← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 306

Sashe 99

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

ZARIA
To zance dai kawu dauda baiyi wani dogon mamaki ba da zancen da yayan yar uwar nasa suka zo mashi dashi tunda shina mijine yana hango dacewan hakan.
Saidai shakuwan daya kawo shine anya kuwa Jafar yayi tunane kafin ya yanke hunkuncin hakan da zuciyarsa aure fa ba abin wasa bane.
Tabbas nayi tunane kawu ko banyi tunanen yin hakan akan yarinyar nan ba kukanku masu hango hakan a garenine.
Duba ga irin kyautatawan da yarinyar nan ta tsaya tayi a kaina lokacin da nake bukatan kulawan matana a gareni ba tare data nuna kyama ko gajiyarta ba kawu ?
Tabbas hakane Jafar nasan wanan kwarai kuwa to amma baka duban zargin matanka akan kana yawan kula yarinyar nan zai zama gaskiya idan hakan ya tabbata.
Kawu nafi tsoron Allah da mutum Allah ne ya halasta min hakan ba wani abin kaucewa addini zanyi ba a yanzu abune na raya sunnan ma,aikin Allah nake kokarin gudanarwa.
Jafar na dai fahinci daka riga daka yanke hukuncin hakan a zuciyar ka tun kan kazo nan din nima kuma ba zan hanaka hakan ba duba da abin da ke hasashe akai.
Amma kai Habu kana ganin ba matsala yun hakan game da naka auren matarka zata bada goyon bayan yar uwarta ta shigo gidan da take aure da sunan auren ahali daya kuma ?
Sai lokacin Habu dake zaune yana kallon ikon Allah yadda dan uwan nasa yake abu kamar ba kai sake ba ya soma gyaran murya da fadin.
Kawu ni ina ganin tunda Allah bai hana abin nan ba kawai ku kyaleshi yayi abinsa har in yarinyar zata amin ai kamar ba matsala dai.
Kawu din yace ke nan akwai matsala daga bangaren yarinyar ke nan kana dai nufin bada sanin taba yake shirin hakan kome ?.
Eh to gaskiya ta sani amma kasan halin mata dubaiyan halaka wanan ne suke duba a yanzu yasa sam bata amince ba duba ga yadda ake da matansa.
Ita me dakinka fa tasan da zancen kawu ya tambaya da sauri Habu din ya girgiza kansa yana fadin bata sani ba gaskiya ban ma son ta sani ai yanzu gudun kada mu samu matsala.
Don gaskiya idan har tasan da hakan yana da wuya ta yarda da wanan abin hakan yasa nake son mu rigata zuwa can garinsu muga shi hardo don yasan ta hanyar da zai bullo mata kafin ta ruguza abin nasan halin maria da wuya ta amince da hakan gaskiya.
Hakan baida matsala tunda kana ganin hakan zaifi sauki yanzu yaushe kuke son ayi tafiyan sai ita nahaifiyar ku kun sanar dasu zancen.
Kawu ni banson wanan zancen ya fita a yanzu sai idan Allah ya tabbatar dashi duk maiji ma yaji amma yanzu fitar da zancen yana iya kawo matsala a gidan mu.
Kaga ga ita matar hakan ba zai mata dadi ba haka kuma ana iya samun matsala a bangaren mama ta kawo cikas a cikin zancen donshi don Allah kawu a bari sai munje can din idan mun dawo idan zaka fadawa mama din sai a fada mata abinda ke nan.
To shike nan tunda kaga haka yafi Allah ya tabbatar muna da alheri shi lamarin aure da haihuwa haka mutuwa ba a son baki yai masa yawa.
Yanzu yaushe zamu tafi kallon Jafar din Habu yayi sai kuma ya koma yace da kawu din ko gobe in Allah ya kaimu ai muna iya zuwa tunda kowan mu yana da tsabgogi a gabansa da zaiyi zuwa jibi.
To shike nan Allah ya kaimu karfe nawa zamu fito ke nan da zaran an sallame sallah in sha Allahu zamuzo mu daukeka mu tafi da hakan suka bar gidan kawu din da wanan zancen.
Nikan nayi jira banji kira ba karshe ma fita tayi zuwa wajen tsabgoginta ta barni gida da yara da yake weekend ne ranan.
Don haka banji komai a gareta ba barxcin mu mukayi sosai saida Yanda ta kira wayana na falka muka gaisa take tambayana anty salma nace ta fita unguwa.
Muka danyi hira take fadin tana son zuwa gidan maman mu kaduna, saidai bata son zuwa a yini kwana take son tayi idan taje ta dan huta.
Kai ni gaskiya ba zan iya zuwa in kwana biyu wanan gida ba ko yaushe fa mijinta yana gida bai fita ko ina shi ni gaskiya saboda shine banson zuwa din.
Kaji da wani zance kuma ?
Ina kike son ya dinga zuwa dama banda abinki ai hakan ma mutuncine bai fita ba balle a ce yana dattijo yana kuma yawo a gari bai kama mutuncin kansa ba.
Nan dai muka kauda zancen take fada min ai yaya J ya dawo shekaran jiya yanzu haka yana gari sunyi tafiya ma a ranan da yaya habu nace Allah ya dawo dasu lafiya.
Take fadin yan iskan ai ance har yanzu fushi yakeyi dasu salima ke fada min dazun data shigo nace wai ita anty salima bata koma bane har yanzu ?
Ai tayi relocation ta dawo garin nan da services din nata wai shi yaya jafar din ya hanata komawa kasan iyamuran tace.
A raina nace tabdi nikan ai ba mai kawo min wanan idan na tafi na tafi ke nan ma saina gama indawo gida baki daya don ba zan yarda da irin haka ba.
Iya fa na tambaya ta kwashe da dariya take fadin iya na nan shekaran jiya mun jima tare ai don na shiga wajenta gaida ita da kafa.
Take min kwarmaton matan yaya din tace tana ganin yana gab da kara aure nace Allah yasa yan iska ya auro masu wace zata zama masu karfen kafa a gidan.
Ke nifa Saiba nan takai min ko ina na rasa mena tare mata a gidan nan har Abba fa ta hada cikin rigimarmu donni har yanzu batayi min magana nima banyi mata.
Sai gashi fada ya kaule tsakaninta da salima wai akan Abba don ya dauki tedy din yar ta da suka shiga part din tace ya aje aiba ubansa ya saya ba .
Ita dai ta sani zata samu daidai da ita koba namiji ba aiya fita sanin kan sheri tana nan ta kasa zaman lafiya da kowa a gida sai masifan tsiya.
Mun dan jima kafin muyi sallama duk tambayan da take min akan yaushe zan dawo ban fada ba don bazan iya cewa ba zan dawo ba ai saidai taji a bakin anty Salma.
Su hudu sukai tafiyan zuwa Adamawan mu na cameroon wajen hardo wanda tun safe suka tashi sai da yamma suka isa ruggan hardo.
Duk da garine harda wutan Nepa akwai dan kauyen namu taro na sosai akai masu tare da mutuntasu sai bayan sun hutane don a ranan zasu dawo.
Kawu ya gabatarwa Hardon abinda ya kawosu watau neman auren diyansu da maria matar Habu take riko wanda kuma shi yayan habu din ne yake neman auren.
Daga inda Hardon yake zaune sai faman girgiza kai da yakeyi yana fadin Allahu akbar tokai kawun yara a kwashe duka a baku gida daya.
Muma nan ai muna da bukata hadin irin bawai muyi abin rashin hankali mu dauki yara har biyu ciki daya mu mikawa daki daya ba kuma ?
Hardo ai Allah bai hana ba kawu ya fada hardon yace na sani ai donshine bani da ja dan sunnah ce babba hakan garemu musulmai.
Maganan manya rabi da rabi hirace har da hiran jikin yaya da yai fama dashi suka tabo cikin zancen nasu hardon ke fadin Allahu akbar.
Kawu dai yana ta masa hira a cikin hikima yana kara cusawa hardo zancen a zuciya hardon yace to ai baku fada muna ba da munyi namu na nan mugwada a gani ko za a dace.
Kuna zube diya haka cikin duniya ba tare da kun tsumasu ba tayaya mutum na wanan irin shiga mutanen za a sakeshi kara zube yayi alkawarin zai basa sayyun itatuwansa yaje yacigaba da gwadawa har habu da kowa nasa zasu iya amfani dashi.
Yasa murya ya kira shatu tazo yace ta debo masa wasu magani a cikin yaren mu na fulani ta juya taje bata jima ba sai gata dasu ta dawo.
Ta mika mashi ko wani saida ya tsakura ya dandana yake masu bayani don su gane tare da aikin maganin .

ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,

3️⃣7️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Chapter 99 · 0% Book details