← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 242

Sashe 122

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dakatawa da yin maganar ta yi tana jin wani irin kuna da numfashin wutar nan take yi mata, tana ji a jikinta sosai. Fasa nunata da scepter É—in ya yi, ya dakata yana jin maganganunta. Ganin ya dakata yasa ta ji kwarin gwiwar cigaba da magana, take ma ta ji zafin wutar ya gudu ganin yana sauraronta.

"Baka san wannan rana zata zo ba ko? Baka san akwai wata rana da zata zo da Ubangijinmu zai tara dikkan duniya waje guda ba ko? A ranar Alkiyama, dukkan masu mulki, sarakuna, shugabanni da azzalumai za su hallara a gaban Allah. A wannan rana, babu wani mutum da zai iya da'awar mulki ko iko, domin Allah ne kaÉ—ai zai kasance da mulki da iko. A wannan rana Allah zai ce. Limanil mulku liyawm? Wanenen mai mulki a yau? Hasbunallahu wani'imal wakil. Babu wanda zai iya samun bakin amsawa Ubangiji wannan tambaya, wane mutum, Allah da kansa ne zai sake amsa tambayar da cewa babu wani mai mulki sai Allah subhanahu wata'ala. Wannan yana nufin cewa dukan iko da mulki na duniya wofi ne, sai wanda aka yi da adalci da tsoron Allah, shi ne kawai zai iya zama mulki mai amfani har ranar lahira. Kai da kake zalinci me zaka ce a ranar lahira? Ka tanadi abin faÉ—e ne?!!".

Ta jefa mashi tambayar tana wani irin huci sakamakon wannan wuta, ga kuma kululun bakinciki da ya tirnike mata zuciya. Da kyar ta É—aura mashi da maganar bayan ta É—an huta ta gama sauke numfashinta.

"Idan ma baka yarda da maganata ba to ka duba a cikin Alqur'ani, cikin Suratul Ghaafir, sura ta 40 aya ta 16. Allah ya ce
سورة غافر – آية 16
يَوْمَ هُمْ بَارِزُونَۚ لَا يَخْفَىٰ عَلَى ٱللَّهِ مِنْهُمْ شَىْءٌۚ لِّمَنِ ٱلْمُلْكُ ٱلْيَوْمَۖ لِلَّهِ ٱلْوَاحِدِ ٱلْقَهَّارِ
Fassararta
A ranar da za su bayyana gabaɗaya a gaban Allah, babu wani abu da zai ɓuya daga gare Shi. Sai Allah Ya ce. Wanenen mai mulki a yau? Sai kuma ya amsa da kansa dan babu mai iya amsawa, zai ce mulki nasa ne shi kaɗai, Allah shi ne malikyaumiddin, mamallakin ranan sakamako kenan"

"Kasan me ake nufi da tashin alkiyama kuwa? Kasan masifarta kuwa? Kasan balai'n da tashin hankalin dake cikinta kuwa? Na tabbata da bawa yasan balai'n dake cikinta da ba'a wayi gari da azzalumi ko guda ɗaya ba a duniya, kai koda sau ɗaya a samu wanda ya mutu ya dawo duniya ya faɗawa mutane musifar dake lahira da duniya ta tsabtata daga ƙazantar da take a ciki".

"Amma ni Omaish jika ga Abdul Mutallab ina kalubalantarka da ka je ka karanta suratun Az-Zalzalah (الزلزلة) tana daga cikin surorin da ke cikin Al-Qur’ani mai girma. Tana da ayoyi takwas 8, kuma tana cikin Juzu’i na 30. Wannan sura ta yi cikakken bayani game da ranar tashin kiyama, in da ƙasa za ta girgiza da fitar da dik abin da ke cikinta, wato dikkan mutanen da suka mutu aka binnesu kenan. A wannan rana, kowane mutum zai ga sakamakon ayyukansa, komai ƙanƙantar su. Wannan sura tana ƙarfafa imani da ranar sakamako, kuma tana ƙarfafa mutane kan su aikata alheri domin gudun sakamakon munanan ayyuka, dan haka zan so ka karantata tare da fassararta dan ko ba komai bakar zuciyarka na tabbata sai ta ragu, babu wanda zai ji labari game da lahira zuciyarsa bata kaɗa ba, ko shaiɗan ubanku a zalinci shi ma hantar cikinsa kaɗawa take yi a dik time ɗin da aka yi batu kan lahira".

Ta É—an dakata tana jan numfashi mai fita dakyar sosai kafin ya daure ta É—aura da cewa.

" Bayan suratul Zalzalah akwai wasu surori da Hadisai da suka bayyana Tashin Alkiyama da Masifunta, ina kalubalantarka da ka karanta su dikka. A cikin Al-Qur’ani da Hadisai masu yawa, an yi bayani mai zurfi game da tashin Alkiyama, tsayuwarta, masifunta, da yadda za a yi hisabi kafin Allah ya raba hukunci. Daga ciki akwai suratul Az-Zalzalah wadda take magana a kan yadda ƙasa za ta girgiza kuma ta fitar da abin da ke cikinta. Sai suratul Waqi’ah surata 56 ta yi bayani yadda mutane za a rarrabe su zuwa rukuni uku a kiyama. Na dama sune Ahlul Janna wato ƴan aljanma, sai na hagu Ahlun Naar, ƴan wuta kenan, da waɗanda suka yi wa Allah hidima sosai As-Sabiqun. Sai suratul Takwir sura ta 81, ta yi bayani kan yadda rana za ta narke, taurari su faɗi, da kuma yadda dabbobi za su taru. Sai suratul Infitar, surata 82, ta yi bayani kan yadda sama za ta tsage, ƙasa ta zube, kaburbura su bude, kuma mutane su san sakamakon ayyukansu. Sai suratul Inshiqaq surata 84, ta yi bayani yadda sama za ta tsage kuma mutane su hadu don hisabi".

"Hadisai Masu Bayani Kan tsanani da tsaruwar Alkiyama, masifu da bala’o’in tashin Alkiyama akwai bukhari, hadisi mai lamba 4635, sai Muslim lamba ta 157, Annabi Muhammad (SAW) ya ce. Kiyama ba za ta zo ba sai rana ta fito daga yamma. A cikin Muslim again, a ranar Alkiyama, mutane za su tsaya tsawon shekaru 50,000 kafin a fara hisabi, shekaru dubu hamsin da, ba kuma irin shekarun duniya ba, wuce nan, sannan za'a sauko masu da rana dab kansu, wanda ya yi aikin alkhairi ya bi Allah da manzonsa zai kasance ne a ƙarƙashin inuwar alarshin Ubangiji. (Allah kasa muna daga cikin masu samun wanna ni'imar) Za a yi tambaya kan imanin mutum, ibadarsa, arzikinsa da yadda ya kashe shi, da iliminsa da yadda ya amfani da shi, idan aka yi maka wannan tambaya me zaka ce?"

Ta jefa mashi tambaya tana kallan yadda face É—insa yake kara rikiÉ—ewa. Babu alamar zai iya buÉ—ar baki ya yi mata magana, dan haka sai ta cigaba da cewa.

"Bayan dikka wannan fa akwai hayewa gadar airaÉ—i, kafin nan akwai musifun kabari, kasan me siraÉ—i kuwa?. Annabi (SAW) ya bayyana cewa akwai wata gada mai tsananin siranta da ke kan wutar jahannama, wato gadar Siradi.
Wasu za su haye gadar cikin sauri kamar walƙiya, masu aiki na kwarai kenan, wasu kamar iska zasu wuce saboda tsabar kyan aikinsu, wasu kamar doki, wasu kamar tafiya a kafa, wasu kuwa za su fadi cikin wuta saboda zalincisu. Ga shi gadar tana da kaifi fiye da takobi kuma tana da duhu mai tsanani, kai da kake aikata zalinci me kake tinanin zai faru da kai idan baka tuba ba?". Ta kai karshen maganar tana ciza laɓɓanta da karfi saboda azaban zafin wutar ya kai mata makura.

Allah yasa kun samu karin imani a kan tunatar daku lahira da na yi.💘 Wlh a dik time da na tina lahira sai na ji gabaɗaya duniya ta isheni ta fita a rai'na, sai in ji gabaɗaya na rasa me yake mun daɗi, ranar haka nike wuni sukuku, my people's akwai aiki a gabanmu babba, wlh kiyama ba karya bace, tashin hankalin dake cikinta bawa ba zai iya ɗauka ba, dan haka ku kullu ɗamara domin neman gobe mai kyau, duniya dikka kyalkyali banza ce, ruɗin shaiɗan ne ma yake ƙawata maku duniyar, dan haka ku yi wa kanku kiyamul laili tin kafin dare ya yi maku! Allah kasa mu dace ka yi mana kyakkyawar karshe.

Ƙasa cigaba da yin magana Sweetie ta yi saboda azabar da ya isheta, ta gagara yin magana kuma.

Ga dikkan alamu maganganun Sweetie sun yi tasiri a ransa, saboda kuwa ya tsaya cak ya gagara motsawa, wannan ma a tunaninsa Sweetie tana magana ne a kan Annabi Isa, kun san shi suka ɗauka a matsayin Allansu, so ya zaci tana faɗa mashi Annabi Isa zai tuhumesa a kan zalincin da yake aikatawa ne, dan haka sai ya ji kalamanta sun taɓa zuciyarsa sosai, dama ai komai taurin zuciya sai dai in bata ji batu a kan Allah ba, dole ta yi laushi sai dai idan mamallakin wanna zuciya ya ki yarda ya saduda ne kawai.

Ita kuwa Sweetie a hankali ta fara ganin dishi dishi, kafin wani lokaci numfashinta ya ɗauke cak saboda wutar ta yi mata yawa. A daidai lokacin da numfashinta ya ɗauke a dai'dai wannan lokacin barci ya ɗauke Ronnie kwance a gadan Black Tiger. Bawan Allah aman da ya yi ta shararawa ta jijjiga shi matuƙa, jikinsa dik ya mutu shi ya haifar mashi da barci.

Allah kasa kalaman nan nata su kara tasiri a zuciyar Black Tiger ko dan ta yi nasara, Sweetie ta sha wuyar rayuwa wlh, tun daga forest fa, ga kuma makanta, kai ta wahala fa, ina maganar Allah ba wasa ba wlh, dole zuciya ta girgiza wai dan ma bai da sani a kan hakan, ma'ana bai karanta ya gani muraran ba, ai da yau bashi ba kwanciyar hankali bare barci. Ina matuƙar kaunar part ɗin BLACK WORLD, saboda addinina, Allah ka kashemu muna masu imani da kai.💘

🔥🔥🔥KINGDOM OF POWER🔥🔥🔥

In short, sati guda cur Zunaira ta yi a hospital a kwance kafin ta farfaÉ—o, a cikin sati É—ayan nan abubuwa sun faru wanda suka haÉ—a da kwanciyar commander Zafar a gadan asibiti, yanke jiki ya yi ya faÉ—i tin ranar da King ya umarcesa da ya hukunta Hoorain, suna isa bakin kofar É—akin duhu bayan ya tura Hoorain ciki ya rufe kofar kawai sai ya yanke jiki ya faÉ—i, ranga ranga aka É—aukesa zuwa hospital, yanzu haka satinsa É—aya a hospital amma bai farfaÉ—o ba, doguwar suma ya faÉ—a, bawan Allah.

Sannan ciwon guyson yaki sassautawa har sai da Dr Raj ya bar Leesharh ya tsallako ya taho kingdom of power da kansa domin shi ya saba da yi mashi dik abin da ya dace. Kwana uku da kwanciyar guyson ya yi dirar mikiya a kingdom of power É—in, a ranar da ya zo a ranar ya shawo kan matsalar, amma har yau bai koma ba yana nan, Bilal ya É—auko wasu Drs suna kula da Leesharh a Dubai

Tin ranar da Auta ta dawo Mahnoor bata sake haÉ—a ido da Jaish ba, dan baya zama kwana biyun nan, tin asuba yake fita, baya dawowa wani lokaci sai karfe 12 ko 1 na dare, shi ma aikinsa ta sako shi a gaba.
Chapter 122 · 0% Book details