← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 242

Sashe 12

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Mahreen ki dawo nan kada ki yarda ki bisu".
Nennen da ranta ya gama ɓaci, ta kawo har wuya ne ta faɗi haka, tana da bala'in son girma, amma sai dai bata san ta yadda zata bi da mutane su girmamata ba, yau ga shi ƴar cikinta ke gaya mata ita ce munafuka kuma ma gulmaciya, me ya kai wannan ciwo fisabilillahi? Alhaki ai kuykuyone, ga shi ta fara gani.

Ina kafa me na ci ban baka ba? Kafin Nenne ta dasa aya a maganarta ma Mahreen ta kurewa ganinta, kamar wata haske ta wuce fiwwww, yarinya mai saa mai kuma baiwar iya gudu.

Galala Nenne ta saki baki tana jin ɗacin maganganun Mahreen a ranta, karin ɓacin rai ma shi ne yadda Mahreen ta haɗe har da gwaggo ta zage, abin ya bakanta mata matuƙa.

Ta É—an jima tsaye a wajen tana tunani, wucewar da Mairo ta zo zata yi a kusa da ita ta É—aga mata gaisuwa ne ya fargar da ita ashe a kan hanya take tsaye.

Wani irin ƙasƙantacen kuma walaƙantatcen kallo ta bi Mairo da shi, bata amsa gaisuwar Mairo ba, sai wani kallon up and down da take binta da shi, ashe a wajenta Mahreen ta gaji irin wanna walaƙantatcen kallo da take yi wa mutane, wlh dik yadda kake ji da kanka idan aka yi maka irin wannan kallo sai ka ji kamar kai ba kowa bane, ka ji ka kaskanta ka walaƙanta, sam kallon bashi da daɗi.

Ganin haka yasa Mairo ta nufi kama kanta ta wuce, salum alum ta kama hanya, dama tasan Nenne bala'i ce, ta gaisheta ne kawai dan kada ace ta ganta bata girmamata ba.

"Ke zo nan?". Cewar Nenne.

Ba musu Mairo ta juyo ta dawo wajen ta tsaya, cikin sanyin murya ta ce. "Adda gani nan......."

Bata idasa maganar ba ta shanyeta dif sakamakon wani bahagon marin da Nenne ta sakar mata tasssss. Nenne bahaguwa ce, haka yaran ArÉ—o dikka suke lefty, harta Ibrahim bahagone, hakan yasa Mahnoor take bahaguwa ita ma, ta gada wajen mamarta, ArÉ—o shi ne ainahin bahago, so a wajensa suka gada.

A miliyan Mairo ta dafe ƙuncinta, take wasu zafafan hawayen suka faso idanunta a guje suka fara tsere a saman kumatunta, jikinta har ɗan kerma yake yi, hannun da ta dafe ƙuncinta sai rawa yake yi.

Tsabar masifa da rashin kunya irin na Nenne wai ƙoƙarin kara mata marin take yi, daga bayansu suka ji muryan bappa yana faɗin.

"Kada ki kuskura ki sake marinta". Cikin zafi ya yi maganar, ya jima bai zafafa a magana irin haka ba, tun maman Mahnoor tana nan, yau ransa a ɓace ne yasa ya zafafa.

Sanin halinsa da kuma jin ya zafafa yasa Nenne bata kara kai mata marin ba, dan tasan fa bappa ruwa ne ya daki babban zakara yasa ya yi sanyi.

"Jeki abinki Maryam". Ya yi maganar ne yana kallon Mairo da idanunta suke jajir, dan fa ba karya ta maru sosai.

Wucewa ta yi ba musu, dan tana da ladabi da biyayya. Shi ma bappa zuwa ya yi ya wuce Nenne tsaye a wajen kamar gunki bai ce mata uppan ba ya nufi hanyar gidansu Faisal, dan bappan Faisal ya aiko ya zo yana son ganinsa.

Bakinci ta kara taruwa ta yi wa Nenne kaho a wuya, ta rasa da wanne ɗaya zata ji! Wata zuciya ta ce mata ta bi bayan bappan ta je cikin mutane ta ci mashi mutunci ko zata huce haka nan. Wani zuciyar kuma ya ce ta bi bayan Mairo ta laƙƙaɗa mata ɗan banzan duka, hakan zai sa ran bappa ya ɗacaca sosai. Wani zuciya ya ce ta koma gida dik zasu zo ne su sameta tun da gwaggonta ta yi mata alkawarin zata murza kambunta, zata baza mulki a cikin gidan.

Tunani dai kala kala cike fal a ranta ta rasa madogara, sai zallar mugunta a bakar zuciyarta.

Daga ƙarshe dai da ta ga babu sarki sai Allah, sai ta shafawa kanta ruwan sanyi ta nufi gida tana ta wani kunkuni tana tsinewa bappan da bai san tana yi ba a cikin zuciya.

============🔥😥💔============

BLACK WORLD🔥

Shiru Sweetie ta kwanta saman bed É—in Ronnie tana tunanin duniya, su kuwa suna church. Can tunanin kyan Black Tiger ya ratso mata ta cikin kwakwalwarta. Ai a miliyan ta tashi zaune tana É—an sake fuska.

Can sai ta fara ganin shi a idanunta yana yi mata gizo, ta mutu a kan romance pink lips É—insa.

Zuro ƴan kafafunta kasan bed ɗin ta yi, sanna ta diro ƙasa, dan gadon yana da tudu sosai. Da sauri ta miƙe tsaye ta nufi wajen glasses da ta gani kusa da tampatsetsan mirror.

Takardu ne cike tab a cikin glasses É—in, su handout, Bible, drama books, text books da dai sauransu, Ronnie akwai san karatu sosai, shiyasa yake da tarin takardu sosai.

Ƙoƙarin buɗe glass ɗin ta yi a tunaninta dan ta duba ko akwai hotunan Ronnie da yayan nasa, sai dai abin da bata sani ba shi kansa Ronnie ranarsa ta farko ce na ganin yayan nasa a lokacin da ta gansa.

Kasa buÉ—e door É—in ta yi, dan komai nasa mai mahimmanci killace yake da securitys.

Sam bata ji daÉ—in hakan ba, dan ta so ta gansa. Gaban mirrorsa ta nufa dan ta ga kanta ko zata rage kewar Pretty da take ji.

Hannayenta dikka biyu ta sanya ta dafe saman glass na saman table É—in mirror, ta zubawa kanta idanu ta cikin mirror tana kallon kyan da ubangijin talikai ya yi mata.

Tunanin yadda kamannin Kamran É—inta zai iya kasancewa ne kawai ya faÉ—o mata a ranta, da shi take kwana take kuma tashi.

Kamar walkiya haka ta ga mirror yana ƙoƙarin darewa gida biyu, da farko ta ɗan tsorata, sai kuma ta dake tana cigaba da kallon mirror babu ko kyaftawa.

Kamannin face É—inta a jikin mirror ne ya fara sauyawa izuwa wani kamanni na daban, still bata tsorata ba, sai kara zaro idanu da ta yi tana cigaba da kallon kanta.

A hankali ta cigaba da rikiɗa tana canzawa izuwa kamannin da bata taɓa ganin irinsa ba.

Wani irin haske ne ya bayyana ta cikin mirror wanda yasa ba shiri ta É—aga hannayenta izuwa saman face É—inta dan ta kare idanunta daga samun matsala ta dalilin wannan haske.

Buɗe tafukan hannunta da ta yi wajen ƙoƙarin rufe face ɗinta ne ya yi sanadiyar bayyanar nata magic ɗin ba tare da ta sani ba.

Bata ankara ba sai ji ta yi wani irin tsawan tarwatsewar mirror ya daki dodan kunnenta.

Watsa watsa mirror ya yi a ƙasa, karfi ne ya haɗu da karfi, fitar magic ɗinta yasa ya haifarta wannan, dan hasken nata ya haɗe da wannan haske da ya fito ta cikin mirror, kuma nata yana da matuƙar karfi na ban mamaki, shi ne sila.

A miliyan ɗari ta yi kasa da hannunta a in da ta waro idanu tana kallon yadda mirror ya yi watsa watsa, haƙiƙa a wannan karon ta jijjiga sosai, ba ita kaɗai kuma ta jijjiga ba, har da shi Black Tiger sai da ya jijjiga, dan kuwa fashewar mirror nan ba ƙaramar abu bace a wajensa, ba mirror ce kamar kowanne ba, bai taɓa zaton zata buɗe tafukan hannunta magic ɗinta ya fita ba, da bai yi ƙoƙarin razanar da ita ba.

And bugu da kari unexpect magic É—inta ya daki saitin zuciyarsa, kafin ya farga ya kare kansa haskenta ya tarwatsa tasa da har ya É—an yi baya kaÉ—an, ya ji hakan a jikinsa sosai, sai dai kuma, a take ya juya magic eyes É—insa ya kusar da raÉ—aÉ—É—in da ya ji.

Zuciyarsa ta bakanta sosai a kan hakan, ba'a taɓa wanda ya taɓa gigin yi mashi abu makamancin hakan ba, dan haka sai ya kudurta a ransa dole ya hukuntata ya kuma durkusar da magic dake jikinta.

Ita kuwa sai ƙoƙari take yi ta fahimci abin da ya faru da har ya kawo tarwatsewar wanna mirror haka?.

Ji ta yi É—akin ya fara juya mata, sai ta fara ganin kamar fanka yake yi mata. Da gudu ta bar gaban mirror ta haye saman bed.

Nan take wani iska mai karfi ya banko kofar ɗakin ya shigo, tana ƙoƙarin juyar da kallonta izuwa wajen kofar ba zato ba tsammani ta ji saukar wani mahaukacin mari a kuncinta wanda bata ga hannun mutum ba, bata san daga ina marin ya fito ba.

Tun da take a rayuwarta bata taɓa jin wani abu mai bala'in zafin wannan mari ba, dik da magic dake jikinta hakan bai hana ta ga wani irin duhu ya gilma mata ba, har wani irin jiri mai karfi ne ya ɗebeta daga zaune, na ƴan sakanni ta gaza gane a wani duniya take, kunnuwanta gabaɗaya sun toshe bata iya jiyo sautin komai.

Gabaɗaya kwayayen fitillu masu hasken da suka kawata ɗakin ne suka fara ɗaukewa suna sake kawowa a lokaci guda, dai'dai lokacin da ta dawo cikin hankalinta take ƙoƙarin fahimtar me yake faruwa. Dai'dai lokacin chandelier ɗakin ta jijjigo daga sama ta yo kanta a guje.

Ihu mai sauti ta kurma tare da dirowa kasa daga saman gadon, sai wani irin haki take yi tamkar wadda ta ci uban gudu ta ƙoshi.

Ga mamakinta sai ta ga tana dirowa kasa chandelier ya fasa faÉ—owa saman bed É—in, ya juya ya nufota da karfin gaske.

A juye ta nufi baya baya dan ta fita waje. Sai dai kofar room É—in ya rufe kansa tun bayan shigowar wannan iska da ya jijiigo da chandelier.

Ihu take yi sosai dan bata taɓa ganin iska mai karfin wannan ba, ga shi dik in da ta yi sai chandelier ya bi bayanta.

Kurewa É—akin ta yi a in da ta mannu da jikin bango tana cigaba da ihu.

Ronnie dake zaune saman chair a cikin katafaren church É—insu sai ji yake yi gabansa yana faÉ—uwa, sai ya ji zuciyarsa ta tsinke, kansa yana sara mashi, dik ya sara nutsuwarsa da sukuninsa, yana jin kamar wani abin ne zai faru da shi.
Chapter 12 · 0% Book details