Sashe 81
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daga kwancen da yake yake tunanen halin rayuwa yau shine a haka ake fama dashi mutumin da baisan dadin zama a waje daya ba ko yace yasan dadin hutu shiko a yaushe cikin ujula yake haka ya taso ya kuma saba da wanan rayuwa hakan yabi jikinshi sosai kuma don bai iya zama ba tare da yana wani abin da zai taimakawa rayuwansu ba a gidan. Yau sai gashi ubangiji yana ikonsa a kansa hutun dole na wahala ya sameshi irin hutun da bawa bai kauna a rayuwanshi sai in dole ya kama irin haka din. Yaushine matanshi suka hada mashi kai suke nuna mashi kyama da yake gani a idanuwansu karara tun suna boyewa har ya fahinci hakan da gaske. Gashi har Asmau don wauta irin nata har yarshi ta cikinshi take hana zuwa gareshi don kada cutan jikinshi ya shafesu tunda ance dasu ana kamuwa da wanan cutan . Don haka su kiyayeshi kada su kama dashi suma bai taba zato ko tsamanin ko kowa ya gajushi a duniya su zasu iya gudun shi ba haka yadda sukeyi. Hawaye masu zafine suka zubo a idanuwanshi duk yadda ake kai zuciya nesa yana kai akan matan nasa da ba haka yaso dasu ba sai gashi shi bai watsa masu kasa a ido ba sune zasu watsa mai akan cutan da Allah ya dora mai na jerabawa imani. Ajiyan zuciya ya sauke yana kara kallon part din nasa da yai shiru alaman ba kowa a lokacin tare dashi mamace da a zaune wajen ita kuma ta fita zuwa wajen iya. Su kuma yaran nan tun safe baiga gilmawan su ba dama sukanyi hakan suje su dan huta mama ko kawu su zauna dashi din tashi yake son yi ya gaza tun dazun so yayi ya dan mike ya kewaya bandaki amma babu kowa a dakin wanda zai taimaka mashi ya tashi daga inda yake kwancen. Fitowana daga part din iya naji gara naje can din in dubashi don yaya Habu nagida kada in takura masu wanan yasa na zabi hakan na nufi can da yaro a hannuna. Falon babu kowa banda niyar shiga dakin amma naga na dan lekashi ko idonsa biyu in gadashi lokacin hakan yasa na yunkura saiga Saare a bayana batayi min magana ba nima banyi ba . Na leka nishinshi naji yana yunkurin tashi zaune itama ta fado dakin da nata sallaman tana mashi sannu taimaka min in tashi ya fada a cikin yar murya. Ba tare daya amsa gaisuwan da take mashi ba sai naga ta dubi inda nake tana fadin meyake fadane banji shi ba nace yace ki taimaka mashi ya tashi. Bari dai in kira mama ta fada tana juyawa da sauri har tana bangazana a lokacin yaron na aje a gefe na karasa na kama hannunsa da sai ranan na taba kamashi irin haka. Ina mashi sannu ya mike zaune yana nishi Allahu akbar wai yaya J ne Allah ya mayar haka cikin dan lokaci fitsari nake son zuwa don Allah ya kara fada. Zaka tashine na fada a rude ya kada min kanshi dake duke yana maida numfashi hakan yasa na kokarta na tayar dashi tsaye na kamashi zuwa bandaki yana kokarin zama a toilet na fito daga dakin saiga mama ta shigo da saurinta tana fada. Yaya zaice ki kamashi kice baki iyawa inba shashanci ba mutum kamar jafar yana da lafiya zai tsaya sai an kamashine ? To kedai kina kusa ashe ya samu ya mike ko nace ehh mama na kaishi bandakin kingani ba shiyasa banson mu barshi shi kadai wallahi. Ta karasa kofan tana kiran sunanshi ya amsa daga ciki banji meyace da ita ba dai a lokacin na dauko yaron na fito falo tana zaune tana waya nayi niyar zama a lokacin amma sai na canza shawara zan fita. Ke wallahi ni tsoro naji ina zan iya zanga kamar zai sai gani tayi shiru tana watso min harara a fakaice fita nayi daga falon gaba daya. Don yanzu ban kaunar wani abinda zai hadamu kuma da ita kowa ya tsaya matsayinshi a gidan shiyafi sauki baya da gaisuwa ba abinda ke hadani da ita kuma. Na fita muka hade kuma da abokanshi da suka zo dubanshi mun gaisa zan tafi suke fadin don Allah yi muna sallama munzo duba J ne magaishe shi kice su umar ne da musa . Na juya ina fadin ya kewaya amma bari in fadawa mama idan ya fito na shiga na samu mama a falo take fadin ashe kin fitane Habu ya bada maganin ? Ban shiga wajensu ba mama yanzu can na nufa dai akwai wasu a waje sunzo gaida yaya umar da musa gashi ko ya kewaya nace na fada masu ai yana bandaki. Bari mugani idan ya fito kice ya shigo ta shiga kuma naji tana kwala kiran sunana hakan yasa nabi bayanta ina amsawa. Kinga kayan nan nake son akwashe na manta dazun in shiga dasu ciki nace barin kwashe mama na gyara gadon kafin naji fitowansu tana mashi sannu take fadin ya taka a hankali dai. Magana yakeyi banji ba naga tayi dariya tana fadin yace ki fesa mashi kamshi a dakin kinsanshi sarkin son kamshine. Na dauko kamshin na fesa har zuwa bandakin sai kuma na shiga nayi flushing na wanke wajen nagama na fito yana zaune bakin gado yake gaidani da kai na kawar da kaina gefe ba tare dana amsa ba. Ni har ga Allah bala,in tausayin bawan Allah nake ji mutum mai kawaici da mutunci irinshi shine a haka yau lalai bawa ba a bakin komai yake ba a wajen Allah. Muryan mama ya katseni da take fadin kicewasu umar din su shigo na amsa da to na koma daukan Abbati in fita dashi saidai hannusa yana cikin nasa hakan yasa na isa nayi masu iso suka shigo. Ina gaba suna biye zuwa dakin hakan yasa naji jan tsukin da Saare keyi bandai kulata ba na dauko yaron na fito suna gaisawa don da shiga umar din ya soma fadin ikon Allah Alhamdullahi J kaine a zaune yau ? Masha Allah gaskiya jiki ya soma kyau Allah yasa hakan kaffarane a gareka mamace ta amsa da amin gaskiya mama naji dadin ganinshi a yau din nan ikon Allah mama ta karbe da ikon gaskiya. Na samu ya habu a falo yana cin abinci na sake gaidashi zan shige yake ambatan sunana hakan yasa na juyo gareshi alaman akwai maganan da zaimun ke nan na karasa gabab shi na tsaya. Ki zauna yace dani hakan yasa na samu waje na zauna dan nisa dashi kadan ya dan dauki lokaci kafin ya ture plate din yana aje cokalin ya kalloni yana daukan abin goge baki yace. Rahama tambaya nake son maki kuma banson ki musa ki fada min gaskiya iya abinda kika sani zanj dadin hakan idan baki toge ba. Gabanane ya fadi yace wani magani kike ba J a ina kika samoshi kuma waya baki ki bashi shi ya jero min tambayan a lokaci daya ? Magani ? Na fada a sanyayye ya amsa da eh magani wanda kike bashi nake son jin karin bayani daga bakin ki ? Ke Rahama kece keba yaya J magani as how hakan ya faru Ramaah waya baki magani ki bashi Ramash innalillahi wa inna alaihim rajiun kin kasheni Ramaah ? Kaina dago na dan kalleta da mamaki a daidai lokacin ya habu ke fadin haba mana maria ki bari mu saurareta. Dole tana da dalilin yin hakan wa zai turota wajen mu balle kiyi tunanen zatai poisoning din shi kawai ina son ji daga bakintane kawai yayi maganan a cikin hikima. Jin abinda ya fada yasa hankalina ya dan kwanta ina fadin ni ba kissa zanyi ba taimakonshi nayi don ganin irin wahalan da yakeyi. Ki taimakeshi Ramaah ina kika san wani magani da zaki iya taimakawa dashi Ramaah ? An fada maki haka ake shan magani ba tare da kasan aikinshi ba haba anty maria nifa Dage ya ban makaru lokacin da muka je ruggan mu shine nake bashi yana amfani dashi yadda yace ayi. Ina fadin Dage ne ya ban naga takai zaune rugwaf saman kujera tana dafe kirjinta da hannunta biyu ta kara maimaita sunan da fadin Dage Ramaah ? Baki na turo ina fadin to meye a dakin baffa fa ya debo maganin tunda yasan duk aikin da sukeyi ninace ya debo min shi kuma ya debo. Ramaah baki tsoron baffa ya sani koya sani tsakaninshi da dagene nidai na karba kuma na bashi kudinshi. Kasa magana tayi sai bina da kallo da takeyi baki sake ga kuma alaman tsoro a fuskanta saida mijin nata yai magana ta juyo da kallonta gareshi. Koma dai meye maganin yayi don haka shi za,acigaba da mashi har muga aikin maganin don tun ranan data fara mai amfani dashi ya soma samun sauki a jikinshi. Ban son wanan zancen ya fita ku kama bakinku kawai ku dai san halin gidan nan yanzu dai zaki dauko min maganin in kaiwa mama da sunan nina karbo mashi a daina bashi a boyen da akeyi. Jeki dauko maganin mu gani haka na juya jiki ba kwari zuwa cikin dakina na dauko maganin can kasan jakata inda na boye mai yawan saidana rage na fito da sauran na kawo mashi. Shane da kunu ko da madara ko wani abu dai hakka mai dan ruwa saidai idan ana amfani dashi mutum zai kiyayyi duk wani abu mai yauki kada ya cishi. Na bashi na magarya da dutsen tama da za a nemo ya amsa yana mamaki ya fice daga part din sai lokacin ta samu daman magana. Fada sosai tayi min tare da min kashedin irin wanan babban kuskuren dana tafka din da kada in kara irin wanan wautan idan wani abu ya sameshi fa ta sanadiyana ? Ni dai kasa magana nayi don sai a lokacin tsoro ya kamani don sam tunanen hakan baizo min ba da farko sai yanzu din data fada. Saare aka turo kirana nazo suna zaune har da kawu yaya Habu ke fadin ki duba wanab maganin da kyau kece zaki dinga ba yaya J shi safiya da yamma don Allah a kula akwai wani na wanka da za a kawo shima nayiwa mama bayanin