Sashe 19
Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiru bai sake yin magana ba, dan shi kaÉ—ai yasan kalar raÉ—aÉ—in dake a cikin ransa.
==========================💘
Sosai King ya yi mamakin jin busoshin yaki da ake ta famar busawa a cikin kingdom É—in, sai dai bai tashi hankalinsa ba, saboda shi É—in dakakken namiji ne wanda babu tsoro ko miskala zarratin a cikin jininsa.
Kai tsaye fada ya nufa domin yasan me yake gudana ake ta buga mashi bososhin yaki har haka.
A nan ya isko commander Zafar da sauran wakilan fada gabaɗaya, cikin takun jarumta ya ƙarisa saman kujerar mulkinsa, tin da ya shigo kuma warriors guda biyu suka take mashi baya har izuwa wajen kujerar tasa.
Miƙewa tsaye daga saman kujerunsu su commander Zafar suka yi domin bashi girma, har sai da ya zauna saman tasa kujerar sannan suma suka zauna.
Dik sun kasa kunne suna jiran umarninsa da abin da zai faÉ—a. Shi ma idanu ya bisu da shi har na tsawon good 5 mins, kun san halinsa akwai jin kai da izzar sarauta, su kuma suna tsoron fara yin magana hukunci ya hau kansu a kan bai basu iznin ba.
Sai da ya cika ya hantse sannan ya ɗan yi gyaran murya cikin nutsuwa, cike da izza ya fara ƙoƙarin buɗe bakinsa domin ya yi magana.
Wani bujumin warriors ne ya shigo cikin fadan bisa umarnin salama, sanye yake cikin kayansa na mayaka, dik da cikin hular kayan yaki yake zaka iya fahimtar face É—insa babu alama sassauci ko annuri.
Shigowarsa ya dakatar da King daga maganar da yake da niyar yi, suka zubawa wanna warriors É—in idanu.
Takowa ya yi cike da jarumta har izuwa tsakiyar fada, sannan ya É—an risinar da kai wanda kun san wanna dole ce a gidan sarauta, girmamawa ce ga sarki wanda ya rataya a wuyoyinsu dole!.
Cike da girmamawa ya ce. "Ranka ya daÉ—e ina neman izinin yin magana".
Muryarsa akwai kaifi a cikinta, maganarsa akwai zarra a cikinta, yanayinsa akwai tsantsar jarumtaka matuƙa, tsayayyen namiji sosai, ga tsawo da cikar halitta matuƙa. Cikin kwararriyar larabcinsa ya yi maganar.
King ya É—auki almost 3 mins kafin ya É—an motsa lips É—insa, cike da izza ya bashi izinin yin magana.
Ba tare da ɓata lokaci ba wannan warriors ɗin ya kyankyasa mashi cewa akwai baki a wajen babban gate na Kingdom ɗin wanda suke da buƙatar a basu izinin shigowa dan su yi magana da shi.
Nan ma sai da King ya ɗauki ƴan mintoci kafin ya buƙaci sanin wasu irin baki ne?.
Kamar ba mutun ne yane magana ba wanna warriors É—in ya amsa da. "Ga dikkan alamu wani sarki ne da tawagarsa, bamu da masaniyar daga ina suke, amma ga dikkan alamu a kan hanya suke".
"Sune silar buga waÉ—an nan busoshin yakin?". King ya jefa mashi tambaya cikin nutsuwarsa.
Cikin dakiya ya amsa da. "Sune ranka ya daÉ—e".
Kallan commander Zafar King ya yi kafin ya dawo da kallonsa a kan sarkin fada da kuma sarkin gida da suke binsa da kallo.
"Commander ina san sanin su wanene waɗan nan cikin ƙankanin lokaci". Ya kai karshen maganar tare da ɗagawa wanna warriors ɗin hannu alamar shi kuma zai iya tafiya ba tare da King ɗin ya sake waiwayarsa ba.
Cikin zafa ya juya yana taku manyan maza ya nufi waje.
Miƙewa tsaye commander Zafar ya yi tare da ɗan risinar da kai alamar ya karɓi umarni, sannan ya nufi waje, sarkin gida ne ya take mashi baya da kara karfafa ida nufin King.
=========HOORAIN=========💘
Zaune suke cikin wannan small garden in da Auta ta kamasu suna hiranta ranar da daddare, shi da Ansar da Anwar, hannunsa na riƙe da wayar Auta while tasa wayar tana a cikin aljihunsa, ya kurawa wayar kallo babu ko kyaftawa, Ansar da Anwar suna ta hira a kan bikin da ake gudanarwa, ba'a taɓa biki a cikin gidan ba bayan na uncle Abbas da ya zamana shi ne na karshe tsawon shekaru, daga King har uncle Abbas babu wanda ya taɓa aurar da ɗa or ƴa sai yau, shiyasa murnar ta zarce tinanin mai tinani.
Hotonta ya zubawa idanu yana ta kallo, tana tsaye kusa da wasu flowers dake cikin lambun daddynsu, hannunta ɗauke da Felix ɗinta tana shafe lallausan gashin jikinsa, murmushin dake kan fuskarta ya yi matuƙar kara tsatso tsantsar kyan da Allah ya zuba mata, dimples ɗinta dikka sun lotsa, yarinya mai kyau da haiba game da kamala, ga farinjini da sace zuƙatan mutane da murmushi ɗaya kawai!. Tana sanye da alkyabbarta har kasa launin golden and white.
Ya luluƙa duniyar tinanin da shi kaɗai ya barwa kansa sanin me yake tinawa, dik da ba'a iya ganin face ɗinsa alamu sun nuna yana cikin kunci da bakinciki game da damuwa, kwata kwata baya tare da su Anwar.
Nisawa ya yi a lokacin da ya ji saukar hannun Ansar a saman shoulder É—insa.
"Mekake tunani ne angon gimbiya?". Cewar Ansar.
Ɗan girgiza kansa kawai ya yi alamar babu komai ba tare da ya yi yunƙurin yin magana ba.
Anwar ne ya ce. "Our Hero ka kwantar da hankalinka, In Sha Allah ba za'a hanaka gimbiya ba, da izinin Allah ita É—in rabonka ce".
Ansar ne ya amsa da. "Gaskiya ya cika sanyawa kansa pressure dayawa, gimbiya fa ita ta nuna tana sanka, kaga kuwa ina da tabbacin In Sha Allah babu wanda zai yi maka shamaki a tsakaninku, ko King sai ya sarara a wannan al'amari".
Shi dai ko uppan bai da niyar cewa, hasali ma kansa a ƙasa bai da niyar ɗagowa bare asa ran zai yi magana.
"Kai ma dai Ansar ka faÉ—a, dik ya bi ya takura kansa kamar...........".
ÆŠaga mashi hannu Ansar ya yi alamar ya yi shiru, dan ya lura da gaske Hoorain yake a cikin damuwa ba kamar yadda suka saba ganinsa a É—an siririn damuwa a kan Zunaira ba, yau abin na daban ne, gabaÉ—aya yanayinsa ya canza, sam baya cikin sukuninsa, yana nan a wani birkice haka.
Ni kuwa nace rai wasa ne? Ka É—auki ran makiyinka ma ya ka kare da faÉ—uwar gaba da fargaba bare kuma ka É—auki ran wadda ta fi kaunarka sama da kowa a duniya?! Ai dole nema ka birkice, bama kaga komai ba tukun nan, sai gaba idan abin ya yi tsamari, soyayya ai ba karya bace, aya sukutum Allah ya saukar saboda soyayya,
A cikin Al-Qur’ani mai girma, Allah ya yi magana a kan soyayya a wurare da dama. Daya daga cikin shahararrun wurare da Allah ya yi magana a kan soyayya shi ne a cikin Suratul Rum, aya ta 21
Wannan aya tana nuna cewa soyayya da tausayi suna daga cikin ni’imomin Allah, kuma an sanya su domin mutane su more zaman lafiya da juna a rayuwar aure, so kunga kuwa soyayya ba karya bace ba kuma abin wasa bace, mukaddari ne daga Allah.
"Hoorain lafiya kake kuwa? Meyake damunka?". Ansar ne ya jefa mashi wanna tambaya.
Sun shiga damuwa matuƙa cikin kankanin lokaci na ganinsa a cikin mawuyacin hali.
Bai amsasu ba, sai ma kara risinar da kansa kasa da ya yi haÉ—e da kashe hasken screen É—in wayar tata yana jan dogon numfashi.
Anwar ne da ƙaguwa da san jin me yake damun abokin nasu ya cika mashi ciki ya sake jefa mashi tambayar menene yake damunsa a karo na biyu.
Ɗan siririn tsaki ya ja tare da miƙewa cikin zafa ya nufi barin wajen, dan kwata kwata baya san jin magana a kusa da shi, dik wanda zai yi mashi magana muryar Zunaira yake ji a tattare da shi, koma wannene, hakan ba karamun ɗaga mashi hankali yake kara yi ba.
Da ido suka bishi har ya kurewa ganinsu, a tare suka dawo da kallonsu a kan juna suna mamakin birkicewar da ya yi har haka, basu taɓa ganinsa cikin irin wannan yanayi ba!.
=========================💘
Cikin ƙanƙanin lokaci commander Zafar ya dawowa King da labarin sarkin Daular Qahtan wato Qahtaniyawa ne ya zo, kunsan manya manyan labarawa sun kasu kabila kashi uku ne, nasan dayawa baku taɓa sanin larabawa mabanbanta bane ko? To gaskiya mabanbanta ne, amma manyan kabilunsu sun kasu kashi uku ne, babbar kabila mafi ɗaukaka a duniya cikin larabawa sune ƙuraishawan Modarawa, kabilun modarawa daga cikin fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S.A.W) ya fito, shiyasa ta kasance ma ɗaukakiyar kabila, daga ƙuraishawan Modarawa sai kuma Qahtan wato Qahtaniyawa, su ne na biyu, sai kuma larabawan kangi, su ne kabilun da suka fi kowanne shahara da ɗaukaka a cikin larabawa.
Sosai King Zuhair ya fusata jin cewa sarkin Daular Qahtaniyawa ne ya ziyarcesu, cikin ɓacin rai haɗe da kakkausan murya ya umarci commander Zafar da a je ya yakesu yanzun nan ba tare da ɗaga kafa ba!.
To me dalili?.
Wanna furuci tasa ta yi dai'dai da shigowar aunty miemie cikin fada, ta dan tsorata jin mahaifin nata yana magana da kakkausar murya haka, dan haka sai ta zama mai risinar da kai game da sanyaya kalamanta da kuma tausasasu a wajen yi mashi magana.
Cikin girmamawa ta tambayesa me yake faruwa a dai'dai lokacin da take zaka saman kujerar kusa da shi!.
Bai so sanar da ita abin da yake faruwa ba saboda sanin halinta da ya yi, amma bashi da biyunta a kaf kingdom of power, da ita suke yin shawara, yana kaunarta ya kuma san ba ta kawo shawarar banza, dan haka sai ya sanar da ita ga abin da yake faruwa.
Shiru ta ɗan yi na ƴan mintuna tana nazari, akwaita da hangen nesa, shiyasa irin su King Zuhair masu saurin fusata suna buƙatar irinta a gefensu dan in sun fusata ta dakatar da su daga ɗaukar hukunci cikin fushi, babu wanda ya fi karfin kuskure da kuma ayi mashi gyara!!.