Sashe 22
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
daiyi wuyan gani koda yake naje gidane kinsan mutum mai iyali sole inayi ina leka gida. Dariya ta kwashe dashi tana fadin kajika sai kace wanda ya aje mata masu mata a gida sune bini bini suke zuwa gida lokaci lokaci ba irin ka yaro karami ba. Dariya zancenta ya bashi yake fadin nine yaro karami nida keda mata biyu a gida zaki kalleni kice min yaro. Dariya sosai ta kwashe dashi tana fadin abinda kakewa kanka fata kenan ka fada ka aje mata biyu kamar yadda ku musulmai kukeyi ? Sam kai baka dace da tara mata ba lover boy kada ka tauye kanka sa yawa mana mace daya is ok for you ku more rayuwanku da lokacin ku. Wani kallo yake mata kafin ta tsaigaita da maganan tana kallonshi itama tace iam tell you gaskiyata ke nan har zuciyana na fadama saboda kai din mai tsadane zanso naga wanan mace mai sa,an da zata aurenka ? Me kika daukenine mrs na fada maki matana biyu wallahi kuma ko wace a yanzu tana da ciki da zata haifa min baby. Kallon serious tayi mai tana fadin kacire wasa abinda naga ya dace dakaine na fada sai yayi murmushi don yasan ba zata yarda da yana da mata ko bama mata ba a lokacin. Can ta dan tsagaita dariyan ta saita kanta ta soma fadin ina ta nemanka naji shawaran daka yake don broda ya kirani yace ina guy din don kaya sun fara yawa yana son a fara plan din turawa arewa din. Shima Jafar din gyara tsayinsa yayi ya soma fadin eh to gaskiya ban tsayar da maganan zanyi ko ba zanyi ba a yanzu saina gana dashi yayan naki na fahinci wasu abubuwa daga bakinsa. Wanan baida matsala don yana Nageria yanzu haka kaga bari na nemesa sai muji time din da zamu samesa don gaskiya mr handsome ina sonka da wanan business din don ba karamin samu zakayi a cikinsa ba yafi wanan buga buga din da kukeyi a yanzu. Tana magana tana dauko wayanta a cikin handbag dinta a lokacin ta soma dialing din number dan uwan nata kira kusan zai katse ya daga yana fadin sorry sister ina meetinga ne a yanzu. Dama broda guy din nan danayi ma zancenshi shine yake son ka bamu time da zai gana dakai yake fada mata zai shigo lagos next tomorrow idan ya shigo by 4 pm zasu iya ganawa dashi a ranan. Suka danyi yaresu inda take kara rokawa mr handsome dinta alfarma a wajen yayan nata tana yabawa har yayan ke fadin tabari din yazo din da alama guy din yasan kansa tunda har ya nemi su fara ganawa dashi. Abinda baiso shine cuta da cin amana idan haka ya faru ba zai dubi alakansu ba zai dauki mataki mai muni akan ko waye. Tace by god grace hakan ba zai faru ba son ta yaba da halinsa sosai sun dade suna business dashi ta fada mai hakan don ya yarda. Kai ta dag ta saukewa Jafar kallo tana fadin munyi sa,a basai muje can ba zai shigo lagos banda gobe kaga zamu sameshi 4 o,clock ku gana dashi don forget with d time ta kara fada suka taka zuwa bakin motarta tashiga ta wuce. Shima motanshi dayazo da ita wajen ya nufa ya shiga ya nufi inda zai tafi tare da tunanen yadda abin nasu zai kaya saboda zuciyarshi ta shiga wasi, wasin don imani da tauhidi dake yawo ajinsa na adduan iyayye. Kamar yadda suka aje time karfe biyu yana fitowa sallah ya kirata karo na farko yana tambayanta ko brother din nata ya samu shigowa lagos din tace zata kira ta tambaya taji. Ba a dauki wani lokaci ba ta turo mai sakon wajen da zasu hadu zuwa wajen yayan nata yaci gaba da harkokinsa na yau da kulum a lokacin. Sai bayan ya fito sallah a masallaci mafi kusa ya shiga mota ya sameta tana jiran sa hakkuri ya bata daya tsaya sallah ne a masallaci tace ba matsala tana gaba motanshi nabin nata a baya har gidan dan uwan nata dake wani unguwar masu kudi anan kusa da ruwa. Kai tsaye ganinta security suka barsu suka shiga gidan don tayi masu bayanin tare suke yaji mamakin girman wanan gidan haka yasashi nasa wanan yayan nata ba karamin mai kudi bane ashe. Sun samu waje sun faka motocinsu wajen suka fito zuwa cikin gidan shidai yana dauke da addu,a a bakinshi don zuwa yanzu sai tsoron zuwa shi kadai ya darsu mashi a zuciya yana tuna addua shine mafita koda yazo da wani din ba zai iya mai abinda Allah zai yi mai ba ya fara jero duk abinda ya sani a bakinsa. Wasu kulka kulkan mutanene ta gani suna gadin gidan bai damu ba saboda addua yasa ya daina jin tsoro a yanzu. Sun samu yana meeting da wasu yan kabilansu kana ganinsu kaga manyan matasan arnakun kasan nan ya fake da waya da wani abokinshi a lokacin. Ya fahinci duk wanda ya fito yaga Meiarbe sai yayi mata kirari da bata girma irin tasu na iyamurai da sukeyi bayan sun fitone akai masu iso zuwa ciki don yayan nata ya hangota daga waje yasan sun iso ke nan. Addu,an da Jafar ya doshi wajen dashi yasa suna shiga yaga mutumin aiba wani babba bane can yanda ya zata don irin matasan daya ganine a waje yanzu. Hannu ya mikawa Jafar din su gaisa baiki ba ya mika masa yaga zalla nagartan jafar daya hango a yaron lokaci guda. Bayan sun gaisa yake tambayanshi daga ina yake ya fada mai kai tsaye daga zaria yake yana zaune nan lagos. Ya dan kara kallon Jafar din dake zaune a cikin ladabi kafin ya soma magana yana fadin quity sure kayi min haka nake son dama matashi mai lokacinsa wanda zai iya bada karfinsa ga aikin mu ba ya zauna ya tura ai masa ba. Saidai kota fadama harkan mai zamu soma a yanzu mutane da dama daga arewanku suna son wanan harkan ban basu daman hakan ba don ina jin tsoron hurda hausawan ku saboda basu da amana. Kai jafar ya dago ya kalleshi yacewa Jafar din gaskiya na fada nagwada aiki da mutanen ku a baya banji dadin hakan bane. Allah sarki malam bahaushe da abaya iyamuri ko bayerabe suke tsoron koyi masa kallon banza balle fada a yanzu zamani yazo da iyamuri zai fito fili ya fadi magana akan bahaushe sune ke fadin basu yarda da bahaushe ba suda muke kyama sosai. Saida wasu marasa zuciyan bahaushe da suka batamu a wajensu sun ari rigan bahaushe sun yafawa kansu suna yaudara suna batawa hausa asali suna da akidarsu ta yaudara a yanzu. Kada ka damu you are lucky tunda autace ta kawo ka nasan idan bata yarda dakai ba zata kawoka har wajena ba zan barka hakan don nasan tunda kace kana son ganina kaima kana da abinda kake son fada a kaina. Zama Jafar din ya gyara ya soma fadin najo duk abinda ka fada saidai ina son jin ainihin yadda kake son sana,an naka ya kasance a arewa idan zan iya zan karba da hannu biyu inma godiya idan kuma naga ba zan iya ba zan fada tun a wajen nan ka neme wani don addini mu bai yadda da wasu tsare,tsare ba a cikin sana,an mutum. Kallon guy din chibuza yayi yaro karami yasan kansa akan addininsa abinda bai taba jin manyasu sun fada ba Allah Allah ma suke ai signing din contract dinsu su farawa mutum yaudara shi gashi yazo masa da nasa tsarin akan addininsa yanzu. Ehh to ba wani abu bane ya soma mai bayani akan yana bukatan gina gidajen mai a arewacin Nageria din shi Jafar duk zai kula da wanan bayan haka akwai motoci da zasu shigo wa yanda zasu dinga sintiri kai mai kuma duk zasu tsayane akarkashin kulawan jafar din da komai illa iyaka shi nasa balancen zasuyi yana turo mai kudi a wajensa eather shekara ko bayan duk wasu watanni haka yadda dai abin ya samu karbuwa a wajensa. Ajiyan zuciya Jafar ya sauke don jin ba wani abinda zai soki addininsa ko rayuwansa nan gaba donshine ya amince suka tsara yadda abin zai kasance tare da musayan secret number da zasu dinga magana a tsakaninsu. Ya gargadi Jafar sosai da bai son yawan magana inda yace koda ba,a aka sunan yadda za a fahinci nasa bane shi wanan ba matsalan shi bane kada dai a samu kuskure a cikin harkan . Budan bakin Jafar yace wanan kada muyi fatan haka mu nemi sa,a a wurin ubangiji ya dafa muna kan lamarin da muka dosa . Iyawan mutum ko kwazon mutum baiyi kamar na Allah ba da komai yake a hannunsa kai chibuza ya daga yana yaba nagartan Jafar a zuciyarsa. Dafa Jafar din yayi yana fadin idan ka rike gaskiya zamuji dadin juna sosai dani dakai don a wanam harkan kadai zamu tsaya ba a sannu zanyima hanyar international business . Sun rabu cikin jin dadi da fatan nasara a tsakaninsu sukai sallama akan in Jafar yagama nazari zai nemesa yaji inda za a fara.