiya ni sha'anki ne?". Ya yi maganar ba tare da ya saki gashin nata ba.

Tana turo baki tana yamutse fuska saboda zafin damkar gashin nata da ya yi ta ce. "Ai ke na ji ka ce ta zo ba ni ba, ni sunana Pretty, da Pretty ka ce da na tsaya ko ban zo ba". Kam bala'i, lallai Pretty ƴar duniya ce......... 😅

Rasa abin faɗe ya yi, dan wlh idan ya biyewa yarinyar nan mari ɗaya zai yi mata ta mutu........... "Ni ka sake mun gashi kada ka cire mun su, zafi yake mun". Shagwaɓaɓɓiyar voice ɗinta ta daki dodan kunnensa. Ɗan sauko da kallonsa a kanta ya yi, da karfi ya sake jan gashin nata baya dan mugunta. Hakan yasa ta ɗaga kanta sama dan dole. Ɗago kanta yasa ya kalli face ɗinta a kurkusa, har cikin zuciyarsa ya ji wani iri na ganin kwayar idanunta, ga idanun fari tas tamkar audiga, kwayar olive ɗin kuma ya tura kala sosai, pink lips ɗinta ya tura sosai shi ma, dik yadda aka yi bata jima da yin wanka ba, soft skin ɗinta sai sheki yake yi yana wani glowing. Yaran nan Sweetie and Pretty sun mori jiki sosai, shape ɗinsu tamkar su suka yi wa kansu!

Ya shagala da kallanta sai ji ya yi ta gabza mashi cizo a hannu, wai dan ya ja mata gashi ta ji azaba sai ta kama É—ayan hannunsa ta gabza mashi cizo da karfi kuma taki sake fatar, sai kara datsewa take yi da hakwaranta. Zuba mata idanu ya yi yana kallanta ba tare da ya saketa ba, tinanin abin da zai yi mata yake yi, dan dole ya hukuntata!.

Da taga cizon kamar bai wadatar ba, bai saka shi ya sakin mata gashi ba, sai ta sake shi haɗe da dunkule ƴan hannayenta da basu wuce ya kama ya karya ba ta fara kai mashi duka a damatsan hannunsa. Abin ma gwanin ban dariya, wai ita nan dukansa take yi dan ya ji zafi ya saketa, bayan hannun nata ba auki kamar sandan snooker. Siririn tsaki ya ja kafin ya sa hannu ɗaya ya ɗagata cancak kamar ƴar tsana ya wurga a saman bed ɗinsa kamar wata kayan wanki. Tana ƙoƙarin miƙewa ya daka mata tsawa a kan ta zauna. Ai ina bata tsoron tsawar tasa, dan haka ta yi tashinta, yana tsaye ta zo ta wucesa zata fita.

Juyowa ya yi yana kallan yadda take tafiya ko a jikinta, yau ta goge mashi hadda, wai me zai yi wa yarinyar nan ne ta fara jin tsoronsa? Shi kowa a gidan nan yana tsoronsa amma ban da yarinyar nan, ita dik wasu tsawa da hargagi game da jan ido dik bata tsoransu. Ganin zata fice daga É—akin ba tare da ya hukuntata bane yasa ya ce. "Yauwa my tiger come in.......".

Ai bai gama rufe baki ba ta watso a miliyan ta juyo, ihu ta zunduma tare da ɗale jikinsa, ta ƙanƙame shi gam tana faɗin. "Dan Allah Yah Omerish ka ce kada ya shigo, wlh cinyeni zai yi"...... Mamaki ne ya kama shi, ashe tasan sunansa Yah Omerish kenan, wato dama iskanci ne ya yi mata yawa a kai kenan? Wannan yarinya wlh sai shirin Allah, shi ya rasa ma me zai ce mata, ta wani ƙanƙame shi, wato dai bata tsoron mutane sai dabbobi, yanzu ya gane me zai rinƙa yi mata, dole ya ɗauko abubuwan tsoro ya kawo nan dan ta rinƙa respecting ɗinsa idan tana san zaman lafiya.

Ihun da take ta zundumawa ne ya farkar da shi daga duniyar tinanin da ya afka. A ɗan tsawace ya ce. "Sauka mun daga jiki ki je Tiger na jiranki a bakin kofar shigowa, ba ke bakyaji ba?". Kara ƙanƙame shi ta yi tana cusa kanta a kirjinsa ta ce. "Yah Omerish wlh ina jin magana, dan Allah ka ce ya tafi, wlh ba zan sake ba". Bilhakki da gaskiya take ihun nata!!.

"Kin yi alkawarin zaki rinƙa jin magana idan aka yi?". Kai ta shiga gyaɗa mashi da sauri sauri, tana faɗin ta yi. Hannu yasa ya rungumota a jikinsa sosai ya fara faɗin. "To ki yi shiru ihun ya isa haka kada ki tara mana jama'a, zo ki zauna mu ci abincin a tare". Kin sake shi ta yi, sai dai ta dakata da zunduma ihun, cikin shesshekar kuka ta ce. "To ka ce kada Tigern ya shigo ka ji?". Yadda ta yi maganar har cikin zuciyarsa ta ratsa shi, ga shagwaɓa ga muryar kuka, abin sai ya haɗe. Nisawa ya ɗan yi kafin ya ce. "To ba zai shigo ba, amma idan kina ihu zai shigo ne, sakeni mu je ki ci abinci". Wato shi ma yasan ita sarkin son abinci ne fa!.

Ba musu ta sakesa tana shessheƙa. In short a tare suka ci abincin, kuma wunin ranar a bedroom ɗinsa ta wuni har dare, taki fitowa wai kada Tiger ya kamata, shi kuma yaki zuwa ya je ya rakata, dan bashi da matsala na zamanta a bedroom ɗin, tana ma ɗebe mashi kewa ne, da rana ta yi sanyi ma hayewa saman bed ɗinsa ta yi a kusa da shi ta kwanta, ba jimawa barci ya yi awon gaba da ita.

--------------------------------------🔥

A takaice tsawon sati biyu Auta tana jinya, ban da uhm da mmm babu abin da take cewa, tana kwance shiru a wannan part ɗin, Abdussalam sai ƙoƙarin shiga ziciyarta yake yi ta hanyar zuba mata kalamai masu sanyi da tausasawa game da kulawa, amma dik taki kula shi, sai ma layi da ya shata mashi a kan kada ya kuskura ya matso kusa da bed ɗinta, bai yi mamaki ba, dan yana tinanin zafin ciwo ne, shi kwata kwata bai san da batun soyayyarta ba, wlh da ya sani ko kaɗan ba zai taɓa yarda su yi aure ba, yana san farincikinta sosai, so bai sani ba, ya zaci kawai bata son ayi mata aure a yanzu ne, shiyasa idan ya zo wajenta yake yawan ce mata kada ta damu shi zai iya barinta har ta kammala karatunta kafin su yi zaman aure, dan hankalinta ya kwnata har ce mata yake yi zai iya barinta a kingdom of power cikin ƴan uwanta ya koma Dubai, dik dan ta samu farinciki, amma ina, ita dik ba wannan ne a gabanta ba, hankalinta ya yi nisa, wai a haka ma bata san Hoorain ya mutu ba, ta yi alkawarin babu wani namijin da zata mallakawa jikinta, a cewarta zata yi ta avoiding ɗin Yah Abdussalam har ya gaji ya sawwaƙe mata ta kawo kanta ga Hoorain ɗinta, ta ci alwashin in dai Hoorain bai sameta ba, to tabbas kashe kanta zata yi, dan jikinta mallakinsa ne, ta yi mashi wannan alkawarin tin tana France. Ya kuke tinanin zata ji idan ta san ya mutu? Anya ita ma zata rayu kuwa?!.

A ɓangaren Smart kuwa, wlh yadda kuka san baya gidan, kuma dik abin da yake faruwa yana sane, amma bai shiga harkarsu ba, ya zuba ido, sai dai kuma kamar akwai abin da yake shiryawa daddyn nasu, dan ya ɗaukarwa kansa alkawari idan King ya yi sanadiyar mutuwar Zunaira to tabbas wlh ba zai rabu da shi ba, kuma ya san in dai tasan Hoorain ya mutu da wuya ta tsallake ita ma. Uhm akwai cakwakiya fa!!.

Cigaba da rayuwarsa Smart ya yi, sai kiransa daddynsa yake yi yana cewa ya dawo, amma sam babu alamar komawa, dan ya ce ba zai bar kingdom of power ba har sai ya gyara masu zama, azumi ta iso, Momma zata je Dubai gaisuwar azumi, sai ana gobe za'a ɗauki azumi zata dawo, to shi ne abin da Smart yake jira, so yake yi momma ta tafi, sannan su yi uwar watsin da za'ayi, kunga bata nan bare ranta ya ɓaci ya ji babu daɗi!!.

Uhm Zunaira ta shafe two weeks a saman gadan jinya ba tare da sanin Hoorain baya raye ba, tana nan tana tattalin soyayyarsa a cikin zuciyarta, ta yi mashi ginin da babu mai iya rusa mata!! Kullum tana kan ƙoƙari kara yawan son nasa a ranta!! Ba ci ba sha, dik ya rame ta lalace fiye da tinanin kai tinani, bata da wani walwala, wannan ma wai dan su Chuchu sun ta ƙoƙarin kwantar mata da hankali, wlh shi kansa King tsoron zuwa dubata yake yi, saboda yadda ta rame bata a cikin hayyacinta, abin ya yi mugu mugun taɓa shi, sai dare yake zuwa dubata, har a yanzu yana ganin kamar idan aka ja lokaci kaɗan zata miƙa wuya ta hakura, shiyasa bai fara nadama ba, ban ji kamar bai kyauta ba, ya cigaba da tinanin dik in da aka yi one month zata mance da komai ta fara sabuwar rayuwa da Abdussalam. Uhm akwai cakwakiya sosai!.
Chapter 209 · 0% Book details