← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 276 OF 306

Sashe 276

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

? To wallahi ki fada mata duk ta kuskura takai hannu a kan wanan yarinyar again na barta har abada ke nan a rayuwana tunda ita mutumiyar banzane na fahinci hakan sosai yanzu. Tana magana bai tsaya saurara mata ba yacigaba da fada karshema ya kashe wayanshi yana huci ya ja plate din abinci zuwa gabanshi. Yau da ace ina yawan korafi akan abubuwan da nake gani kansu ashe da ban samu wanan shedan ba daga bakinsa a yanzu ? Ashe yasan nasam komai nunawane banyi a gabanshi sai in nuna komai banji ba akan harkanshi da matanshi koda sun bugo mashi waya a yana gidana ban yarda na taba nuna mashi kishin da nake ji kan hakan ba a fili. Saida yayi cibi kamar biyu zuwa ukku naji muryanshi yana fadin yaushe kika iya motane ke ban sani ba ? Ajiyan zuciya na sauke kafin nace dashi ya jima mana tun ban aureka ba na iya mota lokacin da nake zuwa Abuja hutu anty salma tasa aka koya min driving. Lalai kin kai bafulatanan asali Rahama amma baki taba nuna min kin iya ba har nake zancen a dinga koya maki keda wa yancan kafin Allah ya hore min in sayawa kowa nata ? To idan na nuna meye faninshi yanzu ai gashi daya kama ka sani kasani din ai, kuma don Allah kabar sa kanka a cikin zancen mu da matanka don hakan yana kara min bakin jini a wajen yan uwanka na saya zancen bance mama ba nace yan uwanshi. Rahama kada in magana ta illantaki don ana tsoronta ita din me har waye Nusaiba yar iskan banza kawai dama haka mama ke son gani yasa ta takura min sai in dawo da ita. A zatonsu idan ta dawo zata kwatar masu wani abu dayafi wanda nayi masu a yanzu a wajena kyalesu nayi naga plan din nasu basu san waye Nusaiba ba har suke tunanen hakan a wajenta. Yarinyar da bata son taga duniya naiwa wani alheri koda kuwa ita mamane da kanta har inta sani sai mun samu matsala da ita ta nuna nata iyayyen fa don wauta ? Wai ita suke sa ran tayi masu abinda ban tashi yi akansu ba yanzu kyalesu daga su har ita jira nake ya fito a tsakaninsu ai wanan kan dole inyi mata kashedi a kansa tunda bake kadai bace. Nasan aiba zata iyaki ba tunda sun gwada syn gani yanzu so take tayiwa cikin jikinki rauni a fahintana shiysa take nemam jidali dake. Tayi da wani ai nibama zan koma zuwa wajen bukin ba balle ace ga kuma laifina wanda naje din nan ya isa hakana kuma. Abinda nayi niya bayarwa zanbawa Aminu yakai masu shike nan a zauna lafiya tunda basu son ganina a sha,aninsu. Saboda me ba zaki ba gidantane ko bukin yar uwarta akeyi da zakice ba zaki ba zaki tafi in takai yar iska ta kara tankawa a kanki kuma ? Ai baki san Nusaiba bace tayi hakane kawai ta baki tsoro amma komai bata iyawa na gaya maki ita Asmauce har yanzu bata fahinceta ba. A,a mai bukin tace munzo da yar uwata zamu bata masu sha,aninsu suna bukinsu a cikin dadin rai zuwan mu yasa muna son bata mata buki ? Ita Saratun tace hakana har wani buki bukin da suka sawa kansu karya a kanshi daga ita har mijin bar yar iska karya yazo ya shimfida masu suka hau suna hauka. Daga ita har mama kallonsu nakeyi itace fa a matsayin ta hudu matansa ukku itace yanzu ta hudunshi sai taje ido ya raina fata irin gidan nan ne kuma family house zai kaita. Musu kai kaya ai suna can yaya Ai ta kirani dazun nan tana sheda min sunje sunga abu na daban ba abinda aka fada masu bane ko kayan basu shiga dakin da aka nuna masu ba a matsayin nata yanzu suna can dai ai na kirasho yace wai bai gama ginansa bane kiji makaryaci hakan ne daidai da ita yar iska dama sai mai karya irinsa zai iya kwasanta ai suje can su karata dashi tunda mutumiyar banzace ita. Wai yaya tana cewa ko za a kama mata haya ni zan kama masu haya ya zauna da matarshi ke nan duk shekara inbiya ko ? Shi habibin ashe makaryacine don haka take kiransa da habibi kowa dashi ya sanshi a fanninta. Ya amsa yace babba kuwa aini da ganinsa nasan mutumin banzane yanayinsa kadai ya nuna min hakan a kanshi makaryacine yace shine manager a bankin ashe karyane. Haka akace mana manager ne na bankin manoma ta kasa karya yakeyi ya fada yana mikewa yace tadaiyi auren shine burin mu a yanzu. Sai banji dadin hakan ba don za ayi a dawo ana da an sanine a karshe naja bakina nayi shiru ban sake uffan ba akan zancen shima kuma ya fada min ne don yasan ba za a taba jin zancen a bakina ba indai nice. Can gidan kuma ashe labari yazo masu daga yan jere irin abinda sukaje suka sama a gidan hakan yasa hankulansu ya tashi ita kuma wawiya bata yarda ba wai ai yace dama bai gama gina inda zasu zauna ba. Shiyasa yaso a daga auren amma su yaya Auwal sukaki yarda da hakan sukace ayi haka dai a wuce wajen. Karshe dai dole kowa yayi shiru amma mama hankalinta bai kwanta da irin yadda ina hafsatu ta labarta mata komai ba har matanshi da yaransa da suka gani. Hakan yasa ta kirashi take kara fada mata ina shiga dakin naji yana fadin to yanzu mama ko hakan gaskiyane yaya zamuyi tunda ita tace tana sonshi . Hakkuri za ayi da fatan zaman lafiya su sauran matan da suke zaune dashi ai basu mutu ba ka saurareni malam wanan zance abin a dubane tun yanzu. Mama ba rawan kanta ya kaita ba koma yaya abin yake ai dole dai hakkuri za ayi yanzu tunda ba za a fasa auren ba. Ya kashe waya don tunda na shigo na fahinci da ita yake waya na juya zan fice daga dakin yayi min hannu dana dakata kar in tafi na dawo na zauna don banda jimirin tsayi a lokacin. Mama ke nan ta fahinci inda saratu takai kanta hankalinta ya daga a yanzu shine suke ganin laifin mutane kan anki kara kudi ayi karya niko ko a jikina don ita ta kanta ta nace sai shi a barta taje ta gani ai yanzu. Nima wallahi na damu irin hakan babu dadi ai maka karya sai kaje ka samu ba haka abin yake ba kuma babu yadda zakayi an riga da anyi din. Sherintane yake shirin cita shiyasa ake son bawa da tsarkake zuciyarsa akan kowa nan tace dake ai tana yarinya karama ba kwadayin da zai jata ya kaita auren mai mata koda gudane ? To, gashi yanzu ita bako mai mata daya ta aura ba mai mata har ukku itace ta hudu kinga Allah ya ceceta da irin rayuwan abokan zamanki na kazanta kuma. Ai, Ba,a kula irinsu anty saratu yaya ni harga Allah ta ban tausayi wallahi don babu walwala ko jin dadi dai a gareta yanzu gidan yawa ai fitinane babba ya tunkaro ta. Aita iya makirci sai su saje dasu suyi tayi niko a jikina na jima da sallama lamarin yarinyar nan a rayuwana tun lokacin da tace da kudin gadon mu nake aure na sallama lamarinta. Haba dai kai babbane hakkuri za kayi bata da wani gatan daya wuce ku a yanzu ai ko yanzu kuma ta fahinci kai ba irin mutanen nan bane tunda kai mata komai a rayuwa. Ke kika fahinci hakan ita ai fushi takeyi dani daga ita har mama na kuma rantse a yanzu dai ban kara mata komai saita gane kurenta . Gara dai dakace sai gaba don duk yadda akayi saika saka hannu a wani abin shi dan uwa ai MURFIN JALLO NE don ko wakake a duniya wata rana sai dan uwa ya taimake ka. Rahama mu bar zancen nan idan munci gaba kina tuna min abubuwa akan yarinyar nan yarinyar data dafa min mugun ciwon da kowa yake gudu a duniya wani murfi take gareni a rayuwa ? Shiru nayi ban kara cewa komai ba washe gari tunda safe yasa kai ya fita gidan nasan hakan nada nasaban kiran da mama din take ta mashi tunda dare yaki daga wayan. Wani abu sai mahaifa don kuwa ko yaya ranka ya baci da hukuncinsu dole kai hakkuri idan kana neman rahaman ubangiji. Saratu dai tun bata yarda da zancen da ake fadi ba har ta soma yarda gashi washe gari daurin aure saida maza suka nuna ikonsu akan mama ta yarda ta amince aka daura aure a washegari. Duk cikin sarakan mama mu biyar ni kadaice na bada gudun mawa a harkan bukin aiko yaya barakha tana ta yabawa tana fadin kin gani ko ita da nasu baizo daya ba da saratun itace ma ta bada abin arziki. Aini tuni na gano yarinyar arzikine na daina biyewa zugin mutane akan zancen duniya ba dole ki daina ba tunda tana ma danki rikon munafunci a yanzu ? Komai zaki fada kan wanan yarinyar wajen malam da mukaje dazun cewa yayi hannu akasa aka dambala mijin don ba haka yayi niya ba da farko ? Haba mama don malam yace ansa hannu sai ace kuma Rahamace tasa mata hannu yanzu don Allah me ta tsare mata inma hannune ai saidai tayi wanda zata tafi ta zauna dakinta har abada. Don Allah mama a yanzu ya kamata ki rage irin wanan magana na malamai shekaru fa sunja mama ke in kin fada ai ba za aga laifinki ba ni wanan halin wallahi yana damuna sosai komai ace a je wajen malam ba a barwa Allah lamatin komai yanzu gidan nan. Can Saratu ta dauki mama sukaje wajen malaminsu da Nusaiba yace wai sai Nusaiba ta dawo abubuwa zasu kamkama ga zance kasan hadin bakine amma mama ta yarda da shirmensu. Salima ke fadin hakan aiko mama tayo cikinta da zagi na bacin rai tana batun tsine mata saida anty barakha ta kare tana fadin nikan mama zan kira Jafar yazo kan zancen tunda banga abin zagi ba a nan ? Ai gaskiya salima ta
Chapter 276 · 0% Book details