← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 130 OF 306

Sashe 130

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,

4️⃣8️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

Washegari shi ya shiga kitchen da safe ya hada muna breakfast ruwan zafin shayi sai dankali da kwai suyan damke don duk ya wargaje kwan a wajen juyi saidai yayi dadin ci gaskiya a baki.
Ina daki ya shigo ya sameni duk dana falka daga barcin safen dana dan samu amma na kasa dagawa daga kwancen ina kwance ina faman tunane ya shigo har dakin da abin kari.
Da sauri na tashi cikin mamaki ina gaidashi kin tashi ke nan ya fada yana aje kayan hannunsa din na amsa da eh yaya ina kwana lafiya ya fada yana zama yake fadin dama nayi zaton baki tashi ba ai ?
Yau muna da baki gidan nan duk da ba wajen mu sukazo ba zasu dauki kayane su tafi wanan kayan dake dakina kayan fadan kishiyace dana hadawa yan uwanki a a kai masu.
Saidai ita Asmau don haihuwan da zatayi nasa an hada mata har da kayan baby na kuma dan kara mata ya dara na Saiba din.
Kallonshi na danyi yace ehh ai kinga in Allah ya raba lafiya ba sai na koma sayan komai ba kuma shike nan na gama a yanzu.
Allah ya sauketa lafiya na fada ya amsa a cikin dadin rai da amin ai watan haihuwan nata ya kusa kamawa Allah yasa lokacin kun samu hutu sai kawai in daukeki mubar garin nan na dan wani lokaci.
Ita kuma dayan antyn fa yaya yace wai Saiba kike nufi idan na dauketa yanzu wazai kula da ita Asmau din, da hidima zaimata yawa ai ?
Maza ke nan na fada ni zainab makawa sai kiga namiji ya koma yaro karamin a gaban mace yana sakin magana kamar bashi ba.
Balle J da yanzu yana da madafa dan magana zai tunar dasu cewa sun nuna suna kyamarshi a baya don haka yanzu baida lokacin tsayawa dasu ai nasan dai abinda zai fada ke nan a karshen zancensa.
Tare muka karya dashi bayab mun gama nakwashe kayan zuwa kitchen na tsaya wankewa na gyara kitchen din dana fito nima wanka nashiga na zauna bayan na fito na shirya tsab a cikin wani atamfa dinkin zamani don dogon rigace amma tellan ya tsaya ya tsara dinkin kamar ba hannune ya dinkashi ba.
Dinkin akwai na ciki wanda zaki fara sakawa mai dan hannu saina sama mai adon da stely din dayasha duwatsu har kasa saiki rantse daga egypt aka shigo dashi haka.
Hullane mahadinsa don dan kwali bai haduwa da kaya haka sai gyalena ainihin da akai amfani dashi a matsayin gyalen yafawa da kayan .
A kyalen yadin kayan da akayi cin bakin gyalen dashi da duwatsu sai hakan yaba da mana,ana ga gayan sosai zai fito da duk macen data sa a jikinta abuja ke nan.
Sallaman su yaya Ai yasa na fito don sunki zama sunata gwara sallama shima lokacin yana ciki dakinsa kuma kofa a rufe.
Nice na fito ina amsa masu sallamansu suka juyo kofana muka fara gaisuwa nake ce dasu su zauna sai bayan sun zauna din na gurfana ina gaidasu da zuwa.
Masha Allah anty Rukkaiya ta fada tana bina da kallo tace a,a lalai ba laifi gaskiya Allah ya baku zaman lafiya amarya.
Na mike naje kitchen na dauko masu abinsha da snack gami da ruwa saida na ciko tire na kawo masu na aje na juya ina fadin barina sanar dashi isowan su na nufi hanyar dakinshi din duk suka bini da kallo anty Rukkaiya ke fadin.
Akace yayan fulanin ruggane gasu kamar ya Niger mana sun waye sosai ba zakice asalinsu rugga bane tun wanan madin har tafi ta wajen habu wayewa ai.
Itace daidai da matanshi ai don yaran basu da mutunci baka zuwa gidansu kasha ruwa balle abinci ni yaya Ai ko sun ban abincin su ai ban iya cima .
Yana zaune saman hasonsa ya dora kafa daya a sama dayan na kasa yana latsan laptop nayi sallama nashigo dakin.
Kai ya dago ya dan dubeni kamar zai maida hankali ga abinda yakeyi bayan ya amsa sallaman tasa sai kuma yayi saurin dagowa ya zuba min idonsa.
A dan maraice nake fadin su yayane sukazo suna falo zaune hannu ya miko min bakinsa na fadin har sun iso ashe ?
Na tako zuwa gareshi ina fadin yanzun suka shigo hannuna ya kama ya jawoni na fada jikinshi ya rugumini tsam yana fadin duk kayan da kika saka Rahama sai naga sunfi maki kyau ga wanda kika cire.
Wai meye sirin hakanne Rahama jin hannusa ya fara yawo a jikina yasa nace dashi cikin wani sallon fitar da magana su yaya fa suna falo suna jiranka kada suga an barsu su kaidai zaune.
Yaja numfashi yana dagani yace kece ai kika kashe min jiki yasa na kasa tashi na manta da zancen su .
Cikin kissa na dan kalleshi ina fadin ni kuma yaya yanzu dana shigo don Allah me nace dakai da zakace laifinane kuma ?
Au baki san abinda kikai min ba to ki duba nan da sauri na mike daga jikin nasa ina fadin nidai muje don Allah kada suga mun jima haka ?
Kamahin nan naki Rahama ba karamin illanta min zuciya yakeyi ba har na fara tunanen yadda zan koma maraya ranan da bani kusa dake wallahi.
Suma da kalan nasu a can da zaka shaka dama mata suna mukatara ai amma ba kalan mu daya ba a wajen abubuwa kowa da irin nasa fasahan ai.
Wai ashe kina magana haka dama ya fada yana gyara saita jikinsa daya mike tsaye ni dai nayi gaba ina dariya ya biyoni da yaya Rukkaiya data dauki cup tana shan lemo muka fara arba tayi saurin ajewa yake fadi daga bayana ashe kun iso yaya.
Mun iso Jafaru kasan halin yaya Ai ai da nabita nata aitin bakwai muna gidan nan ita bataki hakan ba a wajenta yayi dariya yana zama yace.
Haka ake son mutum ai da cika alkawari jin suna gaisawa yasa na koma dakin nasa ana basu waje bandakin na gyaro kafin na fara gyaran gadon dakin nasa lokacin ya shigo dakin .
Baki dai gajiya da aiki ke nafi son ki huta yadda nima zanbi jikin ki in huta da dare in sauke gajiyana yadda nake so amma sai ki wuni a tsaye kina aiki waike mai wayau don mutum ya tausaya maki ko ?
Dariya ya ban sosai saidai ba halin hakan shi yana mamakin sakewana nima haka mamakinsa nake ji yadda yake abinsa da iyalinsa cikin sakewa haka ?
Dama haka yake amma matansa suke kullum cikin fada ko dashi ko kuma a tsakaninsu kullum ba zaman lafiya a part dinsu can gida.
Ganin ya gara akwatunan biyu yasa na garo masa sauran muka fito dasu falo zuwa gaban su yaya din ina ajewa na juya na bar wajen naje na karasa aikin da nakeyi na gyaran dakin.
Shine ya shigo yake fadin su yaya suna tambayan ki don ba lalai bane su dawo ta nan din kije kuyi sallama dasu na fita na barshi a dakin.
Kudi ya dauka ya fito ya samemu yana fadin suje ko suka fice tare dasu bayan ya gama kwashe akwatinan zuwa motanshi.
Nan kofan gidan na dan rakasu suka shiga mota suka tafi ajiyan zuciya na sauke bayan tafiyansu din Allah yaso na hada masu leda su rike don basuci wani abin kirki ba ga abinda na aje masu a falon na motsa baki.
Na tattara kayan na koma daki na kwanta tunda yace min sai yamma zai dawo gida don haka ba sai nayi abinci ba ke nan.
Akwatuna shiddane suka fita dasu zuwa can gidan sai wasu jakkuna ban kuma tambaya ba tunda ya fada min kanun zancen cewa zasuje dasu yaya can gidan kai masu kayansu na tausan gaba irin da wasu mazan arewa keyi idan sun karawa matansu abokan zama.
Chapter 130 · 0% Book details