Sashe 273
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
tsaye bawai irin na wacce tayi nadama bace gaskiya. Koda ya isa gidan ya samu mama ta hau ta cika don me yayiwa matarshi haka da wanan zancen ta tareshi da fada ga matarshi ta dawo don ya nuna masu iyakarsu yaje gidan wata ya kwana ya barta nan ? Amma dai mama gidan matana na kwana ko da zata dawo wa kuka fadawa dawowanta ga shekaran jiya din ? So tunda banda amfani ga da zata sanar min zata dawo ai gara inje inda akasan darajana ko kai ji nan malam naga yarinyar nan gaba daya ta juyema kai to ka natsu kasan abinda kakeyi yanzu. Rahamace zata juye min kai kuma mama ya tambaya fuskanshi dauke da murmushin mamaki ga maganan mahaifiyar nasa. Inda mama din tace ba dole ince haka ba tunda kai baka san me kakeyi ba ta ina ka taba jin anyi hakan itama inba makira bace ai tana da labarin matarka ta dawo data karbe ka . Ina ruwanta da zancen dawowan Nusaiba mama tunda ba a unguwar nan take ba ina zata sani koma dai ta sani ko bata sani ba dai tunda tasa kayiwa wata wullakanci itama ta saurarinata ai yana tafe. Mama wai meyasa kike saka kanki cikin irin shirmen nan bafa dake ake zancen nan ba banga abinda zaisa kina saka kanki irin wanan maganan ba girman ki na zubewa ? Ooh yanzu don na tsaya gyaran gidanka shine girmana ke zubewa malam to ya tude karshen zubewa ke nan badai ga yar gwal din matarka zai zube ba kawai to aida sauki tunda iya nan zai zube din. Mikewa yayi yana tambaya iya tana can bangaren ne har yanzu salima ya samu ta amsa mai da tana can yau ta tashi bata jin dadin jikinta tun jiya. Subbahanallahi ya fada ya dakata yana tambayan ta meke damun iya din take fadin gudawa tayi sai jikinta ya mutu . Shine baku kaita asibiti ba mama kuka barta a gida haka amma haka baiyi ba wallahi ya fada ya fita da sauri zuwa part din da iyan ke ciki. A kwance ya samu tsohuwar cikin wani hali na ban tausayi da sauri ya kamota zuwa asibiti shida salima da mama din akaje asibitin dole aka kwantar da ita aka saka mata ruwa. Lokacin ya kira yazid a waya ya haushi da fada kan rashin kula tsohuwar da baiyi ba kuma yana gari fada sosai yayi da kanin nasa yana bashi hakkuri. Sai lokacin jikin mama yayi sanyi ta shiga kame kame tana fadin wallahi na dauka irin yadda yakan dan bugeta ta mikene kawai. Mama bidon Allah yayi iya da tsawon rai mai lafiya ba jikin iya a yanzu ba komai zaku bata taci ba ya kamata ace ana duba irin abincin da zataci tunda tana da gatan hakan a yanzu. Ya bugo min waya a gabansu yana fadin in shirya abinci gasu nan asibiti da iya an basu gado hankalina ya daga anyi dace nagama abincin rana ke nan na kwashe na cika kula Aminu yakai masu. Wanan ciwon na iya ya kwantar da fitinan da akaso tayar mashi wanda shima a hake yake dasu ashe kan hakan da dare tare mukaje dashi duba jikin iya din don yazid ya kawo wa yancan da zaizo da matarshi sun duba iya din. Akwai haske tar a lokacin duk da shigana ba wani shiga nayi ba a lokacin amma hakan ya tsonewa mama da iyalinta idanu . Duk dago kai zanyi zan samu dayansu yana satan kallona a cikinsu bamu jima ba ya soma fadin wa zai kwana a nan din nida Dubu zamu kwana Hafsatun kawu ta fada. A,a mama ki koma gida abar mama ta kwana don ko maman tudu taso tazo ta kwana sukace basu son mutane da yawa a nan din. Da dai ka barmu mun kwana mu biyu din tunda ba a san me dare zaiyi ba a hankali na fara takawa don barin dakin cike da mamakin hali irin na mama din . Ke nan tana nufin jinyar mahaifiyarta sai wani ya saka mata hannu a cikinsa bayan tasan ba shiri bane a tsakaninsu ko banza. Ya jima a tsaye kan iya ya dago yana fadin bari nakai yarinyar can gida indawo bai tsaya ba ya fito zuwa wajena ina tsaye na dafa mota ya iso yana fadin muje ko ? Saida muka soma hanya nake tambaya yaushe iya ta soma ciwo duk ta rame haka yace waya sani ko yanzu ai salimace dana shiga take fada min da haka zata halaka a daki ita kadai. Daga asibiti idan an sallamota nan gidan zan kawo maki ita don ta samu kula mai kyau don Allah ace abar tsoho da yunwa ga tsufa ga ciwo sai lokacin da akaga dama za a bata abin karyawa taci ? Ni dai banyi magana ba har muka isa gida duk abinda zan fada idan ba zagin mahaifiyarsa zanyi a gabansa ba me zance don laifin duk natane game da hakan gaskiyaa. Tunda ya dawo bai koma ba kamar yadda yace don har mama ta bugo waya wai in zai dawo yazo masu da ruwan zafi a flask. Yace gaskiya ba zai samu dawo ba don har ya kwanta saboda yana jin rashi dadin jikinsa. Hakan yasa tayi fushi ta fara zage zage tana fadin Jafaru baida ta ido akan wanan yarinyar don in yana gabanta tankar yana gaban Allahnshi ne Haba dai dubu kada kice hakan kawai dai zuciyace take kaunan mai kyautata mata duba ga irin kokarin yarinyar nan gareshi ba tsoro bane hakan kyautatawace kawai a tsakaninsu. Kin dai tsani yarce har baki ganin kirkinta a yanzu amma ai tayi kokarin da ba kowa zai daure yayisa ba kinga ko dole yaso abarshi a yanzu yadda tayi fama din nan a baya kanshi Na kula kema hafsatu a yanzu kamar kin fara shakku da tsoron yar nan koda yake ba laifinki bane koda kinyi hakan don kanki kikewa yaki hakana din. Kwanan iya biyu ta samu lafiya kamar yadda yace yaso ya wuto da ita gidan mu sai iyan tace dashi a bari agama bukin Saratu in muna raye sai tazo ta zauna dani har in haihu shiyasa yayi na,am da hakan ya barta. Sun fara shirin buki gadan gadan har lokacin ana neman abinda ake nema din na wasu abubuwa ga yan uwan duk kowa yaja bakin aljihunsa ya tsuke yana kallo. Shine mai saukin da suke saka ran zai fitar dasu kunya shi kuma din ya nuna yanzu Habu ma ya fishi karfi don dukiyanshi da aka wawashe yana kwance bai gane komai ba. Ga karyan da take sonyi ta burge mutane a wajen bukin nata ba abinda ya kamkama daga wajenta shima angon ta rasa gane kanshi a yanzu datayi magana zaice ba kudi bai son karya a sha,ani. Tana sonshi kamar me don haka saita kyale ta kasa tambayansa komai abu yayi yawa ya taru masu lokaci guda.