← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 306

Sashe 83

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,

2️⃣9️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

A cikin yan kwana biyun nan na rage shiga part din yaya dubashi sosai nakan shiga da safe na bashi magani da yamma kuma in koma in bashi dama sau biyune shan maganin haka nice zan tsaya in gyaro dakin har bayi in wanke in hada kayan daya cire na wankesu.
To dana gama nabar part din ke nan ba zan koma ba ina dakina kwace ina karatu ko kuma ina game a wayata don rage damuwa.
Ba komai yasa hakan ba kuma don kaucewa surutun da anty Saare ta farayi a kan mu nida yar uwarsu saiga anty Salima ta samu pass ta dawo.
Ina dakina naji muryanta suna gaisawa da anty na hakan baisa na fito ba saida naji tana fadin ina Ramaah namike na nufo falon a daidai kofa na tsaya na rike labule ina fadin sannu da dawowa anty Salima.
Come up kina jina ashe kika share haka zakiyi min oyoyo daga nisa nayi murmushi na karaso tana dauke da Abbati a hannunta take fadin.
Wai sannuku da fama fa mama ta fada min irin kokarin da kukeyi keda Nafisa Allah ya saka da alherinsa itama iya ance jikin ba dadi nace ai dole tana kallon masoyinta zai chala ai dole ta damu.
Wallahi yaya kan yaji jiki Yanda tace wallahi maria saida naji tsoro dana ganshi wai kuma yaji sauki ke nan yace.
Aiki bari abin akwai tashin hankali wallahi ni naga kokarin su Nafisa da Ramaah da ke iya zuwa ko wani lokaci dasu ake jinyasa din.
Sunyi kokari ba kadan ba maria su yan iskan matanshi ai gara da mama tayi masu haka ta korasu gidajensu tunda jira suke ya mutu wai har sune zasuce suna kyamatar yaya don Allah fa maria ?
In banda aure mukkadarine me yaya ya gani a wajen wa yan nan yan iska abin namijine kawai wallahi dama mama tace kada su dawo gidan nan tunda abin nasu iskancine haka ?
Anty Salima kun gama ke nan nake tambayata saida kalloni tayi dariya tace da saura Ramaah saura wata hudu mu karasa yanzu.
Nayi mata fatan Allah yasa a gama lafiya ta amsa min da amin ta mike dauke da yaron a hannunta don ta hadashi da sweet din da yake kokarin budewa a lokacin.
Ramaah taso muje mana ta fada adaidai kofan fita daga part din data tsaya hakan yasa na yunkura na nufeta.
Wayana da yai kara shiyasa na koma dauka har ta wuce ban samu binta ba wata course mate dina ta kirani take fada min zancen test da za ayi wanda asali ban samu labarin hakan ba mun dan jima muna magana kafin mu kashe wayan.
Salima ta jima da fita don shi ban bita ba don bansan inda ta nufa ba a lokacin dama kuma banda niyar fita lokacin na share muna fira da yar uwata.
Tana fita part din ya J ta nufa da yaron a hannunta suka shiga mama na falin ita da baki suna hira don haka direct dakin yaya din ta nufa ta kara dubashi don ta jima wajenshi dazun kafin ta fito zuwa part din mu.
Zama tayi tana mashi ya jiki ya amsa da sauki yana zaune ya jigina jiki da gado laptop dinshi a saman cinyarsa ya mike kafa yana taba system din.
A ina kika daukoshi yake tambayanta akan yaron take bashi amsa da part dinsu naje na daukoshi aina zata yana da kiuya har yanzune ?
Bai yarda da kowa a gidan banda Ramaah sai uwarshi dasu kadai yake yarda su daukeshi.
Tana ina ita Rahaman yake tambayanta ba tare da ya dago daga abinda yakeyi ba a lokacin.
Tana can ai tare zamuzo sai ta tsaya recieve din call ba zata zo ba ai don yanzu itama kamar gudana takeyi .
Gudunka kuma yaya No ba ina nufin na kyama ba kullum itace ke ban magani safiya da dare ta kuma gyara min dakin nan but saidai kamar akwai abinda wani ya fada mata game da hakan da takeyi.
Haba dai ya J ban tsanmanin akwai wanda zai fada mata wani magana game da kai ta yardda kawai dai kila don taga ka fara samun lafiyane yasa haka ?
Amma Ramaah mutum ce mai kaifi daya tana da gudun zuciya ai kaga duk abinda zai hadata da Saare tana kaucewa don nasu baizo daya ba .
Duk kokarin yarinyar nan a kan mu wallahi saida Saare tasa ta canza mata indai ba yanzu a bayana suka shirya ba ko shiga komai daya shafi saare batayi a gidan nan.
Laptop din ya rufe ya dago yana sauke ajiyan zuciya yace abinda nake zargi ke nan a zuciyana tun dawowan saratu gaba daya yaran suka dauke kafansu da part din nan don haka akwai abinda tayi masu da ba,a sani ba game da shigowan nasu.
Sosai ya sake jiki da salima suna magana wanda ba wanan bane farkon hakan sukan danyi shawara a tsakanisu wani lokaci dama.
Shigowan mama da bakin suke fadin zasu tafi Allah ya bashi lafiya ya kara tsarewa wanan yasa suka daina hiran da sukeyi din a lokacin.
Koda yamma yayi anty Maria ce ta tuna min don ina daki ina duba takarduna hakan yasa na fito zuwa part din iya inda na samu anty Saarece kadai tana girki gaida iya da yanzu ba kasafai take fita ba ko yaushe zaki sameta a falonta zaune don bata dogon tafiya.
Saidai da safe zata kokarta ta shiga wajen jafar din kafin rana ya haska kuma ta fito idan ta zauna sai kuma washegari zata koma fita wani lokaci kuma zaikai sau biyu tana lekashi.
Lafiyane bata dashi yasa akace ta dinga zama a waje daya kada ta dinga yawan fita rana saita dauki hakan ya zamo mata dabi,a yanzu.
Mun dan taba hira na fita don in samesu a can din ban kaiga fita nake jin Saare na fadin ashe iya mama ta hakkura ta janye kudirinta akan matan yaya J jibi zasu dawo ?
Iya tace to ai gara ta janye din su dawo ko yaran nan zasu huta duk da ko sun dawo din aiba wani tsiyar zasu tsinana banda fitina da bakin kishinsu.
Ai gara dai su dawo din duk wasu masu rawan kafa saboda kwadayi da munafunci suna jin dadin sun tafi ai zasu kama kansu yanzu kam.
Keko kikan fara tsiyar ki ke nan na zata maganan kirki kike min ashe da wata manufa kike wanan maganan ?
Da wata manufane mana in bashi ba iya daidaine ace wai don sun tafi su suzake haka suna wanan shishigin akan yaya don Allah ?
Wai fa yarinyar nan Ramaah itace harda gyaran dakin yaya tayi wanan tayi wancan saboda kilibibi irin nasu.
Inma kilibibine dai uwarki ta saka suyi ai don haka itace babban kilibabban ke nan ke bakiyi ba Allah ya kawo masuyi baki a laikum kuma zaki dauko sirfa ki saka a zancen waiko yar nan kina tuna mutuwa kuwa don Allah ?
Yanzu laifine zaman amanan da yaran nan keyi damu a gidan suna iya bakin kokarin su wajen ganin sun kyautata muna amma ke ko yaushe kushesu kikeyi ?
Anya kuwa saratu kinwa kanki tanadin alheri kuwa haka kikaga yar uwarki nayi gidan nan baki da zance sai bakin ciki da hassada da hade haden fada tsakanin matan yan uwaki da duk wanda ya zauna a gidan nan don ya lakaci arziki.
Daga daki da salima take kwance tana jinsu ta fito tana fadin balle ba wanan zancen don yaya yace sai sun fadi wanda ya fada masu yana da wanan cutan a jikinshi a zauna kotu.
To ai kinji irinta banga laifinshi ba wallahi gara yai masu hakan tunda basu da kwabo a idanuwansu banda shirme kalar tasu yau in yana da cutan nan ai sungama kamuwa suma yadda ake fada.
To Iya ni kuma su sukace na fada masu hakan kome iya taja tsuki tana fadin ke arr tir da wanan halin naki tunda sunce a bakin yan gida sukaji wa zai fada masu in bake ba ?
Sai ki shirya don ba zancen dawowansu gidan nan da har kike murnan hakan da zasu dawo ko zasu dawo gidab nan ba yanzu ba kuwa .
Sam bata san Salima tana dakin ba da bata dauko zancen da iya ba don a zatonta Salima na can part din jafar din data barta yasa take wanan hiran da iya din.
Tsuki taja ta koma daki kayanta take gyara dama tagama ta fito daga dakin a dan fahintar ta akwai kamshin gaskiya ga abinda suke zargi don wanan zancen da yar uwarta tayi tabbas da yarinyar nan Rahama takeyi.
Suna falo zaune da baki da suka shigo daga wancan unguwar tasu don haka bayan na gaidasune nake gaida yaya din da jiki ya amsa da Alhamdullahi.
Jikin idan yabi da hakan insha Allahu an take Allah ya mayar da aniya ga maishi wata daga cikin matan ta fada.
Kai tsaye na nufi dakin na shiga na gyara na fito na gyara wasu part din da babu kowa a wajen lokacin matan suka mike har mama zasu tafi ita kuma zatayi masu rakiya.
Bayan fitansu nayi kokarin share tsakiyan falon duk yana zaune muryanshi naji yana fadin meke hanaki zuwa gaidani yanzu ?
Cak na tsaya da sharan na dago ina dan dubanshi yace bakiji me nace ba meke haki zuwa dubana kamar yadda kikeyi a baya ?
Ba komai yaya ina zuwa school ne yanzu din na bashi amsa a saukake don gudun ya fahinci wani abu.
Amma sai naji yace ba gaskiya bane da can baki zuwa school ne kike tsayawa kulani ?
Shiru na danyi don ban san me zance dashi ba again ya sake fadin kin taba ganin likitan da bai duban mara lafiyansa a kai akai ?
Hakan ya bani dan murmushi kadan wanda dana sakeshi a fuskana ba tare dana san da zuwansa ba ,wai nice likitanshi yake nufi.
Sosai abin ya ban dariya Ramaah dama ashe nan kika nufo muryan anty Salimace na dago ina fadin nazo ance Iyatu bata nan yau shine nake dan gyaran wajen.
Dazun fa naga Nafisa na gyaran wajen nan ban kula taba naci gaba da aikina ta zauna suna zancena da dan uwanta dake zaune ya harde kafafuwanshi saman table.
Sai dana gama na fesa kamshi na dan rakube ina fadin yaya a zuba maganin yanzu ko sai anyi magariba ?
No banda zabi ai duk lokacin da kika ban zansha idan yanzu ko sai anjima din duk dayane hakan yasa na juya zuwa inda flask ke ajiye a ciki muke zuba mai kunnu koda zaki buda yana turiri da zafinsa.
Sabon flask mama taba Nafisa ta sayo don hakan suna kallona na dauko maganin na hada na dinga juyawa daga tsayen da nake.
Saarece ta shigo falon fuskanta a daure saida ta kallo inda nake takai zaune tana gaidashi yace ina tashiga tun safe bai ganta ba ?
Dan kame kame ta soma wai ai tazo yana barci sai kuma bata dawo ba lokacin dana kowa kai kunnu na mika mai ya karba yana min godiya bai tsaya jirab komai ba yayi bissimillah ya kafa kai ya soma kwankwada.
Yana sauke cup din mukai mai sannu ya amsa yana gyara zama Saratun ke fadin amma yaya gaskiya kabar shan magani haka barkatai da baka san asalinsa ba .
Wanan abu haka kamar wani,,,,,.
Shima ai lalurane ya jawo hakan haka kawai mutum ba zai dinga turawa cikinsa magani ba ai, salima ke bata amsa.
Ki bari na fada mashi tunda akwai wanda asibiti suka bayar a dinga sha wanan aisai a cutawa mutum wani ciwo na daban kuma yazo ya kama mutum wurin shaye shaye.
Saare ko guba Rahama ta ban zansha a yanzu don kwai taji dadi saboda yadda hankalinta ya tashi akan ciwona lokacin da aka fara kyamatana su din basu gujeni ba.
Suna tare da mama a part din nan suna taimaka mata ko ciki daya muka fito iyakar ke nan ai abinda yaran nan ke min Allah ne kadai zai saka masu da alherinsa amma ba zan iya masu kwatan kwancinsa ba.
Baya na koma na sake shigewa cikin kitchen din nasu don banson su san da naji zancensu don saida ta bari na juya zuwa dauraye cup din ta soma fadin hakan.
Ina jin amsan daya bata din yasa na fahinci ya gane me take nufi.
Daidai ina fitowa naji ta sake fadin Allah sarki su anty saiba sun damu su dawo dakunansu wallahi amma mama taki yarda kome yasa mama takeyi hakan oho ?
Shine ai Saiban ke fadin kodai ana zarginsu da wani abu na dabanne yasa mama cewa su koma gida su jira Allah ya baka lafiya.
Da suna da wayau aida basu tafi ba saidai su turo mutane a bata hakkuri amma sun nuna abinda take zarginsu dayi hakan gaskiyane ke nan a yanzu.
Nidai har na bar part din suna zaune ban kuma koma wajensu ba na fice zuwa part din mu na zauna ina tunanen kalamin ta tana nufin mune zamu cutawa yaya J din ke nan ko ?
Dama abinda yar uwata ke gudu ke nan gashi ko hakan ya fara baiyana a bakin saare din nidai bansan me muka tarewa wanan matar ba na fada a raina.
Da ace tasan cewa nice sanadin samun wanan maganin ga yaya aida abin yafi haka ke nan da yanzu ta zarga min wani sheri da zancen yar uwata ya tabbata ace mudin yan tsafe tsafe da gaske.
To zancen yaya nasan kamar a kunnen matanshi ya fada don sai ta kwashe komai ta fada masu kamar yadda anty Nafisa tace ita ke kwasan sirin tana fada masu wanan wani irin sune takewa matan dan uwan nata hakane wai ?
Chapter 83 · 0% Book details