← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 217 OF 242

Sashe 217

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ÆŠan gudu ya yi ya kamota tare da rike hannunta suka wuce suka nufi gym É—insu. Yana zuwa ya hau motsa jiki, a hankali ya fara cigaba da koya mata, push up ya fara yi, a nan Black Tiger ya zo ya samesu suna yi, bai bi ta kansu ba ya fara nasa gym É—in, tin da ya shigo wajen ta tsaresa da kallo, ya yi masifar kyau cikin wasu shegu kuma tsadaddun gym wears, shi kuma sam bai kalli in da take ba ya fara aikinsa.

After some minutes Ronnie ya ce mata ta zo su fara faɗar takobi da ya fara koya mata last week, cike da murna ta fara tsalle tare da tasowa ta nufesa. Wani keɓanɓɓen waje suka shiga can ɗan gefe da gym ɗin, wajen tamkar duniyar mafarki yake, ga ruwa yana zuba ta sama kaɗan kaɗan kamar shower haka. Dai'dai tsakiyar da ruwan yake zuwa ta zo ta tsaya yana jiƙata, shi kuma zaro takobi marasa tsawo da nauyi sosai guda biyu ya yi, ya miƙa mata guda ɗaya ya riki ɗaya a hannunsa, sannan ya ciro hulunar faɗa masu kariya ga kan mutum, ya bata ɗaya ya ɗauki ɗaya, gabaɗaya wajen shake yake da kayan yaki kala kala.

Faɗar wuƙa suka fara yi ruwan nan na zubowa a kansu yana cigaba da jiƙasu, yanzu ta ɗan fara iyawa ya fara yi mata manya manya, da a hankali hankali yake yi mata. Ita ma ta zage tana san ta ko yi abubuwan, dan suna burgeta, yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa take san Ronnie, saboda iya faɗarsa ga shi ɗan wrestling, bugu da kari yana da horon mayaƙa, abin ƙayatarwa kuma ɗan wasa ne, kwallon kafa, basket ball, kai dik wasanni yana bugawa har snooker bai bari ba, ga su skater dikka, shiyasa ta ce ya koya mata ita ma ta zama kamarsa.

Cigaba da wasan takobinsu suka yi gwanin birgewa, tana ɗan tsoro tsoro sai da ya ce mata kada ta damu, ta kawo mashi kowani irin hari ne ba zai ji ciwo ba, zai iya tarewa, ita kuma ta ce kada ya zo bai tare ba ya ji ciwo, kai ya girgiza mata alamar kada ta damu, shi fa da yayansa yake wannan training ɗin, dan haka zai iya tarewa, kuma idan har bata kawo hari kowacce iriya ce ai ba zata taɓa iya yaki ba, dan haka dole ta kawo hari. Jin abin da ya ce yasa ta ɗaga takobin hannunta da karfi ta nufesa zata sara mashi a wuya.

Ɗan juyawa gefe ya yi a in da ta wuce ita da takobin nata gabaɗaya ta tafi zata kifa, hannunsa ɗaya da bai rike takobi ba yasa ya tallabo flat tummynta, dama tafiya ta yi zata kifa, sai ya tarota ta gaba gaba. Ajiyar zuciya ta sauke tare da ɗagowa cikin zafa, wai irin ita ma yanzu zata fara yi mashi da zafa tin da ta ga yana tarewa, ashe da gaske zai iya tarewa ba zai ji komai ba!!. KAI SWEETIE WANI LOKACI AKWAI SHIRIRITA, TO MEMA TA IYA DA HAR TAKE GANIN IDAN TA KAWO MASHI HARI BA ZAI IYA KAREWA BA?! WAI ITA A TINANINTA TA ƊAN IYA WANI ABIN.......😅

Yunkurin sake kai mashi sara ta yi, ina ai sai ya fara wasa da ita tamkar wata ƴar tsana, ya cigaba da bata wahala har sai da ta gaji ta ce. "Lovely bro am tied, ka barni haka, ko sau ɗaya ban yi nasara ba fa". Jefar da takobin ya yi tare da jawota jikinsa yana faɗin. "Ai in dai a kai'na ne ba zaki taɓa yin nasara ba, muje ki yi wanka". Turo baki ta yi. "Soon zan yi nasara". Jinjina kai ya yi. "Zan yi fatan hakan, zan so gani lovely sis ɗita ta yi nasara". Raba jikinta da nasa ta yi tana jefar da takobin kasa kafin su nufi cikin gida. Wanka ta fara yi kafin ta bashi waje ya shiga, shi ma wanka ya yi.

Shiryawa ta yi cikin wani haɗaɗɗen gown fari irin mai breast cuf ɗin nan, so kana iya ganin tudun matasan tula tulanta da suke gwanin birgewa, ta yi masifar kyau matuƙa, ga kayan ya fitar mata da coca cola shape ɗin jikinta sosai, dan irin malesian gown ɗin nan ne, ya bi surar jikinta and rigar bai kai mata har ƙasa ba, da kaɗan ya rufe mata cinyoyinta, ta sanya wani high heel, yadda kuka san wacce zata tafi club party, ta zuba chewing gum masu balai'n kamshi a bakinta tana wani tauna, da alama yau da rashin mutumci take ji. Fitowa ta yi ta nufi sama kololuwa tana gyara headband ɗin kanta, wai hoto zata je ɗauka a saman, ɗazun taga wayar Ronnie a wajen.

Tana haurowa shi kuma yana saukowa sanye da pj's dress a jikinsa, ya yi fitina a cikin kayan. Wuceta ya yi tamkar bai ganta ba, ita ma wucewa ta yi kamar bata gansa ba. Har ta É—an yi nisa sai kuma ta É—an É—aga hannunta sama kamar mai neman wani abin a sama, a hankali ta juyo tare da cewa oh irin ta gane magana take san yin mashi É—in nan. Gently ta ce. "Hi big bro! One minute please!". Ta faÉ—a tana sauke hannunta izuwa saman waist É—inta.

Dakatawa ya yi da tafiyar ba tare da ya juyo ba, alamar dai ya bada one minute da aka tambayar. Cike da yanga ta tako ta nufosa, dik Ronnie ya koya mata wannan iskanci, shi ya yi mata wayo ya ce ta rinƙa yiwa Black Tiger haka zasu yi nasara, bata san wayo ya yi mata dan yasa su rufta da san juna ba, shi a nasa tinanin idan ba soyayya ba akwai matuƙar wahala Black Tiger ya iya canzawa, sannan ba zai taɓa musulunta ba idan ba ya kamu da soyayyar musulma ba, Sweetie ta faɗa mashi babu aure a tsakanin namiji krista da mace musulma, to shi ne yake san Black Tiger ya rufta kogin sonta, idan ya yi zurfi sai ace ba zai mallaketa ba sai ya musulunta, wannan ne shirin Ronnie, amma bai sanar da kowa ba, ko ita Sweetie ya ɓoye mata, shi dai burinsa yayansa ya dawo hanyar tsira, shi ai ya ɗanɗani daɗin musulunci har sha'awa yake yi wa wani, Allahu Akbar, musulunci duniya!! Musulunci ya yi, wanda baya musulunci wlh an barsa a wahalarce, ya kuma bonu ya lallace!! Yanzu dai Ronnie ma ya shirya na shi plant ɗin, zai baza capacitynsa ba tare da saninsu ba. Sai dai shi kuma Ronnie ɗin abin da bai sani ba shi ne, DUNIYAR SHAIƊANU ba zasu taɓa barin Black Tiger ya yi aure ko ya yi soyayya ba sai dai wani ikon Allah, amma wlh babu batun so ko aure a tsarin da suka tsara mashi da sihirinsu tin yana yaro, sai dai mu musulmai mun san suna nasu ne Allah kuma shi ne the best planner, ya gama tsarawa Black Tiger dik wani abin da zai yi a rayuwarsa. A tsarin DUNIYAR SHAIƊANU manyan malamansu ma masu takewa mahaifin Black Tiger baya basu da ikon yin soyayya ko aure, dan sun ce mata rauni ne, su ba zasu taɓa yarda da abin da zai raunata zuƙatansu ba, mahaifin Black Tiger shi ne kaɗai aka amincewa da ya rinƙa tarewa da mace, shi ma ɗin kuma idan ya tare da mace har ta samu ciki ta haihu, to tana haihuwa za'a kashe uwar su ɗauki ɗan, dan a cewarsu uwa mace barinta haɗari ne, dan mata suna da zuciya mai rauni da tausayi sosai, so zata iya koyawa yaron rauni da tausayi. Ga dikkan alamu ita ma mahaifiyar Black Tiger kasheta suka yi. (Ni kam ma anya ba gawarta bane suka yi mutun mutuminta a cikin fadarsu na in da na ce maku sun cakawa mace wani dogon karfe tin dafa bakinta har ya fito ta gabanta? Kun tina wajen? Da alama tin da aka yi gunkinta ita ce matar shugaban nasu wato uban Black Tiger kenan)

Bala'i can, akwai cakwakiyar na gasken gaske. Amma my people's ya kuke gani idan Allah yasa Black Tiger ya musulunta, kuma yasan daÉ—in uwa ya fara neman uwarsa? Me zai faru?.

Uhm gaskiya musuluntar Black Tiger yana da matuƙar wahala, saboda ko da ya so su ba zasu kyalesa ba, dan ma dai yana cikin killacewar da babansa ya yi mashi ne, amma dik ranar da ya fito shikenan ya koma cikinsu, yanzu haka sai shirin yadda zasu samu su ɗaukesa suke yi, akwai kalubale mai girman gaske a gaban Ronnie da Sweetie, amma da yake Sweetie ba haka ta zauna ba, tana kai kukanta ga Allah tana faɗa mashi sunan Black Tiger a kowacce Sallah nata idan ta yi, da izinin Allah kuma Allah ba zai basu kunya ba!!.

Kai my people's kun ji Ronnie ko? Zai jefi tsuntsu biyu da dutse É—aya, wai ya yi wa Black Tiger and Sweetie wayo su kamu da san juna! shi ma fa É—an duniya ne wasa wasa!!.

Yana tsaye ta iso in da yake, zagowa ta yi ta gabansa ta tsaya!. "Shi ne zaka ganni kamar baka ganni ba ka wuce ko?". Ta jefa mashi tambayar kamar zata saka mashi kuka. Shiru bai tankata ba, sai ma da ya É—an kara É—aure angry face É—insa. "Kasan me? Kome ka yi kyau yake maka, da ka É—aure fuskarma ka kara kyau ne".......... KALAMAN RONNIE TAKE YI MASHI, DIK SHI YA KOYA MATA!!

Idanunsa a kan kirjinta bai ce ko uppan ba, kunga yanayin rigar tata, so yana iya kallan tudun tula tulanta. Yatsun hannunta ta kyasta mashi a saman face É—insa, nisawa ya É—an yi tare da cewa.

"Ke wai bakya jin tsoro ne a rayuwarki?". Zazzakar muryarsa ya daki dodan kunnuwanta.
ÆŠan siririn murmushi ta saki wanda har sai da fararen hakwaranta suka bayyana.
"Menene kuma tsoro?". Ta yi maganar tare da gyara rigar jikinta da kyau. Sai ka ce dole aka sakata ta sanya rigar, ta biyewa Ronnie zai yi mata wayo bata sani ba, wato fa dik iliminka idan mutum ya rigaka zuwa duniya to fa wani abin sai ka sarara mashi! Yanzu dai ya nuna mata fifikon shekaru!.
Chapter 217 · 0% Book details