← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 139 OF 306

Sashe 139

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

musha ruwa. Kashedi nazo maki akan mijina Ramaah ina jin hakan nace to nakai zaune gefen hannun kujeran da anty Nafisa take zaune sama. Sai naji anty Nafisa tana fadin haba dai anty Saiba hakan aiba girman ki bane yaya zaki mata gida kice haka kuma ? Ke Nafisa dakata ban ambaci sunan ki ba dana shigo don haka ki kyaleni inyi da ita, ita da yanzu take ganin takai tunda tasan yadda suka shiga suka fita suka iya asirce shi har ya aureta ? Tunda sun saba da bakar bidan asiri suna mallake mutane har ita ta isa tasa J ya juya muna baya ya daina shiga duk wani harkan mu wallahi bata isa ba ? Daga ita har Maria din da kike takama ta samu habu ta mayar dashi saniyan tatsanku da kowa naku saidai ku tsaya ga habu shida kuka sama amma baku kai can ba wallahi. Ashe nakai har na usa kuma ke nan tunda har na iya mashi asiri daya kamashi don da bakiga hakan ba da baki tako har nan zuwa min kashedin ba ? Daga daga inda nake zaune nake fadan hakan tare da jin duk wani tsoronta da shakkunta ya fita a raina lokaci guda. Wallahi ke Ramaah karamar yar iskace baki isa ba wallahi ina ganin hakan na mike tsaye na sake fadin ai isan ya kawo haka tunda gashi har kin tako zuwa gidana ko kunyan hakan bakiji ba ko kin gani gidan ku ? Ta kwashe da wani irin dariya tana fadin wai gidanki kuji min yarinyar nan fa kije gidan mana idan kin isa mara kunya kike da gaske kije gidan ? Gida kan ko yau nake son zuwa zanje don baki da wuta baki da aljanna akaina Nusaiba kuma gida ba naki bane don haka baki isa ki hani shiga ba. Bansan ya akayi Salima ta kira mama ba na daiga tana fadin wallahi mama muna zaune suka shigo ita dasu anty ikilimanta. Niko ina fadin ai bansan kin dau abinda zafi haka ba dana rigaki yi maki takaka a gidan inga abinda zaki min din ? Haka kikace zan dawo ko don ki wallahi nace ki dai dawo don mijinki daya ajeki amma ba dai niba basan da tsiya kikazo ba dana tareki dashi tun farko ? Yanzu da kika sani ai sai kiyi wace zakiyi din tunda kin sani ke dai da tsiyan ta kawoki ai ina sauraren ki ? Anty salima na fadin wai ba zaku daina ba don Allah ke saiba duk inda akaje baki da gaskiya tunda ke kikazo har gidanta . Kaji wata munafuka na amsa da fadin munafuka tafiki Nusaiba ? Saida ta kalloni cikin mamakin jin abinda na fada nace keda kika yi munafuncin daya ciki kika fada ciki inkina ganin kin iya sheri an fi wallahi. Koda yake ba abin mamaki bane ai tunda dama kowa ta dalilin sheri da munafunci ya sanki a gidan. Don kawarki kikaiwa kwancen miji gashi har kina nuna kinfi son mijin fiye da ita a yanzu kin dauka zakiyi min sherine yaje a banza ko gobe kika kara min sheri zakiga fiyema da hakan wallahi. Sam ban yarda na raga mata ba kamar yadda anty Salma ta fada min inyi a duk wace tayi min takaka a cikinsu in debe tsoro da kunya inyiwa maishi tas don gobe karta dawo min gida . Hakan ko nayi mata don na debe tsorona a lokacin na shafawa idona tako na mayar mata da martani don a debe tsoron juna a tsakanin mu dama ina kule da ita a raina har lokacin. Jin wayan da Salima keyi da yaya Habu yasa suka bar gidan ajata ajani tana fadin bata zuwa ko ina sai taga karyan rashin kunyata gidan . Don naga na samu waje zan kawo mata iskanci zata gwada min ko ita waye ranan don sai ta murjeni kamar filawa nace mudai murji juna dake Nusaiba bari ganin kinzo da wa yan nan wallahi, in kuma kina iyawa ki gwada. Sai kuma ta juya kan Salima da Nafisa tana fadin ku kuma haka zasu kare a gurin bin kanwar baya bayanku don kwadayi da wullakanci . Su rasa wace zasu bi har gidanta saini suje suyi aure yafi masu zama gindin yarinya karama suna zugani ina daukan ni wata tsiyace ? Fadan ya koma namu duka kowa ya fadawa dan uwa maganan dake bakinsa data sani batai hakan ba da har gobe tana da matsayi a wajena na wace ta girmeni kuma take gaba dani a gidan aure. Saidai kash zuciya yakaita da girmanta ya fadi wajen kowa a wanan lokacin don ita kanta bata taba zaton zan iya bude baki inyi mata haka ba. Koda yaya Habu ya iso sun tafi ko yace zai dauki mataki kan hakan agabanmu yakewa maigadi warning da kada ya kara bari wanan matan su shigo gidan nan. Anyi haka da kamar sati zancen ya lafane don har kaduna mama taje da kanta suka dawo da ita bayan an tsawata har lokacin kuma shi bai dawo ba kasan saidai da alaman yaji duk abinda ya faru don daya kira yake tambayana cewa bata sake zuwa ba ko ? Na amsa da bata zo ba don yakan kira a sati saudaya ko sau biyu a cikin sati yaji lafiyan mu a dan gaigaisa da jama,a kuma. Hafsatu dake tankade a kofan kitchen taga mijinta ya fito da shirinsa ta bishi da idanu don yanzu gaskiya karara ya canza mata fuska gashi alkawuran da yayi na gyaran dakin yaransu bai cika ba. Wayanshi dayayi kara a cikin aljihu ya tsaya dauka daga kofan dakin nasa ta gane dawa yake wayan don jin sunan mama dubu daya ambata sun dan jima suna magana kafin taji ya soma fadin. Amma ita salima me zatayi da kudi har haka kudin nan fa gaba daya na dauka nasaka a wanan sana,an takin don yanzu kinsan shike shiga da sauri da daminan nan . Kallonsa da sauri Hafsatu matarshi tayi ganin hakan yasa ya karasa saka takalman shi dake kofan daki ya fita ta bishi da kallon tsarguwa. Wani kudi yake zancen yakai sayen taki dashi dazaice hakan amma ai gamu gani badai a kan kudin nan ya matse mata ido da wani hurda ya rikesu gaba daya ya sauya mata. Dakin dake kusa da hanyar bandakinsune wanda iya take rayuwa da a cikinsa kafin a sai wancan gidan da suke zaune a cikinsa yanzu. Shi taga ya gyare fes tayi magana yace bataga ginan ya rankwafo bane kada ya fadi saita yarda da hakan daya fada lokacin. Sunyi hakan da yamma yana cin abinci yake fadin ina ganin fa zamu karu a gidan nan hafsatu amma saidai yadda hali yayi tukun don bamu gama shiryawa ba tukum da bazawar tawa har yanzu. Aiko hafsatun tayi cikin shi da masifa ta inda take shiga banab take fita ashe duk lokacin ankai sati biyu da daura aurensa bata sani ba sai lokacin ya gwada fada mata aiko baisha da dadi ba a ranan wajenta
Chapter 139 · 0% Book details