Sashe 4
Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Wani É—aki wannan mugun ya kaini, É—akin babu hanya kuma dik in da ka juya sai kaga kanka, (kewaye yake da mirror kenan) a wannan É—aki ya sakani sai ya turo mun wani bakin maciji mugu, dik ta in da zan gudu sai in ga babu hanya sai dai hoton fuska zan gani, ga macijin shi kuma yasan hanyan sai ya yi ta bina, ina ta ihun sunanka kuma baka zo ba.............".
Tana kai karshen maganar ta fara ruwan hawaye masu ɗumi, wato kenan dama azabtar da ita Black Tiger ya rinƙa yi da ya ɗauketa, ya yi ta razanata, Allah sarki wlh razana tafi zahirin mugunta cutarwa da wahalar da zuciya, wani ma idan yana da karamar zuciya mutuwa zai yi idan aka razanar da shi, Allah gara a maka azaba direct a kan ayi ta razanaka da ababen ban tsoro. Wato Black Tiger ainahin bakin mugu ne da babi mix wlh, yasan sirrin mugunta da azabtarwa.
Hannu Ronnie ya kai ya fara goge mata kwallar dake idanunta ba tare da ya yi magana ba, saboda shi dai yasan Black Tiger baya yafiya, bai taɓa yafewa kowa ba a rayuwarsa, ya kware wajen yi wa mutane azaba da wuta, so sai yake ganin kamar zai zo ya raba shi da ita.
"Ronnie ka yi magana mana". Ta faɗa yanayin voice ɗinta a shagwaɓe sak na PRETTY yau kuma.
Jinjina mata kai ya yi, can kasan makoshinsa ya furta. "Zan yi magana Sweetie, amma ba yanzu ba, for now dai kyaleni ki yi shiru".
"To yunwa nike ji fa". Ta faÉ—a tana É—an kwantar da kanta a wannan faffaÉ—ar kirjin nasa na Æ´an Wrestling É—in.
Da sauri ya É—ago kansa haÉ—e da kallonsa a kanta.
"To hau saman bed É—ina ki zauna bari in kawo maki abincin ko?". Da kyar ya iya furta hakan.
Da okey ta amsa mashi tare da wucewa ta nufi saman luntsumemen bed É—in nasa, har tsoron haurawa taji ya kamata, gani take kamar idan ta hau zata jita a sama.
Idanunsa a kanta, bai fita ba yana jiran ta haura bed É—in sannan ya fice. Da yaga kamar ba zata iya hawa ba sai ya ce. "Ki hau babu abin da zai faru".
Da sauri ta juyo da idanunta a kansa, kai ya jinjina mata alamar tabbatarwa da babu abin da zai faru. Da sauri ta haye ta zauna, sai da ta É—an lumshe idanunta ta sake buÉ—ewa saboda daÉ—i da laushin mattress na bed É—in, ga wani kamshi na musamman mai kwantar da hankali dake tashi a arear wajen.
Juyawa ya yi ya fice daga room ɗin, ita kuma ta fara bin ko'ina da kallo tana mamakin yadda komai yake a shirye tsab gwanin ban sha'awa da ɗaukar hankali, ga fitinannen kamshi mai sanya nutsuwa a zuciya, lallai yanzu ta yarda da zancen Floris da take ce mata Ronnie shi kaɗai ne kanin Black Tiger, kuma ɗan gata ne, a yanzu ta gasgata hakan matuƙa.
Shiru ta zauna tana sakawa da warwarewa a cikin kwakwalwarta har ya dawo cikin room ɗin hannunsa ɗauke da katon glass tray mai shake da kayan abinci tab a ciki, abubuwa kala kala wanda bata taɓa ganin makamantansu ba.
Saman glass center table dake tsakiyar wasu egg chair a can gefe ya ɗaura kayan abincin, a ɗakin Black Tiger swan sofa chairs ne, a ɗakin Ronnie kuwa egg chairs ne, sunanan kamar design na kwai ne a ka fafake cikinsu aka yi wajen zama, sun yi matuƙar tsaruwa sosai.
"Zo in baki ki ci sai ki yi wanka mu je ki rakani". Ya yi maganar yana kai kallonsa a kanta.
While ita ma shi take ta kallo, sai yanzu ta lura da ya rame kaɗan ya kuma kara hasken fata, kamar wanda ya jera kwanaki yana zazzaɓin dare.
"Ina Floris?".
Ta jefa mashi tambayar tana saukowa daga saman bed É—in.
Sai a lokacin ya tuna yau bai haɗu da ita ba, ya je school ya rubuta last exams ɗinsa ya dawo, yana dawowa kuma wajen yayansa ya wuce domin ya gaya mashi ina Sweetie take, a kan haka suka samu matsala ya fita ɗakin a fusace, zaman da ya yi a cikin cineman part ɗin yasa ya samu sanyi a zuciyarsa da har yasa ya miƙe ya dawo wajen Black Tiger domin ya bashi hakuri sai ya sameta a ciki.
"Ya ka yi shiru baka bani amsa ba?".
Ta yi tambayar ne a kusa da shi, bai ga lokacin da ta sauka bed É—in ba, saboda ya afaka duniyar tunani.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "I don't know where's she, amma nasan ba zai wuce she's in her room or Delisha room ba".
Yana kai karshen maganar ya miƙo mata hannunsa a kan ta kama.
Ba musu ta saka Æ´an hannayenta saman tafukansa, har ga Allah tana jin daÉ—in kasancewa a tare da shi.
Kamata ya yi ya zaunar da ita saman lallausan duma dake shinfiÉ—e a wajen, sannan ya sauko mata da trayn haÉ—e da tambayarta me zata ci.
Zubawa abincin idanu ta yi tana kallonsu, bata ma san menene bane bare har ta iya zaɓa, nama kawai ta sani wannan ma dan wanda yake taimaka masu a forest yana kawo masu nama sosai, so tun kafin ta makance tasan ya kamannin namar yake.
"Ko dai in zaɓa maki ne?".
Ya yi magana idanunsa a kanta.
ÆŠago kai ta yi suka kalli juna. "Ni fa Ronnie ban san waÉ—an nan abubuwan ba, amma dai ka bani naman ya fi tun da shi nasani".
Tun da ta fara magana ya kafe ɗan bakinta da idanu yana jin wani irin shaukin yadda take motsa laɓɓanta wajen furta word, har ji ya yi baya son ta dakata da yin magana.
"Namar jimmina ce da ta ɗawisu, sannan akwai ta ɓauna, wanne zaki ci".
Yadda ya yi maganar sai ya burgeku, saboda idanunsa a kan lips É—inta ya yi, kuma ya yi maganar kamar wanda bakinsa yake ciwo.
"Dik abin da ka lissafan nan ban sansu ba, ni dai nama kawai na sani".
Hannu ya kai saman tray É—in ya ciro mata wani haÉ—aÉ—É—e tsadadden plate mai shake da namar É—awisu wanda ya ji gashi mai kyau, sai tashin daddaÉ—ar kamshi yake yi ya ji kayan haÉ—i.
"Kin ki ki faÉ—a mun sunanki na ainahi ko Sweetie?"
Yana magana yana É—auko kananan wukake haÉ—e da fork domin ya taimaka mata wajen yanka namar ta samu ta ci.
ÆŠan siririn murmushi ta saki har sai da dimples É—inta suka lotsa kafin ta ce. "Sunana na ainahi Sweetie".
"Ba gaskiya bane! Sweetie ba suna bane".
Shiru ta É—an yi, wani zuciya yana ce mata ta faÉ—a mashi gaskiya, ta yarda da shi, shi É—in ba mugu bane, wani zuciya kuma yana gaya mata kada ta yarda da shi, dan mom É—insu ta gargaÉ—esu a kan kada su yarda da kowa a duniya idan ba Kamran ba!.
"Don't restrict yourself, in baki son gaya mun ba sai kin sha wahalar tuna abin faɗa mun dan in ji daɗi ba, don't worry, a dik yadda kike zan ji daɗin kasancewa dake, so forget about the name, yanzu karɓi abinci ki ci".
Ya yi maganar ne bayan ya saita mata fork mai É—auke da gasashen namar É—awisu a saitin É—an bakinta.
Sosai ta ji wani irin a jikinta na jin furucinsa, jikinta ya yi sanyi, bai kamata ace ya nemi sanin wani abin dangane da ita ta ɓoye mashi ba, amma ya zata yi to? Dole ta bi umarnin mom ɗinsu.
BuÉ—e É—an bakin nata ta yi ya saka mata namar, suna aikin ganin juna ido cikin ido.
"Ka yi rashin lafiya ne Ronnie?".
Kai ya girgiza mata alamar a'a, sannan ya É—aura da cewa. "Me kika gani?"
B komai ta bashi amsa tana ƙoƙarin ɗauko ruwan roba dake cikin tray ɗin. Hannu yasa ya karɓi ruwan tare da ɓalle mata bakinsa, sannan ya zuba mata a tsadadden glass cup da ya zo da shi.
"Yau zaki bini church ko?".
Ya yi magana yana miƙa mata ruwan.
Karɓa ta yi ta kafa a bakinta, kusan rabi ta sha kafin ta cire, tana ƙoƙarin ajiyewa a kasa ya kai hannu ya karɓa, bakinsa ya kai ya shanye ragowar tare da ajiye cup ɗin ya zuba mata idanu tana taunar namar da ya bata bayan ta cire cup daga bakinta.
"Mu bama zuwa church ai".
"Why?". Shiru ta É—an yi kafin ta ce. "Coz I am a Muslim".
"Komai nace maki sai ki ce mun baki sani ba, to ya aka yi kika san church kika kuma san banbancin addininmu?".
Ya jefa mata tambayar yana É—aga mata gera É—aya, har lokacin idanunsu a kan face É—in juna.
"Saboda shi abu ne wanda ya shafi addini, ko ban san church a ido ba na karanta labarinsa a litattafanmu na addini".
ÆŠan zaro idanu kaÉ—an ya yi kafin ya ce. "Okey kenan in na fahimta addininku ya yi magana a kan namu?".
Jinjina mashi kai ta yi haÉ—e da cewa. "Kamar yadda ainahin littafin addininku yake magana a kan musulunci ba".
ÆŠan girgiza kai ya yi. "Ban gane ainahin littafinmu ba? Ko so kike ki ce yanzu ba na ainahi muke amfani da shi ba?!".
Haɗiye namar dake bakinta ta yi kafin ta amsa mashi da. "Kusan hakance, ainahin littafinku ai annabinmu ne ya zo da ita, kuma magana take a akan musulunci da dokokin Allah da dai sauransu, amma yanzu gabaɗaya an canza littafin da rubutun cikinsa, masu son zuciya tun tsawon shekaru da suka gabata sun canza wasu abubuwa, a hankali hankali suka rinƙa zare wasu shafuka masu muhimmanci daga ciki, suna shigo da na san zuciyarsu dan su ɓatar da alumma, haka mom ɗinmu ta ce mana".
Tun da ta fara magana idanunsa yake a saman laɓbanta babu ko kyaftawa, sai dai kunnuwansa suna saurarenta da kyau, ƙwaƙwalwarsa kuma yana jujjuya mashi zantukan nata, lallai ba shakka ta zo da babban al'amari, ya za'ayi ta ce an canza masu littafi? Ƴar karama da ita da wanna zancen, lallai so take ta jawa kanta bala'i, dan kuwa ba zata iya wanna faɗar ba!!.
Sai da ta dasa aya a maganar ne ya sauke ajiyar zuciya tare da ajiye fork na hannunsa, sannan ya É—an gyara zama kaÉ—an.