← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 207 OF 306

Sashe 207

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kusan hakan yake faruwa a tsakanin mu tsawon wata daya saidai na kasa fadawa kowa wanan maganan. Wa zan tunkara da wanan zancen nace ga abindake wakana a tsakanina da mijina alhalin yana kwance haka sharkaf dashi bai ko wani dogon motsi balle magana. Har abin yakai ya fara damuna da zaran dare yayi banda katabus dashi ya dinga bina da ido kenan harsai yaji mun hada jiki dashi a sannan zai dinga jero ajiyan zuciya yana saukewa a fili. Dole zan biye mashi da abinda yake so na fannin wasannin aurataiya a tsakanin mu har zuwa lokacin da naga ya samu gamsuwa na jaye jikina daga nasa in koma gefe ina hawaye a cikin kunci. Ganin dai a kwai sauki sosai dake shigansa na gane hakan kuma nadaga cikin karuwan samun kuzarinsa a lokacin don yakanyi barci a daren da duk hakan ya kasance a tsakanin mu sosai. Washe gari nakan kula da fara,a a fuskanshi da walwala idan anyi magana zakiga yana dan murmushi a gefen fuskanshi sai gashi kwatsam naji suna zancen cewa zasu fita dashi kasan wajen. Nafi kowa sani a yanzu ciwon yaya bana asibiti bane ciwone dake da alaka da jinnu ko sihiri da akewa mutum wani lokaci. Ranan babu kowa nake fadin mama niko sai naga da an dakata da wanan fitan da za ayi da yaya a yanzu don yana samun sauki sosai kawai dai kamar baison a gane hakan ne a yanzu. Nayi tunanen hakan Rahama ina kula da kusan hakan a tsakaninku saboda a yanzu kin rage yawan tashin hankalin da kika shiga a baya game da rashin lafiyan nan a yanzu duk babu shi sosai wanan yasa na mayar da hankalina a kanku dole nasan akwai dai ? Dan murmushi na sake a gefen fuska ina kawar da kaina gefe take fadin ai bari almuri zan samu lokaci nayi magana dashi shima sai kuma ta koma tambayan . Yanzu wani cigaba kike gani ga lamarin nasa wanda ke nuna akwai sauki sosai ga laluran nasa don hakan ke nuna alaman lafiya idan ya fara wani abu ? A zuciyana na amsa da abu ko mama tunda ya iya raye dare daga kwance yake iya biyan bukatanshi nada namiji a hakan amma a fili cewa nayi da ita. Yanzu mama yana iya daga hannunsa wani lokaci har yana kokarin yunkurawa ya tashi zaune ko yayi kokarin kiran sunana idan yana son wani abu. Masha Allah koda ya boye hakan ba laifi bane don zamanin nan da muke ciki wanda baka zata ba bakayi tsamani ba shine zai ha,ince ka banga laifinsa ba idan har ya boye hakan gare mu yanzu. Yanzu matsalan shine ni kinga kamar sun ma fara gajiya da nine nan a yanzu yadda dubu da sarakuwarta ke nunawa zamana daku a yanzu yakai masu ko ina don na tare gaba na tare ba a garesu. Matsalan dai tasan tun Alh yana raye irin dokan daya kafa muna a gidan nan da kuma irin hadin kan daya sanya na dole tsakanin mu. Aida dubu nada hankali da bata karbe zancen da duk wani laluran jafar da iyalinsa a hannuna ba din ko shi dan dakinane kamar yadda kikaga Nafisa yar dakinta a yanzu tun Alh yana raye irin dokan daya kafa muna ke nan . Idan ke mace zaki yaye danki zai kira wace zaki ba yayyen dan haka kuma rikonsa zai koma hannunki ke nan har girmansa. Sai bayan rasuwan Alh ne kan mu ya dan rabu tun wajen robon gado da kowa ya nuna nasa halin akan abinda Alh ya barmu dashi. Yanzu da kokarun mijinki yayi dabaran dawo da hadin kai a tsakanin mu donshi haka halinsa yake kamar na mahaifinsa . Shigowan matan su yaya Auwal ya katse muna hiran mu don haka mukan zauna wani lokacin muna hira tsakanin mu saboda shakuwa da ita da yanzu nayi sosai takan ban labari irin na kunne ya girmi kaka a yadda na kula zamane akayi a baya irin zaman mumuke a tsakaninsu. Irin a fili ana son juna ana nuna babu matsala amma ana kishin mumuke irin zaman kakanin mu da iyayyen mu da ba a gane kan gida din nan . Anan falon aka zube da matan su yaya din ana hira lokacin Iya da matar Yazid suka shigo falon sam bata da marmari don bata sakin jiki da kowa sai iya da mama kadai take dan zama dasu bayan hakan ko yaushe tana part dinsu bata shiga mutane. Zakice tana gudu mutane fuskanta kuma sam ba fara,a acikinsa matan gidan suyi gulma sun gaji sun saka ido don sun fahinci itama ba kanwar lasa bace ashe. Bayan sun gaisane da iya suke tambayanta ko itace matar Yazid din iya ta amsa da fadin itace to bai zauna ba balle ya kaita wajen yan uwa a cewan iyan. A nan muka wuni dasu abinda yasasu tafiya yunwa don an jima ba a gama abinciba kamar kullum haka kuma da za a kawo aka zubo dan kadan waina mu dukan mu part din ke nan. Ina jin lokacin da mama takece masu suje gida su nemi abinda zasuci don wanan ma komu ba zai isa ba balle su din kullum haka ake abincin kamar na rowa a kawoshi bai isn mutane saukin abin ma yanzu wani lokaci ita nan takan yo muna dabara daga can gidan ta idan ta tafi shi muke samu muci. Da zasu tafi na yafa mayafi na rakasu har bakin get amma saida suka shiga suka sallami mama dake can part din ance wai tayi bakine bandai san ko suwaye ba. Sun tafi na koma don in gyara part din na samu Asmau da yara sun shigo muka gaisa na gaida ita da aiki take fadin tun safe tana tsaye bata huta ba yasa wai bata leko ba. Dakin na fito na barta da mijin don in suna ciki nakan dawo falo ko dayan dakin in dan kwanta wani lokacin kuma inyi barcin gajiya . Hakan ne ya faru don ban tashi ba sai wajajen karfe biyar saura na tashi nayi sallah na fito na fara gyaran falon har lokacin suna ciki da mijinsu da yaransu na dai shiga mun gaisa dasu din na fito naci gaba da aikina. Nayi mamakin rashin shigowan mama a wunin ranan don tun safe data shigo bata samu dawowa ba wai tana can tare da baki ake fadi ashe ba wasu baki bane ita da yarantane a lokacin. Saida dare iya bata shigo ba naji mama na fadi cikin kashe murya yau akwai abinda dubu da yaran nan suka samu don tun safe suke hayanita tsakaninsu. Jin hakan yasa na dago na dubeta take fadin kinsan mu ba a son mu sani don kamar makiya ake daukan mu duk da iya ta dan kyankyasa min . Wai yaran nan matan Jafar to har dake dai ke nan ake nufi ko sunce Habu da yazid din sun dulmuye dukiyan dan uwan nasu suna ci su barku a haka a kula daku dashi. Ko ita mahaifiyar taku ta kama masune shine habu kin sanshi ya dawo da komai na jafar da yake juyawa yanzu yace ya daina kula da dukiyan a baya ba an taba wanan maganan ba yanzu kuma sun tayar da zancen ke ban kuna nake tambayan ta ? Ke dai bari abune da baka isa yau danice ai wace ta ta fito da zancen nan data san bata da wayau a gidan nan ? Ina batun yarona dake kwance ina naga wani batun dukiya can har in bari karamar yarinya ta dagula min lissafina haka ? Shiru nayi ina tunane wai wanan matsalan haka daga ina yake fitowane wai na kula fa ba damuwa sukayi da bawan Allah nan ba sunfi damuwa da dukiya kawai akansa. Muryan maman tudun ne dake fadin kinsan ita iya ba ruwanta fadin abinta takeyi kai tsaye tace duk munafuncin daga Nusaibace da saratu ya fito. Kamar a mafalki mukaji murya kamar nasa da karfi saidai yanayin kiran daya kwala min din ya sauya da harshensa da muka sani sai gashi a ranan ya ambaci sunana . Dagani har mama da sauri muka karasa zuwa dakin yake fadi cikin badaniya kamar me koyon magana da Allah ya bashi ikon furtawa yace ko akwai kunama a gadon nan ne ? Da farko bamu gane me take fada ba saboda yanayin dan saurin maganansa haka kuma yanzu da harshen nasa yake kamar a karye. Sai can nace ko kunama kake fada ya daga kai da karfi yace a wani irin yanayi eehh wani abu nake jin kamar yana cizona na yunkura in dagashi na kasa hakan yasa mama fita daga dakin da sauri . Ashe taje nemo koda yan uwansa suna gidan sai yazid ta sama ya habu ya fita tun yamma ya tafi gidansa sai gasu tare da yazid din dasu mama da kowa don mama tudu tace dasu Jafar yayi magana yau. Saidai ba a cikin dadin rai ba sabo harshensa da yake kamar a karye wanan yasa duk gaba dayansu fitowa lokacin . Koda suka zo Allah ya taimaka na samu na cirashi daga gadon zuwa kasa suka shigo sai wani irin nishi da yakeyi mai karfi a cikin kugi na wahala. Mun duba gadon ko ina har jikinsa da komai karkashin gadon duk an duba babu komai gashi kuma a cikin wani wahala duk ana tsaye a kansa ana binsa da kallon tausayi. Hankalin duk wani na tare dashi tsakani da Allah ya tashi a lokacin Asmauce ta fara kuka ta juya zuwa falo don yazid dake mata tsawan yaya haka kuma kada ta tara masu jama,a ? Hakan yasa ta koma falo ganin yadda wahalan yai yawa ga wani irin zufa da yakeyi yasa na shiga neman magani a cikin wardrobe din da sauri na juya na fita zuwa kitchen na dora dan ruwan dumi na sauke na fito. Nan falo wajen Asmau na zauna muka fifitashi tare da ita na koma dakin lokacin yana wani irin wulle wulle nace wa yazid din ka kamashi a bashi magani ? Shiya kama min shi ya dago ina kokarin bashi naji muryan saiba na fadin wanan wani irin maganine kuma a daina bashi abu barkatai don Allah haka
Chapter 207 · 0% Book details